Monday, 1 July 2013

Takaitaccen Bayani Game Da Wakar Hausa

TAKAITACCEN BAYANI GAME DA RUBUTATTAR WAKAR HAUSA MA'ANAR WAKA A HAUSA Kamar yadda muka saba sai mu soma da kokarin gane abin da kalmar waka ke nufi ga mutumin da ya tashi a kasar Hausa. Idan ka hadu da mutum a kasuwa ko bakin titi ko a wani wuri na gargajiya ka tambaye shi abin da ake nufi da waka da Hausa abin da zai iya fada maka ba zai wuce, ‘yawan son yin abu ba’ ko kuma ‘jan magana ko nanata zance kan wani batu da ake son yi.’ Shi ya sa za ka ji mutum na cewa kullum ina wakar zan zo mu gaisa amma abin ya faskara. Ma’ana yana ta sakar zuci na son zuwa inda wancan aboki yake, amma bai je ba. Ke nan wakar abu na nufin ka yi ta kururuta batu ko jan batun a zuci na tsawon lokaci, amma ba a aikatawa. Ke nan idan aka natsu aka yi nazarin waka a zahiri za a ga wani zance ne ko magana da ake ta ja har ta yi tsawon gaske. Amma ga masana waka na nufin abubuwa da yawa. Ga Dangambo, (2007) waka na nufin sakon da aka gina bisa tsararriyar ka’ida ta baiti ko dango ta hanyar rerawa da kuma samun kari ko bahari da amsa amo ko kafiya. Ke nan za a iya cewa waka ta bambanta da zance na yau da kullum ta fuskar tsarawa da ka’idoji. Ana iya raba waka zuwa gida biyu, akwai ta baka da kuma rubutacciya. Ita wakar baka ita ce wadda mawakan baka irin su Shata da Dankwairo da Choge mai Amada kan yi. Haka akwai wakokin baka na dandali da ‘yan mata da na dabe da daka da sauran su. Dukkan wadannan sun wanzu ne kafin zuwan baki a kasar Hausa. Saboda haka ko da baki suka zo, musamman Larabawa abin da suka fi mayar da hankali kai shi ne canza wa waka riga daga gargajiya zuwa zamani, wato Ajami da Larabci da kuma Hausar Boko. BAYANI GAME DA RUBUTACCIYAR WAKA A ZAMANIN LARABAWA Bari mu bi a takaice mu ga shin yaya rubutacciyar waka ta kasance bayan zuwan rubutu. Kamar yadda masana suka nuna hanya ta farko da aka samu karatu da rubutu a kasar Hausa ita ce ta hanyar shigowar Musulunci. Masana tarihi sun nuna cewa Musulunci ya shigo kasar Hausa tun zamani mai tsawo. Sarrafawar da Hausawa suka yi wa haruffan Larabci ta hanyar kwaskwarima da kago haruffan Hausa a ajamance, wadanda babu su a Larabci misali. /b/, /ky/,/kw/,/ts/,/‘y/ da sauran su, shi ya haifar da rubutun ajamin Hausa. Rubutu ya kankama, musamman daga karni na 17 zuwa na 19, domin an sami bunkasar ayyukan addini a rubutun ajami ta hanyar fassara littattafai da sauran ayyukan addini da kuma rubuta wakokin addinin cikin ajami domin fadakarwa da ilmantarwa. Hasashen binciko lokacin da aka fara rubuta waka da Hausar ajami ya nuna cewa a wajajen karni na 17 ne aka fara. Masana sun kafa hujjarsu ne da cewa akwai wasu wakoki na Hausa wadanda suka bayyana tun kafin haifuwar su Mujaddadi Shehu Usmanu. A littafin Yahaya (1988) ya yi bayanin cewa ana tsammanin akwai dadaddun wakoki wadanda aka rubuta da Hausar ajami misali ‘Shi’ir Hausa’ da ‘Wakar Jamuyah’ na Sheikh Ahmad Tila da ‘Tarikh El- Sudan’ wadda Sheikh Abdulkadir Tafa ya rubuta da Hausa, amma sunan wakar ya sa da Larabci. Haka nan akwai waka mai suna ‘Shi’ir Hausa’ ta Abdurrahman Tajuddin da mai suna ‘Sartse’ ta Mallam Alin Abubakar bin Kutunkura da kuma wasu wakoki guda uku wadanda aka sa musu suna ‘Wakar Hausa’ amma ba a rubuta wanda ya yi su ba. A karni na 17/18 akwai waka daya ta Wali dan Masani wadda ya rubuta mai suna ‘Wakar yakin Badar’. Wannan waka ta yabon Annabi (SAW) ce da kuma bayanin yadda Yakin Badar ya kasance. Bayan wannan waka an ci gaba da samun wasu wakoki a karni na 18 wadanda jigonsu suka ginu a kan addinin Musulunci. Akwai wani babban malami Malam Shi’itu dan Abdurra’uf wanda ya rubuta wakoki cikin Larabci da Hausa. Cikin wakokinsa na Hausa akwai ‘Jiddul Ajizi’ Ba’ajamiya, an kira ta Ba’ajamiya saboda fassarar ‘Jiddul Ajizi’ ce