Wednesday 3 July 2013

Bayanin Wasan Kwaikwayon Hausa A Takaice

BAYANIN WASAN KWAIKWAYO A HAUSA A TAKAICE MA'ANAR WASAN KWAIKWAYO A HAUSA Ba da an tsawaita bincike ba ana jin cewa ma’anar wasan kwaikwayo a Hausa a bayyane take daga lura da kalmomin da suka gina shi, wato abu ne mai alamun wasa da kuma kwaikwayo. Shi dai wasa na nufin duk abin da ba gaskiya ba, yana kuma dauke da raha da ban dariya da nishadi, akwai kuma kwaikwayo, wanda ke nuni da aikata wanin abu don kwatanta yadda yake, ko yadda ake yin sa, ko don a kyansa ko kuma muninsa. Abin la'akari a nan shi ne, za a ga cewa wasan kwaikwayo a Hausa ba kamar su daya da drama, a Ingilishi ba, domin su Turawa sun dauki drama ko wasan kwaikwayo a matsayin wata basira da za a shirya a rubuce ta fuskar zube ko waka, mai nuni da yadda rayuwa take gudana ko halayen wadansu, ta hanyar fadi-in-fada da alamtarwa, an kuma fi gudanar da shi a dandali. Duk da cewa akwai ‘yar tazara tsakanin wasan kwaikwayon Hausa da yadda yake a cikin Ingilishi, za a fahimci cewa abubuwan nan da Hausawa suka fi mayar da hankali a kai wajen gane wannan abu, suna nan rakube a cikin dukkan wani wasa mai kama da haka a kowane harshe ko al'ada ta duniya. Yaya wasa yake a cikin wasan kwaikwayo, shi kuma kwaikwayo yaya ya kasance? Duk irin wasan kwaikwayo na gargajiya da ka yi nazarin kayan cikinsa za ka ga alamun nan biyu na wasa da kwaikwayo a cikinsa. Misali: Wasan langa Wasan ‘yar tsana Wasan kalankuwa Ko Wasan Marafa (a rubuce) Dangane da haka duk wani tsarin wasa da aka sa gaba idan bai da wadannan siffofi to ba wasan kwaikwayo ba ne. Haka kuma dole ya kasance da wadannan kamannu. 1) Sake kama ko canza tufafi ko murya. 2) A sami wani wuri na musamman (wato dandali ko dandamali) 3) Ya kasance yana dauke da wani sako 4) Dole a sami tanka-in-tanka BAMBANCIN WASA DA WASAN KWAIKWAYO Wasan Kwaikwayo Wasa Koya darussa Nishadi da jin dadi Akwai kwaikwayo Ba kwaikwayo Canza kamanni Ba canzawa A dandali don a gani Ba dole don a gani ba Ba daukar lokaci mai tsawo Ana daukar lokaci mai tsawo Akwai lokutan gabatar da shi Ba wani lokaci tsayayye Wannan ya nuna cewa, ta hanyar kwaikwayo ne dan Adam yake koyon magana da kuma dabarun sarrafa harshe, hakan kuma ta kwaikwayo ne yake koyon yadda ake sarrafa abubuwan da ke kusa da shi, ta hanyar samar da muhalli, tufafi, makamai da sauran su. Kuma ta kwaikwayo ne dan Adam yake koyon sana’a kamar noma, farauta, kira da sauran su. Ke nan wasan kwaikwayo dadaddiyar al’ada ce a cikin rayuwar Hausawa, saboda haka ana kallon sa ta hanyoyi da dama. A ra’ayin wani masani Ibrahim Yaro Yahaya, ya ce “a al’adance ko a gargajiyance wasan kwaikwayo na nufin dukkan abubuwan nishadi da ban dariya, da tsokana da annashuwa, da kuma motsa jiki, da akan yi a wurare daban-daban, musamman a wuraren bukukuwa, da bakin kasuwa, domin a nishadantar ko kuma a fadakar da al’umma”. Haka kuma a wani hadin gwiwa a tsakanin masana biyu, a nasu ra’ayi, watau Abdulkadir Dangambo da Ibrahim Yaro Yahaya sun ce “wasan kwaikwayo wasa ne inda akan aiwatar da wata matsala ta rayuwa cikin siffar yakini ko kuma a rubuta shi”. Haka Abdulkadir Dangambo ya ce “wasan kwaikwayo kamar yadda sunansa ya nuna, wasan ne da ake gina kan kwaikwayon wani labari ko wata matsala ta rayuwa da ake son nuna wa ga jama’a”. Shi kuwa Tanimu ‘Yar ‘aduwa ya bayar da ma’anar wasan kwaikwayo kamar haka, “wasan kwaikwayo kamance ne na wasu halaye ko yanayin rayuwa, wadda masu hikima sukan shirya su gabatar da shi ta hanyar annushuwa da raha da nishadi don cimma wata manufa”. A wani aiki da su Sadiya Omar Bello suka yi wa edita, sun ce “wasan kwaikwayo wani tsararren abu ne wanda ake kwatanta wata rayuwa ta wani yanayi don bayyana wa mutane ta hanyar wasa”. Har wa yau Atiku Dunfawa ya ce “wasan kwaikwayo shi ne duk abin da aka tsara kwaikwayonsa don nuna cewa jama’a su gani, kuma shi wannan abin da za a nuna yana iya kasancewa ya taba faruwa, yana kuma kasancewa bai taba faruwa ba, sai dai an zauna ne an kago shi da kwakwalwa don nuna wa jama’a”. Bugu da kari, za mu iya fahimtar cewa wasan kwaikwayo ba abu ne na gaskiya ba, kirkirarsa ake