Wednesday, 3 July 2013

Me Ya Sa Muke Yin Rubutu?

DON ME MUKE YlN RUBUTU? Kwalwa ita ce kandamin da ke ajiye da duk wani tunani na dan Adam. Daga cikinta ne ake tsara da shirya da kuma luguden dukkan abin da ake so ya kasance na rayuwar yau da kullum. Idan har an kammala dafuwar ne sai harshe ya shigo domin idar da sako.Kamar yadda aka sani, harshe shi ne injin din da ke sarrafar da kuma aiwatar da duk tunani da kwalya ta shirya ko ta tsara a cikin kowace irin al’umma. Da harshe ne ake fiddo yawancin al’adu da adabi da ma duk wani ilmi na rayuwar dan Adam, ta fuskar bayyanawa ta baki ko kuma a rubuce. Wannan dama ce ta sa ake ba harshe muhammanci, ta yadda wadanda ba su da shi sukan kasance nakasassu, wadanda kuma suke amfani da wani abu makamancin sa, ake musu kallon wadanda ba su cika ba a cikin al’umma. A nan ina magana ne kan bebaye ko kuma masu kama da su da kuma masu amfani da hito a matsayin hanyar sadarwa a tsakanin mutane, misali al’ummar Mazatec da ke kasar Mexico, haka wannan yanayi yake ko a cikin rubutaccen harshe. Duk wadanda ke da hanyar rubuta harshensu, ana yi musu kallon wadanda suka ci gaba, suka fi sauran al’ummomi na duniya wayewar kai da sanin abin da duniya take ciki. Wannan shi ne fasali na farko da aka fara amfani da shi wajen gane bambancin da ke tsakanin Turawa da bakaken fatar Afirka, dab da za a yi mana mulkin mallaka. Rubutu, ko kuma in ce harshe a takarda shi ne ya sanya wa Turawa ji da kai da kuma tokabo, har suke ganin cewa ba wata hujja da bakaken fatar Afirka za su kyamace su dangane da zuwan su nahiyar a madadin ‘yan jari hujjar wancan lokaci. Ba sai an fada ba, harshe a magance da kuma rubuce ya kara sanya wani wagegen gibi tsakanin Turawa da mutanen Afirka, domin kuwa ko da suka yi amfani da alburusai da bindigogi wajen cin wannan nahiya ta Afirka, daga cikin rubutaccen harshe aka samo wannan tunanin. Saboda haka ko da masana irin su Jahn (1963) ke bayanin cewa, ai ko da Turawa suka zo Afirka sun iske mu da wayewar kanmu da tunaninmu da kuma ci gaban zamani irin namu, shi kuma Rodney (1973) ya kara jaddawa ta hanyar cewa ai zuwan Turawan ma ya dakushe ne a maimakon ya taimaka wajen ciyar da nahiyar Afirka gaba, kuma ko kafin zuwan Turawa akwai wasu al’ummomi da suke da harshensu a rubuce, akwai kuma wadanda ke da hanyar sadarwa ta gargajiya; irin ‘yan ma’abba da kuma kida da ganguna ko makamantan haka wajen sadarwa; wannan bai nuna mana irin yadda tunanin jama’ar nahiyar Afirka ya kasance ba a zahiri. Domin kuwa mulkin mallaka abin da ya mayar da hankali shi ne sanya mutumin Afirka ya dinga tunani da rubutu a cikin harshen da ba nasa ba, a cikin harshen da zai sanya Bature ya dinga ci gaba da mulkin Afirkawa ko da kuwa bayan ya nade tabarmarsa ya bar nahiyar a tsawon shekaru. Wannan shi ne a halin yanzu ke faruwa a yawancin kasashen da ake yi wa lakabi da masu tasowa ko kuma wadanda ba su ci gaba ba, ba wai a nahiyar Afirka kadai ba, har da sassan duniya da makircin mulkin danniya da mallaka ya shiga cikinsu ya yi kaka-gida. Shi ya sa yau kasar Ingila da masu magana da rubutu da harshen Ingilishi a matsayin harshen uwa ba su wuce ka kwana ka kirge su ba, amma kuma masu magana da Ingilishi a duniya sun fi kowa yawa a doron kasa, shi ya sa ma ake wa harshen lakabi da harshen duniya, ko kuma harshen danniya! An fadi haka ne saboda sanin irin yadda tunani da Ingilishi da rubutu da Ingilishi yake nakasa kowace al’umma da ta ba wannan abu muhimmanci fiye da harshen uwa ko harshen gida. Ba yadda za a yi al’umma ta ginu ta kuma ci gaba ba tare da kare harshenta da kuma rubuce-rubucenta ba; duk irin yadda mutum zai yi ya ciyar da kasarsa gaba ta hanyar amfani da ilmi da ke cikin littafin da ba a harshensa yake ba, zai kasance cikin matsala da kuma kunci, domin zai zamanto mai yaki da tunani iri biyu, na baki da kuma nasa na gida, wannan na daga cikin abubuwan da suka cunkushe harkar ilminmu da kuma halin da