wadda ya rubuta da Larabci. Ita wannan waka littafin Mukhtasar ne, mawakin ya fassara a wake da Larabci da Hausa. Malam Shi’itu Dan Abdurra’uf ya ci gaba da rubuta wakoki wadanda jigonsu duka na addini ne, kamar ‘Wakar Tuba’ (Jimiya) saboda wakar na karewa da harafin Ja, da ‘Wawiya’ wadda harafinta ke karewa da harafin Wa. A karni na 19 ne aka sami ilmi ya kara zurfafa, karatu da rubutu suka kara bunkasa, ayyukan addini suka ci gaba da wanzuwa , rubutu da ajami ya kara bunkasa. Duk wannan ya faru ne saboda bullowar Mujadaddi Shehu Usmanu Danfodiyo a kasar Hausa. Shehu ya yi karatu mai zurfi, kuma saboda ilminsa da tsoron Allah da buri na gyaran al’umma sai Allah ya ba shi daukaka ya kuma cika masa wannan buri na gyaran al’umma ta hanyar ilmantarwa da wa’azantar da jama’a da yakin duk wata hanya ta alfasha da yin fito-na-fito da sarakunan Hausa masu zalunci a kan talakawa. Shehu ya tarar da al’ummar da ke cike da ayyukan masha’a da sharholiya, don haka ya tashi tsaye don kawo adalci da kawar da barna. Ta haka ne da shi da iyalansa da mabiyansa suka yi jihadi, suka kafa Daular Musulunci, suka kafa al’umma ta jama’a masu bin gaskiya da tsarin Musulunci. Wannan yunkuri da suka yi ba zai dore ba sai da samuwar ayyuka na ilmi, saboda haka Shehu Usmanu da kanensa Abdullahi Fodiyo da ‘ya’yansa Muhammadu Bello da Isan Kware da Abubakar Atiku da Nana Asma’u da sauran su, suka tashi tsaye domin yin rubuce – rubuce na fadakarwa. Haka nan sauran malaman jihadi suka bi wannan hanya don karantar da al’ummarsu. Malaman jihadi sun yi namijin kokari wajen yin rubuce – rubuce da suka shafi fannonin addini kamar Tauhidi da Fikihu da Tarihi da siyasar Musulunci da sauran su. An yi bayanin cewa Shehu Usmanu shi kadai ya wallafa wakoki fiye da dari hudu da tamanin a cikin harshen Larabci da Fillanci da Hausa. Haka nan sauran malamai na wannan karni sun dukufa, kuma sun yi amfani da rubutacciyar waka wajen watsa addinin Musulunci da kau da zaluncin sarakuna da shugabanni da horo da alheri da hani da mugun aiki da ilmantarwa. Ke nan a wannan karni ne aka fi samun bunkasar rubutattun wakoki a kan yabon Ubangiji da madahu da fikihu da wa’azi da sauran fannoni na rayuwa. Masu jihadi sun wallafa wakoki a kan addini domin kauce wa wakokin hululu. Shehu Usmanu da makarrabansa sun yi rubutun wakoki da dama, misali Shehu ya rubuta wakar “Ma’ama’are” da “Tabban Hakikan”. Malam Abdullahi kuwa ya yi wakar “Murnar cin Birnin Alkalawa” da wakar “Tsarin Mulki na Musulunci”. Sun ci gaba da rubuta wakokin ilmantar da jama’a a kan ma’amala da rayuwar Musulunci da mulki da kasuwanci, misali, wakar “Alhakin Mumuni Bisa Mumini” ta Isan Kware da wakar “Gargadi Ga Masu Shan Azumi” ta Nana Asma’u, (Sa’id, 1978). Bayan su Shehu sun yi aiki tukuru sun sami gyara al’umma, daga baya kuma sai shagala ta fara kunno kai, bidi’o’i suka fara yaduwa; sai malamai suka sake tashi tsaye don fadakar da tunatar da jama’a ta hanyar rubuta wakoki, misali Waziri Buhari wanda ya rubuta waka a kan “Juye – juyen Zamani” da wakar “Shirin Guzuri Don Karatowar Mutuwa”. A takaice za a iya cewa a karni na 19 ne aka sami habaka da bunkasar rubutacciyar wakar Hausa, ba wani abu ya sa haka ba sai don saboda zaman ta mafi sauki wajen isar da sakon addini da ilmantar da jama’a. A littafin, ya yi bayanin cewa masu jihadi sun yi rubuce - rubucen wakoki a kan jigogi 10, wato Tauhidi da Sira da Furu’a da Madahu da Nujumu da Hisabi da Wa’azi da Alhini da Tawassuli da Ilmantarwa. Kusan dukkan wadannan wakoki suna da mabudi da marufi, wato farawa da rufewa da ambaton Allah da salatin Annabi. Haka nan tsarinsu na amsa-amo da ma’auninsu duk irin na wakokin Larabci ne. BAYANI GAME DA RUBUTACCIYAR WAKA A ZAMANIN TURAWA Karni na 20, karni ne da Turawan Ingila, ‘yan mulkin