yi, don haka idan muka dauki wadannan kalmomi guda biyu, wasa da kuma kalmar kwaikwayo za su tabbatar mana da cewa, wasa dai wani abu ne da Hausawa ke nufin duk wani abu da aka gabatar wanda ba gaskiya ba ne, sannan kuma kowa ya amince ana yin sa ne domin samar da raha, da ban dariya, ba don cin mutunci ko cin zarafin wani ko wata kungiya ba. Shi kuma kwaikwayo na nufin aikata wani abu ta hanyar canza kama, ko murya, ko jiki, ko siffa, ko muhallin yin aikin, da nufin nuna kwaikwayo ko nunin abin da ake so juya. A bisa wadannan bayanai za mu iya fahimtar wasan kwaikwayo yana da siffofi biyu a al’adar al’ummar Hausawa. Da farko dai akwai wasu al’adu masu tsari irin na wasan kwaikwayo. Na biyu kuma, akwai wasan kwaikwayo irin wanda muka sani ana shiryawa, ana gudanarwa a dandamali, ko a gidan rediyo da talbijin. TAKAITACCEN TARIHIN WASAN KWAIKWAYO A HAUSA Shi dai wasa irin na nishadi ko na kwaikwayo ko kuma na motsa jiki dadaddiyar al'ada ce a kasar Hausa kamar yadda muka yi bayani a baya, musamman ganin cewa ya girmi rubutacce,. Ke nan dole ne a amince cewa tun fil azal akwai wasan kwaikwayo a rayuwar kowace al'umma kafin zuwan rubutu. Saboda haka idan aka koma kan batun tarihin wasan kwaikwayo a kowace al'umma ya dace ne a koma ga al'adu da adabin gargajiya domin ganin ko akwai masu kamannu da irin wannan abu, a nan abin da ke da muhimmanci ba yanayin da ake sami abin ba, wato a rubuce ko a ka, irin amfanin wannan abu a tsakanin jama'a. Haka kuma ba maganar rana ko wata ake yi ba, a’a, lokacin da ake jin cewa ya samu ginuwa a tsakanin al’ummar. Saboda haka a takaicce za mu iya cewa wasan kwaikwayo ya samo asali ne tun farkon ginuwar al'ummar Hausawa. Ita wannan al’umma tana tafiya ne da al’adunta na gargajiya da suka hada da wasannin gargajiya da sauran wasanni. Saboda haka za mu iya karkasa wasannin zuwa gida-gida kamar haka: • Wasannin gargajiya na wasa kurum: Wasan kura ko na maciji ko na kunama. • Wasannin sana'a da suka hada da wasan gardawa (hawan kaho) da na ‘yan tauri (wasan tauri) da na ‘yan kama da na ‘yan dabo. • Wasannin dandali ko wasannin yara da suka hada da A sha ruwan tsuntsaye da Dan akuyana da na ‘Yar tsana. • Wasannin bukukuwan al'ada da suka kunshi wasan Giwa sha laka da Bikin budin daji da na Kallankuwa da wasan bori. Sai dai kafin mu shiga cikin takaitaccen bayani kan tarihin wasan kwaikwayon Hausa bari mu dubi asalinsa da alakarsa da sauran na sassan duniya. Kusan duk an yarda cewa wasan kwaikwayo shi ne ginshikin hanyoyin da dan Adam ke bi yana koyon yadda zai rayu. Watakila, ke nan za a iya danganta asalin wasan kwaikwayo da farkon bayyanar dan Adam a doron kasa. Akwai ra’ayoyi da dama game da asalin samuwar wasan kwaikwayo, akwai masu ra’ayin addini shi ne asalin wasan kwaikwayo. Masu wannan ra’ayi suna ganin cewa wasan kwaikwayo ya samo asali ne ta hanyar bautar gumaka da kabilun Girkawa ke yi a wani biki wanda ya dimanci addininsu. Suna gudanar da wannan bauta a wani kayyadajjen lokaci na shekara. Kuma wannan biki a gaban ‘yan kallo ake gudanar da shi. Haka kuma akwai wani ra’ayi mai nuna cewa a Gabas ta tsakiya da kuma kasar Indiya har ma da wasu sassa na Afirka mutanen sukan yi wani abu mai kama da wasan kwaikwayo musamman a lokacin da suke yin ta’azziyar bikin mutuwar muhimmin mutum don nuna girmamawa a gare shi. Saboda haka wasan kwaikwayo na nishadi, ko wanda ake yi don motsa jiki, ko na addini abu ne wanda ya samo asali da dadewa a kasar Hausa. Wasan kwaikwayo ya samu ne tun wanzuwar al’ummar Hausawa. Kuma muna hangen cewa abubuwan gargajiya sun girmi na zamani ko wadanda ake rubutawa. Abin nufi a nan shi ne wasan kwaikwayo ya samu ne ga al’ummar Hausawa tun kafin wanzuwar ilmin zamani na karatu da rubutu. Da dadewa akwai wasu al’adu da yara ko samari suke gabatarwa ta hanyar kwaikwayo a tsakaninsu, shekaru aru-aru kafin al’ummar Hausawa su fara hulda da cudanya da wasu al’umman da ba su ba, wato na ketare. Daga cikin irin wadannan al’adu na Hausawa akwai: wasan langa; a cikin wannan wasa yara za su kwaikwayi yadda ake yaki. A nan yara za su kasu gida biyu ne wannan langon da wannan, kuma kowane gida