Wednesday 3 July 2013

Mata Marubuta A Faifan Nazari

MATA MARUBUTA A BISA FAIFAN NAZARI: TSOKACI DAGA ADABIN HAUSA Tare da Balbasatu Ibrahim (Mrs) Gabatarwa Tun da Allah ya halicci duniya ya jarabi dan adam da abubuwa guda uku. Wadannan abubuwa kuwa su ne yare, dukiya, da jinsi. Har yau da muke raye wadannan abubuwa na ci gaba da ci wa Dan adam tuwo a kwarya. Dalili kuwa shi ne a duk sanda aka ce wannan shi ne yaren mutum, to zai yi kokarin ganin cewa martaba da kwarjinin wannan yaren nasa sun fi na kowa. Alal misali ja-in-jar da aka yi ta yi tsakanin Turawa da bakar fata a kasar Afrika ta Kudu a shekarun baya da kuma kisan gillar da ‘yan kabilar Hutu suka yi wa ‘yan kabilan Tutsi a kasar Ruwanda a shekara 1989, haka kuma rikicin da ake ciki yin a halin yanzu tsakanin Larabawa da bakar fata a Darfur ta kasar Sudan sun kasance misalai na irin yadda yare ke tayar da takaddama tsakanin mutane. Ita ma dukiya ko mulki kan haifar da zalunci da danniya tsakanin masu hannu da shuni da talakawa a cikin al’umma. Idan muka dubi irin tsare-tsaren siyasar da aka yi ta yi a kasashen Turai, kamar tsarin jari-hujja da na gurguzu da kuma na dimukradiyya da ake ikirari a yanzu, sai mu ga har yanzu ba su hutar da talakan ba, sai kara tsotse shi ake yi, ana kara wa masu karfi, karfi. Matsala ta uku kuwa ita ce wariyar jinsi, wadda Jennifer (1985) ta yi bayanni cewa “ta wanzu ne a sanadiyar ra’ayi ko akidar nan ta cewa “akwai bambancin fifiko tsakanin namiji da mace a cikin al’umma”. Wannan matsalar ita ce take tashe a halin yanzu a ko’ina cikin duniya. Tashenta kuwa ya hada da fagen siyasa da na tattalin arziki da na yanayin zamantakewa da fasaha da ilmi da sauran su. A takaice babu bangaren rayuwar da matsalar wariyar jinsi ba ta kutsa kai ba. Shigowar wannan matsala ta haifar da ka-ce-na-ce tsakanin manazarta ciki kuwa har da na adabi. Ganin cewa bincikena ya shafi harkar bambancin da ake iya samu tsakanin mace da namiji ta bangaren rubuce-rubuce ko kuma adabi, na ya dace na soma da fahimtar yadda wannan takaddama ta samo asali da yadda take taimakawa wajen ginawa da raya harkar nazarin ayyukan mata. Daga ‘yan karance-karancen da na yi, sai na fahimci cewa duk da cewa ana ta hayagaga kan wannan fage na wariyar jinsin ba a cika aza tunanin fagen bisa tafarkin da ya dace ba. Wannan na daga cikin abin ya shiga cikin zuciyata a lokacin da na soma tunanin wannan bincike. Shi ya sa ma na na ce a zuciyata wai me zai hana in dauki fanni daya daga cikin abubuwan da suka shafi mata in gudanar da zuzzurfan bincike a kan sa, ta yadda ni ma zan iya bada gudunmuwa game da irin gudunmuwar da matan Hausawa ke bayarwa ta fuskar adabi. Sai dai kafin na shiga cikin gonar aikin nawa ya kamata mu san cewa wannan hayaniya ta wariyar jinsi ba sabuwar aba ba ce, ta dade da kutso kai a tsakanin al’umma. Wasu masana na ganin ewa ta taso ne tun a wajajen shekarar 1960 har zuwa shekara 1975 lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta bullo da shirinta mai take “Shekarar Mata” da na “Shekarun Mata”a shekarar 1985 aka yi taron Majalisar na Nairobi, sannan aka yi babban taro wanda yake shi ne na hudu irinsa da aka taba yi a kan mata duk duniya, a birnin Beijing na kasar Sin. Wannan taro an yi masa lakabi da “ Taron Beinjing” (Beinjing Conference), wanda shi a shekarar 1995 aka gudanar da shi. Wannan taro ya tattara mahalarta daga ko’ina cikin duniya, ya kuma yanke shawara a kan sha’anin daidaita jinsi na in-ba-ka-yi ba-ni wuri. Wato tun daga wannan taro ne maganar daidaita jinsi take a bakin kowa;‘yan jarida ne ko masana ko manazarta ko marubuta. Kafin in ci gaba, na ga ya dace a san menene jinsi da kuma asalin ita kanta matsalar a da, da kuma yanzu a cikin al’ummomi daban-daban. Jinsi kamar yadda aka sani shi ne bambancin da ke tsakanin namiji da mace a halicce. Wanda kuma ya shafi tsarin rayuwarsu ta zahiri da badini. Haka kuma wadannan bambance-bambancen na canzawa da canjin zamani da rayuwar yau da kullum, Graddol (1993) daga Kassam (1996). Kodayake wasu masana suna ganin ma’anar jinsi ba ta tsaya nan ba kawai, alal misali a ganin De Beauvair (1973:301) “jinsi abu ne wanda mutum ke iya zabar wa kansa”. Ita a ganinta irin rayuwar da mutum ya zabar wa kansa ita ce take nuna jinsinsa, ba wai yadda aka halicce shi ba. Namiji na iya daukar rayuwa irin ta mata, haka kuma mace na iya zabar rayuwa irin ta maza, ko da kuwa al’umma