mallaka suka shigo Arewacin Nijeriya. A farkon karnin ne, suka ci wannan yanki da yaki suka rusa daular Musulunci suka kafa makarantu domin koyar da ilmin boko wato maimakon amfani da haruffan Larabci wajen rubuta ajamin Hausa, sai suka kawo amfani da harufan Latinanci watau na Romawa wajen karatu da rubutu. Haka nan zuwan Turawa ya kawo sauye – sauye ga rayuwar Hausawa ta fannin tsarin mulki da ilmi da al’ada da siyasa da kere - kere da sauransu. Tun da al’amarin tsarin mulki da ilmi ya koma hannun Turawan mulkin mallaka sai suka dukufa wajen samar da littattafan da za a yi amfani da su wajen koyarwa a makarantun boko, suka kuma fara rubuce – rubucen adabin Hausa, misali. J.F Schon ya rubuta littafin Magana Hausa da African Proverbs da sauran su; C.H. Robinson kuwa ya rubuta littafin Specimens of Hausa literature; Frank Edgar ya rubuta nasa littafi na Tatsuniyoyi na Hausa. Turawa sun ci gaba da kokarin bunkasa karatun boko ta hanyar bude makarantu a manyan garuruwa kamar Kano da Sakkwato da Katsina, kuma harshen sadarwa shi ne harshen Hausa. Da abu ya yi nisa ne aka kafa Hukumar Fassara da Talifi da Kamfanin Norla da Hukumar Gaskiya da sauran su domin samar da ayyuka na ilmi. Wadannan sauye–sauyen da aka samu a karni na ashirin sun kawo sauye–sauye a fannin rubutun waka. A karni na sha tara yawancin wakokin Hausa da aka rubuta jigoginsu na addini ne, haka nan tsarin rubuta su, amma a karni na ashirin da kida ya sauya sai rawa ma ta sauya, domin duk da cewa an ci gaba da taka tsohuwar rawa, wato rubutun wakoki a kan addini, sai sabon salo ya bayyana na rubuta wakoki wadanda ba na addini ba. Haka nan marubuta waka sai suka fara gamin - gambiza, su dau tsarin addini a wani bangare su kawo wanda ba na addini ba a wani bangare. Cikin marubutan da suka fara bude kofa game da wannan salo akwai Sarkin Zazzau Aliyu dan Sidi, domin duk da yake wakokinsa sun kasance na wa’azi da gargadi da ilimi, amma ya kawo wani salo wanda ya saba wa salon wakokin karni na sha tara. Wannan bayani ya fito fili a wakarsa ta “Tabarkoko”, wadda wasu ke kira “Tahamisin Aliyu Dansidi”, inda ya bude wakar a baiti na farko ba da ambaton Allah ko salati ga Annabi ba, yana cewa: Aboka zo nan mu bata, Ka dubi dan dai ga wata, Wada daban da batta, Haske na rana da wata, Ba za su zam daidai ba. (N.N.P.C., 1980)​ Haka nan jigon wakar sai ya kasance habaici. A baiti na sha bakwai yana cewa; Kwaddo ina kadangare?​ Na ji kafarsa ta kare, Ya bar diyanshi gangare, In ya yi nan sai a tare, ​Ni ban gano zai kai ba. (N.N.P.C., 1980) Sarkin Zazzau Aliyu dan Sidi ya rubuta wata waka mai suna “Wakar zuwa Birnin Kano”, a inda ya yi bayanin kasaitaccen taron da aka yi a wannan gari. ​A karni na ashirin marubuta sun ci gaba da rubuta wakoki a kan jigogi na addini, akwai irin su Aliyu Namangi da Nasiru Kabara da Akilu Aliyu da sauran su. Duk da an ci gaba da wallafa wakoki cikin Hausar ajami, masu ilmin boko suna rubuta wakokinsu da Hausar boko kuma suna rubutu a kan jigogin addini da sauran al’amurra. An yi rubutu a kan neman ilmin boko da siyasar zamani da soyayya da kiwon lafiya da harkokin noma da na tattalin arziki da sauran su. Ke nan za a iya cewa a wannan karni na ashirin aka sami ‘yan boko masu kishin addininsu da kasarsu da al’adarsu, suka tashi tsaye wajen fadakar da al’umma ta hanyar rubuta wakoki, cikin su akwai Mu’azu Hadeja da kuma wasu irin su Sa’adu Zungur, wanda ya rubuta wakar ‘Arewa Jumhuriya ko Mulukiya’ da Akilu Aliyu da ya rubuta ‘Hausa mai ban haushi’ da Gambo Hawaja mai wakar, ‘A yau ba maki NEPU sai wawa’. Sai kuma Na’ibi Sulaiman Wali mai wakar, ‘Damina’ da Hauwa Gwaram wadda ta rubuta wakar, ‘Ta’aziyar Sardauna’ da sauran mawaka wadanda suka rubuta wakoki a kan jigogi daban – daban.

No comments:

Post a Comment