yana kokarin ture langon dan uwansa ko abokin wasansa. Kuma su wadannan gidaje biyu suna daukar kansu a matsayin abokan gaba na garuruwa guda biyu. Sannan kowane gari yana karkashin sarkinsa. Da ganin wasan kansa yaran na kwaikwayon dabi’ar yaki ne a cikin wasa. Bayan wannan akwai bikin ‘yartsana: galibi yara ‘yan mata su ne suke yin wannan wasan. Wasa ne wanda idan yarinya ta mallaki ‘yartsana, sai ta rinka yi mata raino irin na gaske, ta rika kwaikwayon ciyar da ita, tana yi mata wanka, idan ta girma ta yi mata kunshi, ta yi mata ado na tufafi da sauransu har ta kai fagen yi mata aure da sauran hidimomi. A irin wannan wasa ‘yanmata na kokarin su kwaikwayi yadda ake renon mutum tun yana karami har ya girma, har a yi masa aure a cikin wasa. Babu ko tantama tunda aka sami wasa da kuma kwaikwayo, to ya zamo wasan kwaikwayo ke nan. Bayan wannan hasali ma manya da kansu baya ga irin wadannan wasannin gargajiya na yara, akwai wadansu al’adu da sukan yi masu siffar wasan kwaikwayo. A cikin irin wadannan al’adu, akwai: Bori: wannan wata al’ada ce a kasar Hausa wadda Hausawa kan yi don neman kubuta daga wata cuta da ta kama mutum tana wahalar da shi. Idan ana neman waraka daga wannan cuta mai rikitarwa, to wani lokaci a ce sai an yi wa mutum mai irin wannan cuta girka kafin ya sami waraka. To sai ‘yan bori su taru ana yi musu kida da goge, ko garaya, ko molo, ko duma, ko dundufa. Su ko sai su hau bori suna tuma suna faduwa. Ta wannan haujin sukan kwaikwayi iskokin da ke tare da su ta hanyar jirkita magana da siffofinsu. Haka kuma akwai wasan kallankuwa: Kallankuwa wani wasa ne da samari da ‘yanmata kan shirya suna kwaikwayon aikin mulki da gudanar da shari’a a karkara da kuma yanayin zamantakewa a cikin kaka. Akan gabatar da irin wannan wasan a gaban manyan gari da sauran mutanen gari a matsayin masu kallo. Kuma akan tanadi wuri na musamman don gudanar da wannan wasa, kuma a cikin wannan wasa akan kwaikwayi wasu halayya da dabi’un mutane. Kuma masana na hangen cewa tun a wajen sana’ar Bahaushe ta farko, watau farauta akwai birbishin wasan kwaikwayo a ciki. Wannan yana da alaka da irin abubuwan da suke faruwa can daji idan an je wurin farauta. Domin wani lokaci akan sami ‘yan farauta da irin su Bikin budin daji ko Shan kabewa da sauran su. Kamar yadda tarihi ke maimaita kansa, wasan kwaikwayo ya samu ginuwa a tsakanin al’ummar Hausawa tun azal. Wannan shi ne ya sa aka rarraba shi zuwa gida uku kamar haka: Na daya akwai wasannin gargajiya na Hausa. Na biyu wasannin dandali watau wanda samari maza da ‘yan mata ke yi. Na uku, wannan ya kunshi bukukuwa . ZUWAN LARABAWA DA MATSAYIN WASAN KWAIKWAYON HAUSA Larabawa dai sun shigo kasar Hausa ta hanyoyi mabambanta, da farko dai a lokacin shigo da addinin Musulunci wanda aka ce ya samu karbuwa tun nwajajen karni na 8 zuwa na 9, daga baya kuma ta hannun masu cinikin bayi da saye da sayarwa addinin Musulunci ya zaunu sosai a kasar Hausa. Daga tsakanin karni na 13 zuwa na 15 kuwa addinin Musulunci ya warwatsu zuwa garuruwa da kauyukan kasar Hausa, ta yadda kusan kowane sashe na kasar Hausa ana gudanar da addinin Musulunci. Wannan ya sanya ilmin addinin Musulunci da makarantun allo suka wanzu a kusan ko’ina a fadin kasar Hausa. Wannan ne ya sa al’ummar yankin suka nakalci harshen Larabci ta yadda har suka iya rubutu da shi, suka samar da hanyar rubutu ta ajami. Saboda haka har zuwa lokacin da aka jaddada addinin Musulunci a kasar Hausa a karni na 19, za a ga cewa yawancin Hausawa sun iya karatu da rubutu cikin Larabci da ajami ta yadda aka samar da rubutaccen adabin Hausawa ta wadannan hanyoyin rubutu. Yawancin ayyukan adabin da aka samar sun fi a fagen waka da kuma zube. Ke nan wannan ya nuna mana cewa ba a samar da wasan kwaikwayon Hausa a rubuce a cikin Larabi ko kuma ajami ba. Kila tambayar da wani ka iya yi ita ce me ya sa wasan kwaikwayo a rubuce a zamanin zuwan Larabawa ko cikin rubutun ajami bai samu tagomashi ba? a) Ajami ya zo ne da addini, addini ba wasa ne ba, sai aka dinga wa'azi da amfani da waka, b) Su kan su Larabawa wasan kwaikwayo bai je gare su ba sai a karni na 18, wanda a lokacin