ta kyamaci wannan abu. Haka su kuma Butler (1986.36)da Zimmerman (1991: 13-15) cewa suka yi al’adu da dabi’un mutum ko na al’ummarsa, su ne ke da alhakin bayyana jinsinsa da kuma matsayinsa. Ita kuwa Riley (1997; 2-6) tana ganin ma’anar jinsi ta wuce bambanci halitta kawai, ta hada da bambace-bambancen da ake samu ta bangaren abubuwan da al’umma ke shatawa a al’adance a kan yadda ya kamata mata ko maza su kasance. Haka kuma wadannan ka’idojin sun shafi kowane bangare na rayuwa, kamar yanayin zamantakewa na yau da kullun da tattalin arziki da siyasa da neman ilmi da makamantan su. Har wa yau kuma wadannan tsare-tsare na al’ada su ne suke haifar da matsalar daukakar wani jinsi a kan wani ko danniyar da ake yi wa jinsin mata a cikin wata al’umma. Haka kuma ana bayyana jinsi a matsayin tsare-tsaren al`umma a kan da`bi`u da ayyuka da matsayin da ake ganin ya dace da maza da wadanda suka fi dacewa da mata. A fahimtata ana iya gwama wadannan ra’ayoyin na masana a kan ma’anar “jinsi” a tayar da ma’ana daya kamar haka, mai nufin bambancin halitta tsakanin mace da maniji da kuma dukkan sakamakon da wannan zai haifar ta fuskar rayuwar wadannan halitta guda biyu a doron kasa ta fuskar wadansu al’adu da ake shatawa ko gindayawa domin a cimma wadansu manufofi na siyasa ko zamantakewa.Bisa irin wannan tunani ne za mu fahimci cewa wariya ko bambancin jinsi y hada bambancin halitta da kuma bambancin rawar da kowane bangare zai taka ta fuskar tattalin arziki ko al’ada ko siyasa da dai duk wata fuska ta rayuwa. Sai dai wannan bayani bai kasance an yi shi haka nan sakayau ba, ya samu tubalin gina shi tun da dadewa, kama daga addini ko siasa ko canjin rayuwa ta yau da kullum. Saboda haka ya dace mu koma cikin tarihi domin fahimtar yadda wannan tunani ya ginu da kuma yadda ake daukar ko kuma irin matsayin da ake ba wa jinsin mata cikin al’ummomin daban-daban ta fuskoki daban-daban . MATA A ZAMANIN JAHILIYYA Bari mu koma cikin tarihi, mu kuma soma da nan kusa, musamman wanda ya shafi addinin matan da za mu yi nazari, wato Musulunci. Za mu ga tun a zamanin jahiliyyar Larabawa8 ba a dauki mace a bakin komai ba. Ana ganin an hallice ta kawai domin ta yi wa maza hidima. Haka kuma ana iya sarrafa ta yadda aka ga dama. Alal misali, zamanin jahiliyyar Larabawa sun kasa halitta ga baki daya zuwa gida uku, kaso na daya su ne mutane, kashi na biyu kuwa su ba su kai matsayin mutane ba, amma sun dara dabba, na uku kuwa su ne dabbobi. Halittar da aka dauka ba ta kai mutum ba, amma ta fi dabba ita ce mace. Saboda su a wurinsu mata ba su da kima, ba su da wani zabi a rayuwa sai yadda aka yi da su. Ana aurar da su yadda aka ga dama ko kuma a saka su yin karuwanci ko aikin wahala ba tare da an biya su lada ba. Har ma don wulakanci gadonsu ake yi kamar dukiya. Wato idan mijin mace ya mutu, idan yana da wani da wanda ba nata ba sai ya gaje ta. A nan yana da damar ya ajiye ta a matsayin matarsa ko baiwa ko kuma ya sayar da ita. Haka kuma namiji yana da damar ajiye mace ko nawa yake bukata ba tare da wata ka’ida ba, saboda irin wulakanci da kaskanci da suka lika wa mata, har ya kai suna binne ‘ya’yansu mata masu rai tun suna jarirai idan ba su bukata. A tsohuwar daular Indiya kuwa a al’adar Hindu, an dauki cewa namiji shi ne ubangijin matarsa (abin bautarta). Idan ya mutu a tare za a kone gawarsu, alhali tana da rai. Haka kuma har yanzu mata mabiya addinin Hindu suna shiga halin kaka- ni-kayi, idan mazansu sun mutu, sun bar su, domin ana yi musu kallon “gawa”, wato sun mace a duniya, ba su da sauran jin dadin duniya. Mata da suka shiga cikin irin wannan yanayi ba su kwalliya, ba su ma ko cin abinci, mai kyau, ko mai dadi, sai wanda aka zabar musu. Ba a hulda da su balle a aure su. Sai dai dangin mijin maza su dinga yi musu fyade (shige), idan suka ki ba su hadin kai sai a kore su daga gidan. A halin yanzu mafi yawansu suna gudun hijira zuwa wuraren ibada irin nasu, inda a can kadai suke samu dan sauki. Haka kuma a wancan lokaci a kasar Hindu akan yi matar iyali wato idan da namiji goma ko kusa da haka a gida, sai su dauko mace daya a matsayin matarsu su duka. Irin wannan ko makamancin haka ya faru a kasar Girkawa, inda aka dauki mace tamkar dabba. Ana iya kama ta a yanka kamar yadda ake yanka dabba duk lokacin aka ga dama a matsayin horo. Misali idan mace ta kuskura ta haihu ba a lokacin da ya kamata ta haihu ba, ko ta rinka haihuwar ‘ya’ya mata zalla, to za a yanka ta. Idan kuwa ta rinka haihuwar ‘ya’ya maza kawai, to sai a rinka daukar ta ana kai wa baye ga shahararrun baraden kasar, kamar yadda ake kai dabba, wai don ta haihu ‘ya’ya su biyo baraden a sami zaruman da za su rinka yi wa kasa yaki. A kasar Sin kuwa mace ita ce kasa da kowa wajen daraja, ko wajen cin abinci ba a ba mata, sai an tabbatar maza sun koshi. Haka ma waje bada magani, amma kuma matan ne aka fi tura wa wajen neman abinci. A nahiyar Afrika ma haka lamarin ya kasance, domin a nan ma maza ke jan ragamar al’umma a cikin kowane irin lamari. Mace kuwa ba ta ma san kanta ba balle ta sami bakin fada a ji cikin al’umma. An dauki mata tamkar shanu, sai dai a debe su zuwa gona ko nemo itace. Saboda raunin da ake gani ga mata a kasar shi ya sa tun kafin su karbi kowane addini suna da al’adar aure, wanda suke yi domin mace ta sami galihu irin na maza wanda ake ganin idan ba shi, tana iya fadawa cikin garari. Sai dai wannan galihun da namiji ke ba mace yana da tsada. Domin kuwa duk ita take aikin wahala, kamar zuwa gona, nemo itace, dafa abinci, kula da yara da dabbobi da kuma ayyukan gayya. A kasar Hausa da alama ba ta canza zane ba, haka aka dauki mata, har wata karin magana Hausawa ke yi wanda suke cewa wai “namiji dutse, mace sakaina”, wannan maganar ta kara tabbatar da matsalar jinsi kamar yadda Babba (1986) ta bayyana. Kuma wannan ne ya kara dakushe armashin da ake ganin matan Hausawa na da shi, domin su ma kan su sun dauka cewa ba su iya yin komi sai yadda jinsin ya tanada. Irin wannan tunanin shi ya ne ya jawo koma bayan mata a cikin al’ummar Hausawa. Haka kuma wannan ne ya sa Hausawa suka fi kwadayin haihuwa ‘ya’ya maza bisa ga mata. Har ya kai ma aure na iya mutuwa idan mace ba ta haihuwar ‘ya’ya maza, wai babu magaji. Ko a addinin da suka yi tashe a duniya an sama irn wannan tunani. Addinin Kirista na daya daga cikin su. Domin kuwa a bisa tsarin addinin da kuma littafin da suke bi, cewa ya yi mace ita ce uwar zunubi, wadda ta yi dalilin fitar Annabi Adam daga aljanna. Haka kuwa wannan addinin (na Kirista) ya hana wa mace ‘yanci kai da zarar ta yi aure, ba a kiranta da sunanta ballantana na mahaifinta sai dai na miji. A wani taro na Kiristoci da aka taba yi a shekarar 1856 domin a gano mace ‘yar Adam ce ko dabba, bayan an tattauna sosai an yarda cewa mace ‘yar Adam ce, amma wadda aka halitta domin ta bauta wa namiji. Haka kuma an sake yin wani taro a zamanin Daular Romawa domin a gane ko mace na da ruhi kuma ana iya sanar da ita addini. Haka dai al’amarin mata ya kasance a mafi yawan al’ummomin duniya, kafin zuwan addinin Musulunci. Kuma addinin Musulunci shi ne ya kwato wa mace “yancinta kamar yadda za mu gani nan gaba. MATA A CIKIN ADDININ MUSULUNCI Addinin musulunci ya ‘yantar da mata daga kukumin da dan Adam ya sa musu tun shekaru aru-aru da suka gabata. Addinin ne ya ba mata dama da matsayin daidai da na maza a cikin mafi yawan al’amurra. Misali a cikin Alkur’ani mai tsarki, Allah (S.W.T) yana cewa: “Mun halicci mutane daga namiji da mace”. (Hujrat :13) A wata sura kuma ya ce: “Wanda ya yi kyakkyawan aiki namji ko mace alhali shi yana mumuni, to lalle za mu raya shi rayuwa mai tsarki, kuma za mu saka musu ladarsu da mafi kyau abin da suka kasance suna aikatawa” (Nahl : 97) Da kuma inda ya ce: “Domin Allah ya azabantar da munafukai maza, da munafikai mata, da mushirikai maza da mushirikai mata. Ya kuma karbi tubar muminai maza da muminai mata. Allah kuwa ya kasance mai gafara ne, mai jin kai”(Al-ahzab:73). Duk wadannan ayoyin suna nuna cewa ubangiji da kansa bai bambanta mace da namiji ba, domin duk inda ya ambaci maza sai ya ambaci mata. Haka kuma a wajen sakayya yana saka wa kowa da abin da ya aikata ba wani bambanci. Haka kuma Musulunci ya ba mace wasu hakkoki da aka danne a sakamakon al’adu da kuma zalunci irin wanda aka saba wa mata tun a zamanin jahiliyya. Misali a can da mace ba ta da iko a kan abin da ta mallaka sai dai mijinta. Haka kuma ba ta gado sai dai a gaje ta, ita kashin kanta da abin da ta mallaka, amma Allah (S.W.T) ya ce: “Maza suna da rabo daga abin da suka tsirfata (abin da suka nema domin amfanin kan su). Mata ma suna da rabo daga abin da suka tsirfata.”:32). Game da gado kuma ayar farko da Allah (S.W.T) ya fara saukarwa cewa ya yi: “Maza suna da rabo daga abin da iyaye biyu da makusanta dangi suka bari, kuma mata suna da rabo daga abin da ya karanta daga gare shi ko kuwa ya yi yawa, a rabo yankakke.”