addinin Musulunci da Larabci da ajami sun dade da ginuwa a kasar Hausa. c) Addinin musulunci ya hana al'adu na wasannin banza da labaru na karya da wake-wake na hululu. d) Lokutan koyar da karatu a makarantun allo ba a da wani wuri na koyar da wasan ko yin wasan. Bayan zuwan ajami da Larabawa suka kawo, sai zuwan masu jihadi, su ma ba su bada karfi wajen rubuta wasan kwaikwayo ba. Saboda suna ganin rubutun ajami, rubutun addinin Musulunci ne, babu wasa a cikinsa. Amma an sami wani mawallafi a dab da zuwan Turawa kasar Hausa a 1902, mai suna malam Muhammadu Ajingi, wanda ya yi rubutu a kan tafiye-tafiyensa a tsakanin kasar Hausa da kuma Afirka ta Arewa kasashen Larabawa, wanda suka kama da wasan kwaikwayo a rubuce, kamar yadda U.B Ahmed ya bayyana ya samar da wasannin Turbar Turabulus da Turbar Kudus da ‘Yan matan Gaya . ZUWAN TURAWA DA SAMUWAR WASAN KWAIKWAYON HAUSA Ko da da turawa suka zo sun yi kokari ne su mayar da wasannin gargajiya da na kwaikwayo su kasance na zamani wato a rubuce. Wannan ne ya sanya wasan kwaikwayo zamani ya kasu kashi biyu. Akwai rubutaccen wasan kwaikwayo na zamani. wanda aka rubuta kurum ba a dab'a ba da wanda aka rubuta aka buga ko aka yi wa dab'i. Kamar yadda muka yi bayani a can baya kafin zuwan Turawa dukkan wasan Hausa na gargajiya ne ba a kuma rubuta su ba ko da ajami, Da yake a can Turai al'adar rubutu ta dade, sun koyi dabbakar da ita a rayuwarsu ba abin mamaki ba ne da suke mamaye kasar Hausa suka assasa wannan al'ada, sai dai ba kai tsaye ne aka samar da rubutaccen wasan kwaikwayon Hausa irin na Turawa ba. A lokacin da Turawa suka kafa hukumar fassara a 1929 aikin wannan hukuma ya hada da samar da littattafai don karantawa, bisa wannan tsari ne shugaban hukumar Dr. R. M. East da malam Abubakar Imam da masinjar hukumar malam Basankare suka tsara wasan kwaikwayo na farko da Hausa a shekarar 1936, wanda suka sa wa suna Six Hausa Plays (Wasannin Hausa guda shida). Daga cikin dalilan da ya sa aka soma wannan al'ada bai wuce neman nuna wa jama'a yadda ake tsara wasannin kwaikwayo a rubuce ba, musamman ta hanyar canza tatsuniyoyi da tarihi da tarihihin kasar Hausa zuwa wasannin kwaikwayo. Ganin wannan littafi ya amsu, yara kuma suna karantawa ga kuma lokutta da aka ajiye a azuzuwa domin yin wasannin da kuma shirya wasannin kwaikwayo, sai wannan al'ada ta shige rayuwar jama'a, daga wannan lokaci yara da malammai suka shiga rubuta da aiwatar wasannin kwaikwayo a makarantu da lokutan karatu da bukukuwa Daga cikin daliban farko da suka rubuta wasannin kwaikwayo aka gabatar sun hada da irin su malam Aminu Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule, Alhaji Abubakar Dogondaji da Alhaji Abubakar Tunau Mafara, Wasu kamar na malam Aminu Kano Kai Wanene a Kasuwar Kano? Da Gudumar dukan en-en Kano, ba buga su ba, sai littafin Alhaji Abubakar Tunau Mafara, Wasan Mafara (1949) da na Alhaji Abubakar Dogon Daji, malam Inkuntum, (1953), wadanda aka buga daga baya. Daga wannan lokacin aka shiga cin kasuwar rubutun wasan kwaikwayo, aka kuma ci gaba da samar da su daga madaba'u daban-daban har zuwa yau da ake da wasannin kwaikwayon Hausa a rubuce masu tarin yawa: Marubuci Littafi Shekara Madaba’a 1. R.M. East Six Hausa Plays 1936 Lagos 2. A.A. Tunau Wasan marafa 1949 Gaskiya, Zaria 3. A.A. Dogondaji Malam Inkuntum 1954 Norla, Zaria 4. A.S. Makarfi Zamanin Nan Namu 1959 Gaskiya, Zaria 5. A.S. Makarfi Jatau Na Kyallu 1964 Gaskiya, Zaria 6. A. Muhd Sada Uwar Gulma 1971 NNPC, Zaria 7. A. Dangoggo da Dauda Kano Tabarma Kunya 1971 NNPC, Zaria 8. Umar Dembo Wasannin Yara 1971 NNPC, Zaria 9. I.Y. Yahaya Daren sha Biyu (Fassara) 1971 NNPC, Zaria 10. Umaru B. Ahmed Bora da Mowa 1972 NNPC, Zaria 11. Bello Muh’d Malam Muhamman 1974 NNPC, Zaria 12. Bashari F. Roukbah Matar Mutum Kabarinsa 1974 NNPC, Zaria 13. Umaru Ladan da Dexter Lyndersy Shaihu Umar(Daga Kagaggen Labari) 1975 NNPC, Zaria 14. Ahmed Sabir Mutanen Kogo (Fassara) 1976 NNPC, Zaria 15. Hasan U Kome Nisan Jifa 1978 NNPC 16. Katsina U. D Kulba Na barna 1979 NNPC 17. Ladan U Zaman Duniya Iyawa Ne 1980 NNPC 18. Idris D Matsolon Attajiri (Fassara) 1981 NNPC 19. Alkanci H Soyayya Ta Fi Kudi 1982 NNPC 20. Ahmed U.B Amina Sarauniyar Zazzau 1984 NNPC 21. Katsina U.D Ai Ga Irin ta Nan 1986 NNPC 22. Yaro A.K Bar Ni da Mugu 1986 NNPC 23. Maigari G. I Mugunta Guzurin Wuya 1986 NNPC 24. Sorondinki A. Gani Ga wane 1990 NNPC 25. Mahmoud Barau Bambale Kukan Kurciya... 