(4: 7). Wannan ayar ta nuna muna cewa mace tana da hakki gadon iyayenta da mijinta da ‘ya’yanta da kuma ‘yan uwan haihuwarta, idan ba su haihu ba. Bayan wannan kuma Musulunci ya ceto rayuwar mace, ya ba ta damar rayuwa cikin al’umma tamkar namiji, domin ya hana a bizne ta da rai. Inda Allah (S.W.T) ke cewa: “Kuma idan aka yi wa dayansu albishir da (‘ya) mace sai fuskarsa ta yi murtuk yana cike da tsananin bakin ciki. Ya buya daga (idon) mutane saboda mummunan abin da aka yi masa albishir da shi. Shin zai riki ne a wulakance ko kuma zai binne shi ne a cikin kasa, Na’am abin da suka hukunta kam ya munana.”(Nahl 58:59). Bagu da kari kuma addinin Musulunci ya ba mace damar neman ilmi kamar yadda ya ba namiji. Akwai hadisin Manzo (S.A.W) da ke cewa: “Neman ilmi wajibi ne a kan kowane musulmi da musulma. (Bukhari). Mace ita ce kashin bayan al’umma, idan ta gyaru to al’ummar ta gyaru, idan kuma ta lalace to al’ummar za ta lalace.”(Hadisi Nisa’i). Haka kuma, Annabi (S.A.W) ya ce, “Idan ka ilmantar da mace daya tamkar ka ilmantar da al’umma ne ga baki daya”. (Bukhari) A nan mun ga Musulunci ya karfafa ilmin mata fiye da na maza domin ganin cewa mace ita ke kula da tarbiyar yaro, idan ba ta samu ilmi ba, ba za ta iya tarbiyartar da ‘ya’yanta ba balle su girma su gina al’umma ta gari. MATA A WANNAN ZAMANI Da yake mun ga yadda ake kallon mata a wasu nahiyoyi tun a zamanin jahiliyya da sauran lokuttan da suka shige da kuma ceton da Musulunci ya yi wa mata. Sai kuma mu leka yadda ake kallon su cikin wannan zamani, musamman daga karni na sha-tara zuwa na ashirin da daya. Daga abin da wannan binciken ya samo dangane da matsalolin mata da yadda ake kallon su, a iya cewa har yau da sauran rina a kaba. Har yanzu al’adar nan ta daukar mata a matsayin ‘yan baya ga dangi tana nan sake cikin zukatan al`umma duk kuwa da juyin da Musulunci ya kawo da kuma canjin zamani. Domin ko a kasashen Turai masu ikirarin ci gaba da wayewar kai, inda kuma ake ta hayaniya kan ‘yancin mata har yanzu matsayin mace na mai rauni akan kowane sha’ani, yana nan. Mata suna fuskantar matsaloli da dama ta bangaren ilmi da siyasa da fasaha da aure da aikin gwamnati da sauran su, a ko’ina cikin duniya. Alal misali idan muka dauki bangaren ilmi wanda shi ne mabudin arziki na duniya da lahira, ta hanyarsa ne mutum ke fita duhun jahilci, ya san addini da sauran al’amurran rayuwar duniya. Da ilmi ne mutum ke iya samun babban matsayi a cikin aikin gwamnati. Haka kuma da ilmi mace za ta san kanta, har ta sami damar bada gudummawa a cikin al’umma. Amma a mafi yawan kasashe, musamman masu tasowa, mata ne a baya, wajen samun ilmi. Misali a wata kididdigar yawan jama’a da aka gabatar, an gano cewa a kasashe Sin da Bangaladash yawan mazan da ke da ilmi ya ribanya na mata sau uku. A Afirka kuwa matan da ke da ilmi kalilan ne, kuma mafi yawanci ilmin nasu ba mai zurfi ne ba33, Umar (1990). A wata kididdiga ta “UNESCO” a shekarar 2000 yawan matan da ke cikin jahilci sai kara hauhawa yake yi. Mangwat da Abama (1999) sun nuna cewa a shekarar 1958 yawan mata marasa ilmi ya kai kashi hamsin da takwas bisa dari, sai kuma kara hauhawa da ya yi ta yadda a shekarar 1985 inda yawan mata marasa ilmi ya kai miliyan 133. Har wa yau wata kididdiga ta “UNESCO” ta karshen karni na ashirin ta nuna cewa daga cikin yaran da suka shiga makaranta a Nijeriya, kashi talatin da uku ne mata, sauran duk maza ne. Saboda matan ko da sun shiga akan janye su daga baya, saboda wasu dalilai da masana da manazarta suka sha bayyanawa. A Arewacin Nijeriya ma tun kafin da bayan zuwan turawan mulkin mallaka an maida mata baya a fagen ilmi. Domin ko da Turawa suka ci Sakkwato da yaki suka kwace mulki da karfi sun sami mata masu ilmi da yawa wadanda suka gaji su Nana Asma’u da ‘yanuwanta da kuma takwarorinta, wadanda suka yi ilmin addinin musulunci, suka kuma yi rubuce-rubuce cikin harsunan Larabci, Fulfulde da kuma Hausa don fadakar da al’umma, ciki har da rubutatatun wakoki. Amma sai Turawa suka yi biris da sha’anin ilmin mata har sai bayan lokaci mai tsawo, a farkon karni na 20 da suka bude makarantar maza a Kano ba su bude ta mata irinta ba sai a shekarar 1933. Haka kuma Mulkin mallaka ya raunanar da makarantun allo da ya iske. Wannan ba karamin ci baya ya janyo wa Arewa ba domi mata su ne asasin gyaran al’umma da son ci gaba da samun ilmin addini kamar yadda aka dauko a karni na 19. Da an yi hakan da alam aka ba su ilmin zamani a lokacin da ya dace su same shi da Arewa ba ta tsinci kanta a sahun ‘yan baya ga dangi ba a fagen ilmi da ci gaban al’umma. Daga baya da aka sami makarantu don mata kuwa sai aka yi rashin sa’a da cewa mutane na dari-dari da ilmin boko, saboda addini da akidun wadanda suka kawo shi. Dangane da wanna ga abin da Babba (1986) ke cewa : iyaye na hana yaransu mata karatu, domin kada su rasa miji. Saboda al’umma, musamman ta Hausawa sun dauki cewa boko ke sa yarinya ta hinjire wa mijin, saboda za ta dauki kanta tana da wani matsayi cikin al’umma tun da tana da ilmi, alhali kuwa a zahiri ba haka abin yake ba. Domin mata da suka yi ilmi, su ne za a same su masu tsabta da sanin ya kamata. Ga sanin addini da kuma iya biyayya ga miji, ta hanyar kula da shi da ‘ya’yansa da kuma kayansa. Haka kuma Congleton (1988) a cikin wata hira da aka yi da shi, ya yi bayanin cewa, mutanen Arewacin Nijeria sun fi ba wa tarbiyar da yaro ke samu a gida muhimmanci a kan wadda za a ba shi a makaranta. Har suna ganin cewa ana gurbata wa yaransu, musamman mata tarbiya idan suka bar su suka yi zurfi a cikin makaranta. Wanda kuma a dalili haka maza ba su cika son su auri mata masu ilmi sosai ba. Babban dalili kuwa bai wuce na akidar nan ta cewa mace ta bi miji sau da kafa, ko da kuwa yin haka din zai jawo mata cikas a rayuwarta. Suna ganin cewa mace mai ilmi ta san hakkinta a kan miji da kuma san hakkin miji a kan ta, ba za ta yarda a tauye ta ba a cikin gida kamar dabba, ba kulawa ba wani abin yi. Azare (2000) cewa ya yi babban dalili da ke sa ana hana ko janye mata daga makaranta, shi ne rashin isasshen kudin da za a dauki dawainiyar karatun duka ‘yaya, maza da mata ga baki daya, kuma gudun lalacewar tarbiyarsu, wadda al’adar al’ummarsu ta tanadar musu. Amma kuma sai abin ya zan “an ki cin biri, an ci dila”, domin sai a hana su makaranta amma a tura su wajen kwadago ko tallace-tallace, inda suke shiga cikin hadurra kala-kala, kamar yin cikin shege ko kamuwa da cutar kanjamau . Idan muka dubi matsalar ta fuskar siyasa kuma za mu ga cewa a wannan fagen maza ne suka yi kaka-gida, domin a yawanci kasashen duniya ba a ba mata damar da ta kamance su a sha’anin siyasa ballantana a ce su kai ga taka rawar gani a cikin sha’anin mulki, Ashford (1995:17) ta yi bayanin cewa ana dai babatun dimokuradiyya ne a baki kawai, amma ayyanawar ba haka take ba. Da kyar ne mace take kai ga shiga takarar mukamin siyasa. Idan kuma ta samu shiga din, za ta fuskanci tarnakin al’ada, wanda ke iya hana al’umma ta zabe ta. Saboda idan aka dubi siyasar duniya a yau, mata irin su Margaret Thacher ta Ingila, da Indira Ghandi ta Indiya, da Komaratonga ta Sirilanka, da Benezir Bhuto a Pakistan da wasu kalilan kadai ne wadanda suka taba samun nasarar zama zababbun shugabanin kasashe, wanda yake idan aka kwatanta su da maza da suka taba shugabanci ba su kai ko kashi biyar bisa dari ba. Haka kuma a mafi yawan kasashe masu tasowa, musamman irin su Mexico da Brazil da yawancin na nahiyar Afrika, kujerin da ake ba mata a majilisar dokokin kasa ba su taka kara sun karya ba. Har ma a kasashen da suka ci gaba idan aka kwatanta maza da ke rike da mukamin siyasa da na mata, za a sami bambanci mai yawan gaske. A Arewanci Najeriya abin ma ya fi muni, domin al’umma sun dauki cewa mata karuwai kawai ke yin siyasa. A lokacin da muka dubi matsalar shugabanci sai a ga cewa a cikin matan da suka yi ilmi, kalilan ne ke samun yin aikin gwamnati. Wadanda kuma suka sami aikin, sukan fuskanci matsaloli ta fuskoki da yawa. A kasashen duniya da yawa, har da wadanda suka ci gaba, a kan nuna wa mata bambanci ta fuskar matsayi ko makami da awoyin aiki. Haka kuma akan nuna musu bambanci wajen biyan ladar aiki. A kasar Amurka ga misali, Riley (1997) ta yi bayanin akan tauye ‘yancin mata ta fuskar mayar da su saniyar ware a fagen siyasa. Ta kai ga har shata wani tsari aka yi wanda yake tabbatar da cewa matan da suke aikin gwamnati ko na manyan kamfuna ba su rika manyan mukamai ba, wanda ya sa bambanci tsakanin mata da maza ya dade kafin a kawar da shi a kasar. Ta kara da cewa ta kai ma ga albashin namiji ya fi na mace yawa ko da kuwa aikinsu iri daya ne. Wannan bambancin kuma ya kasance har a kasashen Ingila da Kanada da kuma Siriya. Wannan akidar ba a can kadai ta tsaya ba, ko