1994 NNPC Baya ga wadannan kuma an samar da kungiyoyin wasan kwaikwayo masu yawa a makarantu da hukumomin al'adu na gwamnati da kungiyoyin taimakon kai, ta haka ake ci gaba da raya da gudanar da wasannin kwaikwayo a rubuce da kuma a aikace ire-iren wadannan kungiyoyi suna da tsari irin na shugabanci, sun kuma rubuta wasanni suna aiwatarwa daga lokaci zuwa lokaci, wasu da taimakon hukumomin al’adu na jiha da na tarayya, wasu don kashin kan su. Ire-Iren Wasan Kwaikwayon Hausa Game da irin fadin da ma’anar wasan kwaikwayo ke da shi, za mu iya cewa akwai al’adu da dama wadanda ke da dangantaka da wasan kwaikwayo tun kafin a fara rubuta littattafan wasan kwaikwayo cikin Hausa. Wadannan al’adu akwai wadanda yara samari ko ‘yanmata ke kwaikwayo a tsakanin su. Wasan Yara Maza da Mata Langa: A irin wannan wasan yara maza su ke kasuwa gida biyu, kuma kowane gida yana kokarin ture lagon dan uwansa. Watau a nan yara sukan kwaikwayi yadda ake yaki ne. Don haka wadannan kungiyoyi guda biyu suna daukar kansu garuruwa ne masu gaba da juna suka zo filin daga na yaki. Kuma kowane gari yana karkashin sarkinsa mai suna ruwa da kuma barden yakin sarki wanda ake kira ko aka lakabawa suna dokin ruwa. Kuma duk kungiyar da ta bari aka ture lagonsu to an fi su karfi kuma an cinye su da yaki ke nan. Dan akuyana: A irin wannan wasa yara maza kan yi da’ira ne rirrike da hannun junansu, ma’ana suna zagaye fili ke nan. A cikin da’irar za a sami yaro daya wanda aka ritsa da shi a ciki. Wannan wasan yana siffanta da’irar da rumbun hatsi ne, shi kuma yaron da aka ritsa da shi ciki dan akuya ne wanda ya riga ya yi barnar hatsi. Kuma wannan yaro da aka rutsa yana son ya fita kuma ga shi ko’ina an gewaye shi, don gewayen matsayin rumbu shi ke, don haka idan yana son fita sai ya yi wani babban yunkuri ko kuwa ya sha duka. Wasan ‘Yar Tsana: Yara ‘yanmata zalla su ne suke yin wannan wasan. Yarinya takan mallaki ‘yartsana sai ta rinka yi mata reno irin yarinya ta gaske, ta rika yi mata wanka da kwaikwayon ciyar da ita. Har yarinya ta girma. Idan ta girma ta yi ma ta kunshi da ado da tufafi wanda teloli suka dinka da kyallaye. Daga haka har yarinya ta kai fagen aure, sai ta raba goro ga kawayenta, ta gaya musu ranar biki. Sai ta tanadi kananan kwanuka da tasoshi, har ma da gado, da matasan kai. Su kuwa kawayenta su zo ranar kamu, su siffanta duk abubuwan da manya suke yi na bukukuwan aure tun daga ranar kamu har ya zuwa kunshi da kuma tarewa zuwa gidan miji. Kawaye kan kawo nasu tallafi ko gudummuwa ga uwar diya. Hasali ma sukan bi duk wani tsarin bikin aure su siffanta shi a cikin bikin auren ‘yartsana. Wasannin Tashe Wadannan wasanni yara suke shirya su dai-dai a cikin watan azumi bayan shan ruwa da daddare su rinka bi gida-gida suna wasa manya na kallo suna nishadi da raha. Misalin irin wadannan wasanni su ne masu siffanta irin wadansu halaye na tausayi, kamar su: Tsoho da gemu: Kungiyar masu tashe sai su yi wa waninsu ado irin na tsofaffi a cikin tsohuwar riga, rawani, gemun kada, sanda da carbi. Su bi shi suna cewa wannan tsoho ga shi nan da gemunsa, ba shi da karfin ciyar da kansa, saboda sai an tallafe shi da abin da zai ci. Shi kuwa ya dinga wani yakunewa yana ‘yan tari da mamular baki kamar na marar hakora, yana yi yana jan carbi, masu kallo suna dariya. Jatau Mai Magani: A nan yara masu tashe suna siffanta ko nunin yadda boka yakan lakanci magunguna. Bokan shi ne ake kira Jatau. Yara samari kamar hudu ko fiye da hakan suke raka dan uwansu zuwa gida-gida yana nuna tsirrai, saiwowi da kunshe-kunshen magani, da layu da guntayen fatu da kasusuwa. Yana nuna wa mutane wadannan daya bayan daya yana kuma fadin sunayen su da irin maganin da suke yi. Mairama da Daudu: ‘Yan mata suke da wannan wasa. Yara ‘yan mata kamar shida ko fiye, suna biye da yarinyar da suka yi wa lullubi (amarya, Mairama) da kuma wadda suka sanyawa kayan maza (ango, Daudu) suna bin su da kayan daki kamar su kwanuka da tabarmi da kujeru. Su kuma ‘yanmatan duk sun ci ado irin na ‘yan biki. Idan sun shiga gida sai su yi wa Daudu shimfida can waje daya, su sa Maryama tana daukar abinci tana kai masa, tana mai nuna yadda ya kamata mace ta yi wa mijinta, kamar murmushi, ladabi da sauransu. Kuma duk jama’a gida sun taru suna kallo ana raha. Bayan irin wadannan wasannin gargajiya na yara ’yan mata da samari, akwai kuma wadansu al’adu na manya da sukan yi masu siffar wasan kwaikwayo. A cikin irin wadannan al’adu na gargajiya akwai: Bori: Hanyar addinin gargajiya ce na Hausawa tun asali. Hausawa kan yi amfani da Bori don neman biyan buka ta ko kubuta daga wata cuta. Idan muka dauki hawan bori da kuma irin yanke-yanken da ake yi wa iskoki don neman waraka daga wata cuta wadda ta shige wa mutane duhu. Irin wannan biki na bori da kuma girka za a iya kwatanta shi da bikin addinin Girkawa na bauta wa wadansu irin gumaka, wanda sukan yi lokaci-lokaci na shekara, kamar lokacin hunturu da kuma lokacin bazara. Kuma wannan al’ada ta Girkawa (Greeks) tsohuwar al’ada ce kwarai, don ana ganin wannan ya fara ne a wajan karni na 5 (biyar) watau kafin haihuwar Annabi Isah (ma’ana sama da shekara dubu biyu). Idan aka dubi cikin Encyclopaedia Britanica, a littafi na 15 (sha biyar) kuma a shafi na 983 (dari tara da tamanin da uku) an nuna cewa buduri da ake yi na wannan bautar gumaka a gaban ‘yan kallo shi ne ya haifi asalin wasan kwaikwayo rubutacce na kasar Italiya wanda daga gare shi ne kasashen Turai suka gaji wasan kwaikwayo. Shi kuma Bori irin na kasashen Hausa, wanda ake neman magani ko kubuta daga wata riga ta karuma mutum, musamman na wata cuta mai rikidarwa akan shirya wa majinyacin girka, a yi gagarumin biki, boka da sauran ‘yan bori ‘yan uwansa suna hawa iskoki daban-daban ana kada masu garaya ko goge ko molo. A al’adar girka kowace irin iska da nata irin kida, su kuma da irin magana ko karar da za su yi, mai nuna kwaikwayon irin iskar da ta ke kansu a daidai wannan lokaci. A irin wadannan iskoki akwai kuturu, malam Alhaji, da doguwa, da Halima ‘yar buzaye, danko da kuma sarkin rafi da dai sauransu. Misali idan dan bori ya hau iskar kuturu, sai ya dinga karaji irin na kutare, ya kadandame yatsu kamar kuturu. Irin kidan da ake yi wa masu iskoki yana da tasiri kan fitar da hankalinsu ke yi, suna tumami, suna tsalle, suna karaji, suna faduwa warwas a kasa kumfa na fita daga bakinsu su sandare. A lokacin da suka kai ga hakan to sun fita a matsayinsu na mutane sun zama iskar da take kansu. Dabo-Dabo: Wannan wasa ne na nunin mutum-mutumi. Mutane kimanin hudu ne suke yawo tare da makada ganga biyu suna nuna dabo. A kan yi nunin irin wannan wasa a bakin kasuwa ko wurin taron mutane, su shaci fili su kafa sanduna hudu. Tsakanin kowace sanda akwai fadin kimanin kafa biyar kuma tsawon kowace sanda kimanin kafa biyu da rabi, sai su kawo babbar riga su kifa ta kan wannan tsaikon ta rufe shi sosai ya yi kamar dan daki da kofar rigar a sama. Sai mai nunin dabon ya shiga cikin tsaikon an kewaye shi masu kida na yi, ga masu kallo suna kallo, kowa ya kagara ya ga abin da zai nuna. Lokacin da ya shiga sai ya dinga fito da wadansu ‘yan mutane kamar ‘yan mutum-mutumi sai ka ji suna magana. Wani lokaci ya nuno saurayi da budurwa suna zance, ko ya nuno mutum wanda wani malami ya yaudara ya sa shi yin rawa. Da ya farga da cewa yaudarar shi aka yi, sai ya kai kara wajan alkali wanda zai yanke musu hukunci, ko kuma wannan mai nuni ya nuno ‘yan dambe za su kara. Kalankuwa: Wasan kalankuwa, wasa ne da samari da ‘yan mata kan shirya suna kwaikwayon aikin mulki da shari’a a karkara cikin kaka, bayan an girbe abinci da sauran amfanin kaka an mai suwa gida. Dagacin gari shi ne kan nada sarkin Samari, shi kuma sarkin samari shi ne zai nada mataimakansa kamar su galadima, madaki, waziri, alkali, gwamna da sauran su. ‘Yan mata su suke zabin sarauniya a tsakaninsu. Sai a zabi fili a kofar fada ko bakin kasuwa, ko wani fili. Sai sarkin samari ya zo ya kafa fadarsa, can waje guda kuwa ga