a nahiyar Afrika da kasar Nijeriya, har ma Arewa, mata sun kasance a matsayin saniyar ware a fagen siyasa, domin matan Arewa ba su fara ko jefa kuri`a ba sai 1976, ballantana su shiga takara a zabe su, Dityavyar(1998;145). Matan da ke aiki ma ana yi musu kallon wasu tsiraru ne, wadanda suka fi karfin mazajensu a cikin al’umma. A wajen aikin kuwa akwai mukaman da ake ganin cewa mata ba su isa su rika su ba sai dai maza. A fagen tattalin arziki mata na bakin kokarinsu, domin kamar yadda Osunde and Imorayi (1999) suka bayyana, mata na yin ayyuka da dama wadanda ke taimaka wa wajen habaka arzikin al’umma. Inda suka bada misalin cewa, mata na noma, kiwo da kuma sana’oin hannu irin su saka, har ma da fatauci, suna kuma yin ayyukan gayya. Ita ma Riley (1997) ta yi bayani cewa A kasar Sin ‘ya’ya mata ne ake turawa gona ko wajen ga aiki, domin su nemo wa iyaye da sauran ‘yan uwansa da suka hada da maza abin masarufi. Haka kuma sanannen abu ne cewa a kasar Indiya mace ke neman kudin biyan sadakin aurenta. A nahiyar Afrika, har a arewacin Nijeriya mata na kokarin neman na kai. Inda suke yin duk abubuwan da aka ambata a sama, har ma da kari, domin sukan yi `yan sana`oin hannu, suna dora wa ‘yayansu tallace-tallace, su kuma suna can suna yin wasu sana’a wadanda suka hada har da kitso, dinki, da sayar da abinci a wurare daban-daban. Mack (1992) ta yi bayanin har da cinikin bayi matan kasar Hausa suna yi a zamani da ake yin sa. Amma abin mamaki shi ne duk da wannan gagarumar gudumawar da mata ke bayarwa ta fannin tattalin arziki, al’umma na ci gaba da yi musu kallon cima-kwance wadanda komi sai an nemo an ba su. A yanayin zamantakewa na yau da kullum, mata su ne kashin bayan zaman lafiya da mu’amala mai kyau cikin al’umma. Domin su ne aka fi sani da kokarin sada zumunta da hulda da makwabta da tarbiyar yara da kuma yin ‘yan sana’o’in hannu, masu taimakawa wajen gudanar da rayuwa cikin sauki. Haka kuma tarihi ya nuna mata suna da tausayi da kokari wajen kula da marasa lafiya, musamman a zamanin da ake yawan yake-yake. Ko a nan kusa lokacin jihadin su Shehu Usman Danfodiyo, Boyd (1989) ta yi bayani akan irin gudumawar da su Nana Asma’u da sauran matan zamaninta suka bayar, ta hanyar kula da wadanda aka ji wa rauni da kuma bada abinci da daukar kaya da kula da yara lokacin yaki. A wannan zamani da ake ciki mata na gudanar da kusan duk abin da maza ke yi a kowane bangare na rayuwa idan dai an ba su dama. A harkar aure mata suna samun matsaloli a ko ina ciki duniya. Sai dai bayanin da zan yi a nan shi ne a kan matan arewacin Najeriya, inda har yanzu a kan yi wa yarinya aure ba tare da an nemi yardar ta ba, kuma a nemi ta zauna da mijin nan bisa ga ladabi da biyayya ko da kuwa ba ta son sa. A wani bayani na Callway and Greevey (1994:84) cewa suka yi: “A kasar Hausa ana yi wa yarinya auren wuri, kuma zaba mata mijin ake yi (ba tare da yardarta ba) kuma dole ta zauna da shi, ta bi shi sau da kafa, ta kuma zauna tare da kishiyoyi, ko tana so, ko ba ta so”. Wannan auren da ake yi musu, na wuri yakan jawo musu matsaloli iri-iri, musamman idan suka yi saurin daukar ciki idan an zo wurin haihuwa, mafi yawa yaran da ba su yi kwarin haihuwa ba, sukan sami matsalar yoyon fitsari. Inda kuma daga karshen mazan ke juya musu baya, sai dai iyayensu su yi ta wahala da su. Wannan kuma ba a kasar Hausa kawai yake faruwa ba, yana faruwa a yawanci kasashe masu tasowa. Misali a kasar Somaliya, musamman sai da wata baturiya ta kafa asibitin taimakon irin wadannan mata da ke samun matsalar yankan gishiri, kuma al’umma ta juya musu baya48. MATA DA ADABIN BAKA Shahararrun masana da yawa wadanda suka yi rubuce-rubuce a tarihi da al’adun kasar Hausa, kamar Clapperton da Lander (1829), da Jeroma (1970,1972,1973), da Joseph (1973), da Palmer (1978) da Mark (1985) da Boyd (1989) da Hill (1972), da sauransu, duk sun yi bayanin cewa kafin zuwan baki a kasar Hausa, matan Hausawa sun kasance masu taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da kasar da al’ummarsu gaba. Irin wannan rawa tasu ta shafi bangaren tattalin arziki da siyasa, tarbiya da fasaha da kuma ciyar da harshen Hausa gaba, ta hanyar tatsuniyoyi da labarai da kacici-kacici da karin magana da salon magana da badda-bami da sauran su. Wadannan suna cikin abubuwan da Fafunwa (1982) ya kira makarantun farko na ‘yan Afirika kafin su sami ilmin karatu da rubutu. Amma kuma idan