makada, ana kida taken sarkin samari da na mataimakansa, ana he, ana ba su kudi. A cikin filin idan wani saurayi ya bata da wani abokinsa ko budurwarsa, sai a kai su gaban sarkin samari wanda zai bi diddigin laifin. Idan ya ga abin sai an hada da shari’a, sai ya aika da su gaban alkali don yanke hukunci. Ana daukar kimanin kwana hudu ana yin wannan bikin kalankuwa na yammacin kowace rana. A cikin kwanaki hudu na kalankuwa dagacin gari kan nemi sarkin samari da su yi wani aikin gayya, kuma akan hukunta duk wanda ya ki yin aikin a lokacin wannan bikin. Sauran misalai: Akwai sauran misalai da dama na al’adun Hausawa masu kama da wasan kwaikwayon Hausa. Misali, ‘yankama da ‘yan gambara sukan kwaikwayi halaye da dabi’u na mutane daban-daban a cikin wasansu don ban dariya. Wawan sarki shi ma yakan kwatanta siffofin abubuwa daban-daban wajen sa sarki raha. ‘Yan hoto kuma su ne masu bi wuri-wuri suna nuna gwanintar sarrafa garma ana yi musu kidan manoma, da dai kama-kaman irin wadannan al’adu da dama na Hausawa. WASANNIN KWAIKWAYO NA MAJIGI DA REDIYO Ci gaban da aka samu dangane da rubuta wasan kwaikwayon Hausa ana kuma aiwatarwa a makarantu da dandali shi ya sa ko da abubuwan zamani irin su majigi da rediyo suka kutso kai a kasar Hausa sai aka sami damar mayar da yawancin wasannin kwaikwayon Hausa zuwa a aikace ko dai a saurara a rediyo ko a gani ta dodon bango, wato majigi. Shi dai majigi shi ne ya fara kutso kai, tun daga shekarun 1950, an kuma zo da shh ne domin yin farfaganda da wayar da kan mutane domin su amince da al’amurran da suka shafi mulkin mallaka, musamman wajen noma da kiwon lafiya. Yawancin shirin wasannin kwaikwayon ana yin su ne don jama’a su ga fa’idar noman kudi ba na ci ba. Alal misali noman audugu da gyada da kuma amfani da takin zamani. Ana gabatar da majigi ne a kofar fadar Sarko ko bakin kasuwa ko filin kwallo ko wani wuri makamancin haka. Su kuwa gidajen rediyo sun zama ruwan dare daga shekarar 1960 sukan tanadi ‘yan wasa masu zuwa su aiwatar da wasannin domin jin dadin jama'a masu saurare, wata sa'a kuma ire-iren wadannan kungiyoyin gama-kai sukan je da nasu wasan don a ba su dama su gudanar, ta haka sai wasannin kwaikwayo suka kara samun martaba da daukaka a idon jama'a, yau a yi wannan sabon shiri da sunan sa daban, gobe wani ya fito, amma jama'a ba sa mantawa da su. Wasannin Gidan Rediyo Irin wadannan wasanni jin su kawai ake yi amma ba a ganin masu aiwatarwa. Watau suna irin wadannan wasanni tsara su ake yi a rubuta a kuma kwatanta su a cikin akwatin rediyo ta hanyar daukar sauti. Misalin irin wadannan wasanni: ‘Yau da Gobe na gidan rediyon Rima, da ke Sakkwato, da Samanja Mazan Fama, da Duniya Budurwar wawa na gidan rediyon tarayya na Kaduna, da kuma ‘Taskira Asirin Mai Daki’ da Bakandamiya na rediyon jahar Katsina. Akwai kuma wasan ‘Duman Kada... na Rima rediyo Sakkwato da sauransu. Su irin wadannan wasanni akan ba su wani suna ne, amma kuma idan wannan wasa ya yi yayi ya gama akan jingine shi a waje guda a kuma sake wani wasa da kuma salon suna wanda zai dace da yanayi da kuma lokacin da ake ciki. Su dai irin wadannan wasannin akan shirya su ne domin ilmantarwa, ko fadakarwa, ko gargadi, ko nishadantarwa ga jama’a a kan fa’ida ko muni ko kuma illar wani abu. Wasanni Gidan Talbijin Wasannin gidan talbijin su ne ake jin sauti kuma a kalli hoto. Irin wadannan wasanni su ma akan rubuta su ne, sa’annan a shirya a aiwatar da su tare da mutane a cikin akwatunan talbijin ko a fina-finan majigi. Ana tsara irin wadannan wasannin domin kwatanta halayyar rayuwar al’umma cikin wasa domin bayyana wadansu matsalolin da ke tattare da rayuwa. Wasannin gidan talbijin irin wadannan sun hada da wasan “Baban Larai da Idon Matambayi na gidan talbijin na Sakkwato, da Taskira da Kuliya manta sabo da Dankurma da Karo da Goma da Kaikayi da kuma Kwaryar Kira na gidan talbijin na Kano. Haka kuma akwai “Bakan Gizo na gidan talbijin na Kano mallakar jiha. Kuma akwai “Baba Soja da Kwashi kwaram da Golobo” na gidan talbijin tarayya da ke Sakkwato. Da yake dama dukkanin wasannin akwai alamar ana zama ne a rubuta su, sa'annan a gabatar, shi