aka tashi bayani game da irin wannan ci gaba sai ya zan gudummuwar maza kadai ke fice. Haka dai al’amarin mata ya kasance rayuwarsu na cikin tawaya da rashin walwala wanda ba kome ya hassada masu shi ba sai al’adu, wadanda ke ci da yawun addinai da siyasa domin biyan bukatun wani jinsin da ba mace ba. Wadanna al’adun sun yi tasiri sosai cikin al’ummomi musamman a nahiyar Afirika yadda har su ma matan an dasa wannan akida ta namiji dutse, mace sakaina, har ya zan ba su iya kalubalantar matsalolin da ke tattare da su, Remi(2003). Sai a ‘yan shekarun baya –bayan nan da aka sami mata kalilian masu matsawa, suka tunkari wannan matsalar ta danniyar jinsin mata, ta hanyoyi daban –daban. MATA DA RUBUTACCEN ADABIN HAUSA Daga abin da muka ga a sama mun fahimci abubuwa da dama. Da farko dai matsalar nazari da sharhi game da mata ba ta wuce irin mizanin da aka dora batun ba, ko a adinance ko siyasance ko kuma tafuskar ilmi da zamantakewa. Na biyu kuwa shi ne duk da cewa an yarda mata na taka rawa a gnuwar rayuwa ta kowace irin fuska, da alama akwai wadansu katangai da ake jefawa a gabansu domin kada su kai ga gaci.Na uku ga alama, yadda ake kallon mata a kowane fage da irin rawar da suke takawa da matsalolin da suke fuskanta su ne suka yi katutu ko da a fagen nazarin ayyukan adabin Hausawa. An fadi haka ne ganin cewa mata kamar takwarorinsu maza su ma sun samu ilmin karatu da rubutu bayan zuwan addinin Musulunci. Amma duk da cewa Musulunci ya wajabta neman ilmi, musamman na addini a kan kowane musulmi, namiji ko mace, tarihi ya nuna cewa a kasar Hausa al’umma ta yi watsi da sha’anin ilmin mata, wanda shi ne ya haifar da barin mata cikin jahilci. Wannan ya sa mata suka kasance tamkar dabbobi cikin duhun jahilci. Abin da al’umma ta tanadar musu shi ne aikin zaman gida. Da yake kuma rubutaccen adabi ba ya samuwa sai da karatu da rubutu, dole rawar mata a wannan fage ta takaita. Rawa ba ta canza ba sosai, sai lokacin jihadin su Shehu Danfodiyo da magoya bayansa, a karni na 19, Inda Shehu ya lura da wannan matsalar ya kuma tashi tsaye domin kawar da ita. Ga abin da Shehu ke cewa game da matan kasar Hausa a wancan lokaci: Maza sun dauki matansu tamkar wasu rubabbun kayan gida, wadanda aka gama amfani da su, sai yar a shara. Kash wannan hali ya saba wa ka’ida. Yaya za su bar su cikin duhun kai, bayan ga shi kuwa suna ba dalibansu sani a waje.” Shehu ya ci gaba da cewa fadar nan ta Hausawa mai cewa “aljannar mace tana karkashin kafafun mijinta”, ba ta da wani tasiri sai idan mace ta bauta wa Allah yadda ya kamata. Bauta wa Allah ba ta inganta sai da ilmin addinin Musulunci. Wannan ne ya malamai da magidanta da ‘yan uwan Shehu da kuma `ya`yansu duk sun karbi kiran da ya yi. Nan da nan sai makarantu suka budu a gidajen mutanen da sassa a can cikin gidaje wurin mata. Mafi yawan matan malamai suka zama malamai su kansu. Alal misali matan Shehu da ‘yanyansa da sarakunansa, kamar su Hadiza, Asma’u, ‘yayan Shehu da A’ishatu matar Aliyu Jedo, da Maryam da Fatima, matan Sarkin Musulmi Bello da Maryam ‘Yar Shehu duk sun bude azuzuwan karatun allo a cikin gidajen mazansu. Idan an manta da rawar da wadannan suka taka to da kyar ne za mu manta da rawar da Nana Asma’u ta taka. Dubi Boyd (1989), wadda ta kawo bayanin `yan taru, wadanda suka samo asali daga shirin ba mata ilmi na Nana Asma’u. Haka kuma duk wadannan mata sun yi rubuce-rubuce da suka hada har da wakoki. A kan abubuwan da suka shafi rayuwar al’umma dangane da addinin musulunci, Boyd (1989) ta yi bayanin cewa Nana Asma’u kadai ta rubuta wakoki da dama, amma kuma duk wadannan ayyukan da mata suka yi, saboda su mata ne, sai wannan ya kasance musu tarnaki wajen yin fice da kuma samun shiga cikin mashahuran marubuta. Ko Nana Asma’u idan ba domin bincike-binciken Boyd da wasu ba da har yanzu mutane da dama ba san irin gudumawar da ta bayar ba. Domin ita Boyd ce ta yi kokarin binciko wadannan ayyukan ta kuma buga cikin littattafai da mujallu daban-daban. Amma kuma har yanzu mutane kalilan ne a cikin wannan al`umma suka san ayyukanta. Wannan dabi’ar ta rashin ba aiki mata muhimmaci ba wai a ciki al’ummar Hausawa kadai take ba, har ma da sauran al’ummomin duniya. Misali kasar Ingila, tun a shekarar 1866 wata marubuciya mai suna Anne Evans ta yi rubutu a kan matsalar mata, ta ce ‘mace ba ta da zabi… sai dai ta dogara ga duk abin da ta samu ko ya same ta. Ta kuma tsaya iya