ya sa wadansu daga cikin wasannin suka koma littafi daga baya. Alal misali, Zamanin namu da Jatau na Kyallu na Shu;aibu Makarfi, an buga su daga baya. Haka kuma Zaman duniya Iyawa ne na Yusuf Ladan, wannan ya nuna mana cewa kamar yadda ake samu a kasashe da suka ci gaba ta fannin wasan kwaikwayo a gidajen rediyo da talbijin, a kasar Hausa ma wasannin a rubuce suke, ba a dandali kawai ake yi da ka ba, a ci gaba da aiwatarwa. Wani abin la'akari a nan shi ne, yawancin wasannin ba sa kasancewa na dindindin, yau a yi wannan, gobe a yi wancan, wasu su bace su dawo, wasu su bace har abada, sai dai su bar sunayen gwanaye ko wadanda suka yi suna a wasan, suna watayawa, alal misali: Kasimu Yero - Karambana Alh. Usman B. Pategi - Samanja Dauda Galadanchi - Kuliya Mustapha Muhammad - Dan Haki Umaru Ilu Ambursa - Baba Soja Umaru Danjuma Katsina - Kasagi WASANNIN KWAIKWAYO A BIDIYO Sinima ko fim a wasan Hausa sabuwar al'ada ce, wadda ba ta shigo cikin kasar ba sai a tsakanin shekarun 1950-1960. A can da majigi ne da gwamnatocin jihohi ke nunawa a filin kallo, kofar fada ko kuma a makarantun firamare, yawancinsu majigin a wancan lokacin bai wuce na koyar da tsafta ba ko noman gyada da auduga da sauran ayyukan farfaganda na mulkin mallaka. Daga baya sai aka dinga hadawa da na Cow Boy, wato Amurka don a nishadantar da masu kallo. Sha'awar da jama'a suka nuna na kallon wannan majigi, da kuma ‘yan kasa da suka fara fitowa fili wajen gabatar da wasannin majigi, kamar su Baban Larai ya sa wasu masu ido a Naira suka ga ai za su iya samun kudi ta wannan hanya, sai suka shiga gina gidajen sinima a biranen Kano, Kaduna, Katsina, Sakkwato da sauransu. Ta haka ne al'adar zuwa sinima don kallon fim din indiya da Amurka da Chanis ta kafu, ta kuma yi kaka-gida. Yara tun suna kanana sun saba shiga sinima, sun san ‘yan wasan Indiya da Amurka har ma suke kwaikwayon su. Da kasashen da suka ci gaba suka shigo da bidiyo, sai aka raja'a zuwa ga bidiyon domin ta fi saukin gudanar da al’amurra, don ba sai ka je wajen kallo ba a gida da kai da iyalanka za ku yi kallon duk abin da kuke so. Wannan cigaba, shi ya haifar da ‘yan gida masu neman kudi suka ga cewa lallai za a iya samun kudi ta haka, sai yawancin kungiyoyin wasannin kwaikwayon Hausa da kungiyoyin marubuta littatafai, musamman na Adabin Kasuwar Kano suka auka ga wannan sana'a, wadda a halin yanzu ta yi suna da samun karbuwa wajen jama'a. Yawancin fim din bidiyo da ake da su a yanzu sun samu ne ta fuskar littatafan Adabin Kasuwar Kano, wasu kuma an samar da su ne ta hanyar shirya labari mai ban sha'awa, ba tare da tsarin wasan kwaikwayo ba ko kuma labari don dai bidiyon kawai. SAUYIN YANAYIN WASANNIN KWAIKWAYON HAUSA Daga ire-iren wasannin kwaikwayon Hausa da muka nazarta, mun ga cewa, wadansu na baka ne ko kuma na gargajiya, wadansu zamani ya kawo su, wato rubutu (musamman na boko). Wasu ana aiwatar da su a gidajen rediyo da talbijin da bidiyo. Wani abin sha'awa shi ne yadda wadansu marubutan Hausa suka fassaro wadansu littatafan wasannin kwaikwayon Turawa da Larabawa zuwa Hausa, saboda a kwatanta tsarinsu da kara fahimtar sigogin wasan kwaikwayo. 1. Ibrahim Yaro Yahaya ya fassara Twelfth Night na Shakespeare daga ingilishi zuwa Hausa a matsayin Daren Sha Biyu. 2. Ahmed Sabir ya fassara littafin Ahlul-Kaf na Tawfiq Al-Hakim daga Larabci zuwa Hausa a matsayin Mutanen Kogo 3. Dahiru Idris shi ma ya fassaro littafin Merchant of Venice na Shakespeare zuwa Hausa da sunan Matsolon Attajiri Baya ga wadannan, akwai kuma littattafan labaran Hausa da dama da aka mayar wasan kwaikwayo, aka kuma aiwatar a dandali da gidajen talbijin 1. Shaihu Umar na Tafawa Balewa wanda Umar Ladan da Dexter Lyndersay suka baddalar zuwa Shaihu Umar. 2. Ruwan Bagaja da Ahmad Amfani ya baddala a bidiyo daga Hukumar Fina-finai Ta Jos ta mayar fim. 3. Magana Jari ce da NTA Lagos ta mayar wasan kwaikwayo a talbijin da Ingilishi da kuma na Hausa da NTA Kaduna ta baddalo.

2 comments:

  1. Gaskiya mun gode da wannan bayanai masu dauke da fa'idoji

    ReplyDelete
  2. Wannan gaskiya ne, Muna godiya ubangiji Allah ya Kara basira

    ReplyDelete