dan matsayinta”. Babban abin takaici a nan shi ne ita wannan mata sai da ta lika wa kanta sunan namiji wato “George Elliant’ kafin rubutunta ya sami karbuwa ga al’umma. Haka kuma idan muka koma ga tarihi, za mu ga cewa daga cikin shahararrun marubuta da suka yi suna a duniya, wadanda aka yi ta nazarce-nazarce a kan ayyukansu, da kyar ne idan za a sami mace. Misali mun ga an yayata su Plato da Aristottle da Shakesphere da Milton da Chaucer da Samuel Johnson da T.S. Elliot da sauran su. Amma ba a damu da shahararrun marubuta mata ba irin su Austen da Broute, Woolf da Hurston da sauran su a duniyar Turai da Amurka, ba domin komi ba sai don suna mata. Idan har hakan ya kasance dangane da su Nana Asma’u da dangoginta a zamanin masu jihadi, ba abin mamaki ba ne idan ba a ba mabiyansu wani muhimmanci ba, duk kuwa da cewa an samar da mata mashahurai da suka tashe a wannan fage. Faga cikin irin wadannann an ci gaba da samun mata da suka ci gaba da yin rubuce-rubuce cikin Hausa da sauran harsunan Arewacin Nijeriya,musamman a fannin rubutattun wakoki domin su ne suka fi saukin hardacewa ga matan da ke daukar karatu da kuma dadin saurare ga sauran jama’a. Amma saboda matsalar wariyar jinsi da tarnakin al’adu wanda ya tauye mata ga samun shawarwari daga kwararru game da rubuce-rubucen da kuma gudun korafe-korafe a cikin al’umma, sai aka kara samun dakushe aikace-aikacen mata na rubutaccen adabin Hausa. Idan kuma aka dubi bangaren maza ba haka abin yake ba. A halin yanzu ambaton Akilu Aliyu da Aliyu Namangi ko Abubakar Imam ko Yusufu Kantu ko Alkali Haliru Wurno ko Bello Kagara da dimbin mazan da suka yi rubuce-rubucen cikin adabin Hausa a shekarun baya, sai ka taras an san su. To amma matan fa? Kodayake akwai su ba a ba su damar fitowa su yayata kansu ba, ba a kuma taimaka aka yayata su ba. Ko ‘yan wadanda suka yi fice, ba da yawun bakin maza suka yi shi ba. Domin mata ne ‘yan uwansu, suka yi kokarin da suka fito da su. Wato mata irin su Baturiya Beverly Mark da ta yi kokarin buga littafin “Alkalami a Hannun Mata” (1983),wanda yake dauke da rubutattun wakoki na wasu mata a Kano, wato Hajiya Hauwa Gwaram da Hajiya ‘Yar Shehu. Sai kuma Gambo U. Babba, wadda ta rubuta kundin digirin farko a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, a kan wata malama marubuciya a1986, wato Hajiya Hasana Sufi, sauran matan da aka ji sunansu kuwa, su ne suka yi kokarin rubuta labaransu, suka kuma buga abin su da kan su. Wato irin Hafsat Abdulwaheed (1980) da Yaya Hasana Umar (1980) da kuma marubutan zamani, wato irin su Bilkisu Funtuwa da Balaraba Ramat da Zuwaira Isah da sauran su. Inda kila za a ga wannan aiki ya kankama shi ne littafin Ibrahim Yaro Yahaya (1988),wato Hausa a Rubuce, shi ma rubuce-rubucen maza ya fi yawa, kila saboda rubuce-rubucen mazan ne ya fi yawa, ga abin da yake cewa game da wannan batu: Mata su ma ba a bar su a baya ba wajen ciyar da ilmi gaba ta yin rubuce-rubuce da ajami ko boko, a buga a littattafai. Harsashin da nana Asma’u ‘yar Shehu da Maryama ‘yar Shehu suka aza a kan ilmin mata ya samu kafuwa sosai, har ma ana ta dora gini a kansa tun daga wancan karni har zuwa wannan zamani namu, domin ana samun mata a ko’ina a kasar Hausa suna neman ilmi a makarantun allo da na Islamiyya da ilmin zamani ma. Wasu daga cikinsu in an yi musu aure, suna gudanar da azuzuwan koyarwa a gidajen mazajensu. Akwai mata da dama irin wadanda Yahaya (1988) ya ambata, wadanda suka nemi ilmi har suka zama malamai, kuma marubuta cikin ajami da boko. Haka kuma rubuce-rubucen nasu sun tabo fannoni da dama, sai dai saboda kasancewar mafi yawansa matan aure ne ko kuma ‘yan matan da ke karkashin kulawar iyayensu ba su da damar zuwa wasu wurare don nuna fasaharsu, kamar yadda maza ke samun yi, ya sa ba a san da zaman mafi yawansu ba, wannan matsalar ta fi shafuwar marubuta wakoki, kila shi ya sa mazan suka fi tashe fiye da matan. Lallai akwai marubuta mata kamar yadda aka sha fada, amma ga nawa tunanin ba wai fadar cewa akwai matan ne kawai da ke rubuce-rubucen ajami ke da muhimmanci ba, a’a, a ga ayyukan nasu a zahiri. Wannan shi ne kashin bayan wannan tunani, a nemo matan marubuta wakoki da kagaggun labarai da kuma wasan kwaikwayo, domin kafa hujja ta fasalce-fasalcen ayyukan adabi na mata a kasar Hausa. Ta haka ne za a ga irin rawar da suka ko suke ko za su bayarwa a raya kasa da al’umma.

No comments:

Post a Comment