ilmin yake ciki da kuma rubuce-rubucenmu a yau. Wannan abu da muke fama da shi yau, shi ne kuma Turawa suka yi fama da shi tsakaninsu da Larabci, a lokacin da Larabcin yake cikin ganiyarsa. Kusan duk wani ilmi na kimiyya ko fasaha ko kuma na ci gaban al’umma a Larabce yake kafin Turawa su gaje, su kuma mallake shi daga baya. A lura, ba don Turawa na so ba ne suka debi ilmin Larabcin suka yi amfani da shi, dole, kanwar na ki ce ta sa Turawa suka yi amfani da tunani da nakaltar Larabci don cin moriyar ilmin da ke kimshe a cikin littattafan Larabawa da ke mulkin duniya a wancan lokaci. Daga baya ne Turawa suka fahimci cewa ai yawancin ilmin da Larabawa ke takama da shi su ma sun kwaso wasu ne daga littattafan Girkawa, don haka suka yi watsi da na Larabawa suka koma wa na ainihin, wato Girkanci, ta haka ne mallakar da Larabawa suka yi wa duniya ta fuskar ilmi ta subuce ta koma ga Turawa, musamman na Ingila. Wannan ba wani abu ya nuna mana ba sai cewa gadon gida halal ne ga raggo. Ba ta yadda za a kai ga kololuwar ilmi da ci gaba ta amfani da bakon harshe, domin kuwa komai iya nakaltar harshen wasu da ka yi, ba za ka taba zama kamar su ba, kuma za ka kasance ne a kullum kana magana da bakin ne, ba mutanen cikin gida ba ko kuma ‘yan uwanka, domin kuwa kashi 7 cikin 10 na mutanenmu ba su san da wannan bakon harshen ba, idan kuwa haka ne, to mu da wa muke magana a rubuce-rubucenmu idan mun kimshe al’amarunn cikin harshen Ingilishi ko kuma mun jona tunanin bakuwar al’ada da adabi da addini a cikin rubuce-rubucenmu? Tambayar farko da zan soma da ita, ita ce, shin marubutan baya, wato kafin mu, haka suka yi? Yaya tasirin amfani da bakon harshe da al’ada da adabi wajen gina tunani da rayuwarmu zai kasance ga masu gudanar da wannan harka, musamman ga ci gaban al’ummarmu da kuma kasarmu? A tuna, su kan su Turawan mulkin mallaka sun san irin tazarar da Larabci ya yi wa sauran harsunan duniya ne, shi ya sa suka yi amfani da dabashiri kafin su durkusar da shi, su maye gurbinsa da nasu, shi ya sa duk inda suka sami kan su a matsayin masu mulkin mallaka, a Afirka ko Asiya ko Amurka ba su yi wasa da cusa tunaninsu da kuma akidojinsu ga al’ummomin da suka ci karo da su ba. Sun yi haka ne da sani, domin ta haka ne kurum za su iya yin zaman darshen a cikin harkokin kasashen da suke yi wa sukuwar salla a wancan lokaci. Shi ya sa tsarin ilmin nasu da littattafan da suka shigo da su domin horaswa, suka kasance cikin harshen ‘yan mallakar, a wasu wurare suka matsa sai a yi komi tamkar a Turai, a wasu wuraren kuwa a kaikaice, wasu kuma ba ka iya bambanta su da masu mulkarsu ta kowace irin fuska, dubi Amurkawa ka kwatanta su da mutanen Indiya ko Pakistan da kuma bakaken fatar Afirka, musamman a tsakanin inda Faransa ta yi turke da kuma inda Birtaniya ta kafa tata lemar. Ma’ana, wannan rarrabuwar ita ce ta taimaka wajen gane illar mulkin mallaka da kuma yadda aka rarraba kawuna domin a ji dadin mulki. Bisa wannan tafarki ne Leopord Senghor na Senegal ke nuna bakin cikinsa game da irin ilmin da ya samu ta hanyar Turawan Faransa, yana cewa, ‘a lokacin da nake fafutukar karatu a gida da waje, ‘yan uwana da na bari a gida ba su yi boko ba, sun kasance ‘yan kasa na gari, ni kuwa a kullum da na bar makarantar Firamare na shiga Sakandare, na wuce zuwa Jami’a, sai kara hannun riga na dinga yi da al’ummata da kuma kasata.’ Ya ci gaba cewa ‘a daidai lokacin da nake karatu, sai na kara sanin tarihi da yanayin kasashen Turai, ina kuma kara jahilcewa game da tarihin al’ummata da kuma kasata.’ Daga karshe ya ce ‘a lokacin da na dawo gida daga Faransa, sai na ga na kasance bako cikin jama’ata, tsararrakina da na bari ba su yi karatu ba, suka kasance malamaina.’ Wannan haka ya kasance dangane da yawancin marubuta da shugabanni a nahiyar Afirka, musamman wadanda suka kasance karkashin mulkin kasar Faransa. A bangare daya kuwa, wadanda suka zauna cikin inuwar mulkin Birtaniya ba haka abin ya kasance ba, ga wasu, kamar yadda Mista East ya bayyana game da Abubakar Imam a matsayinsa na marubuci, ya ce, ’Abubakar (Imam) ‘yana daya daga cikin ‘yan kalilan da ya kasance duk da cewa ya sami ilminsa ta hanyar horaswa cikin Ingilshi da littattafan Ingilishi, daga kuma Turawan Ingilishi, bai yi watsi da harshensa ba, domin kuwa yana bayyanar da tunaninsa cikin harshen nasa, ba cikin Ingilishi ba kamar yadda saura ke yi.’ Tambaya. Me ya bambanta Senghor da Imam? Ba wani abu da ya wuce cewa shi Imam bai yarda Ingilishi ya kasance masa harshen tunani ba, bai yarda bakin al’adu sun yi masa katutu, ba ma Ingilishi kadai ba, kusan duk wani bakon abu da ya ci karo da shi a lokacin da yake nadar ilmi da ya gina masa rayuwa bai cika amsar sa kai tsaye, sai ya yi bita da nakaltar irin tasirin da zai yi masa. Shi kuwa Senghor ya tashi ne cikin wani tsari da ya fifita tunani da al’adun Faranshi bisa na bakar fata, haka al’adu da addini da kuma tsarin ilmin baki daya. Bai sami damar bambance barcin makaho ba ko kuma duma daga kabewa, ba don komi ba kuwa saboda irin yadda aka rene su tun daga gida. Imam ya sami ilmin addini mai zurfi ko kafin ya hadu da Bature da makircin da ya shigo da shi, saboda haka bai yarda wani makiri ya yi masa wayon wanikiki ba, tun yana karami. Ko da ya shiga dakin ajiyar littatafai na makarantar Elemantare da Midil a Katsina domin ya yi nazari don shiga gasar rubuta littatafai da aka shirya a 1929 da kuma 1933, bai yarda ya yi amfani da duk abin da ya ci karo da shi ba, sai dai ya karanta, ya jinjina kamar mai sayen kaza, amma yana bukatar mai kwai. Haka kuma sai ya auna abin da abin da addininsa da kuma tadojinsa na kwarai suka aminta da su, sa’annan ya kattaba shi a cikin nasa aikin. Saboda haka muna iya cewa bai taba yarda da tasirin bakin al’adu ko addinai da ya yi nutso a cikin su, sun ja masa akala wajen yin rubutunsa ba. Haka su Tafawa Balewa da Ahmadu Bello da Aminu Kano da Sa’adu Zungur da Mu’azu Hadeja da Mudi Sipikin da Alkali Bello Gidadawa da Gambo Hawaja da Shekara Sa’ad da wasu da dama daga cikin marubutanmu na da suka yi, kuma wannan shi ya haifar da akidar nan ta goya wa talaka baya da nema masa mafita daga al’amurran da suka kasance suna sa masa kunci da dabaibaye shi ta fuskar siyasa da mulki da tattalin arziki da sauran al’amurran zamantakewa na yau da kullum. Bari mu yi bitar wasu daga cikin ayyukan daya daga cikin mashahuran marubutan kasar Hausa wato Abubakar Imam, domin mu gani ko za mu iya samun haske dangane da irin abubuwan da aka yi a da, da yadda suka yi tasiri har zuwa yau, kafin mu koma ga ainihin batun namu na yau, shin mu wa muke yi wa rubutu, don me muke yin rubutu, me kuma muke so rubutunmu ya yi a rayuwar da muke ciki! A cikin ayyukan da Abubakar ya yi na adabi ba daya da ya zauna ya shirya a cikin ransa da nufin ya nishadantar kurum ko kuma ya burge kawai ko kuma dai don a san da shi a cikin harkar rubutu ko kuma rayar da ilmi. Bai yi haka a lokacin rubuta littafin Ruwan Bagaja ba, duk da cewa a lokacin da ya yi rubutun yana da shekara 22 a doron kasa. Ko da ya shiga dakin ajiyar littattafai na makarantarsu domin ya sami samfur na irin yadda zai tsara labarin nasa, ya kuma ci karo da littafin The Water Of Cure na ‘yan uwa Grimms daga Jamus, ba haka nan ya bi shi ya kwashe komi da komi ba da ya ci karo da shi a cikin littafin, kamar yadda labaran suke a kasar Jamus, tun asalinsa ba, sai da ya bi ya nakalci labaran, ya yi musu kwaskwarima ya debe al’adun Jamusawu da suka yi hannun riga da na kasar Hausa, sa’annan ya maye gurbin wadanda ya karanto da na Hausawa. Saboda haka za a ga ya cire addinin Kiristanci, ya shigo da Musulunci, al’adun Jamusawa suka bada wuri domin na Hausawa. Da kuma ya shiga cikin littafin Alfu Lailah yai nutso da ninkaya ya debo hikayar Abdussamad da ‘yan uwansa, ita kuma ya kwashi wani gefe ne da ya dace da tunanin malam Bahaushe ya jefa a cikin littafin Ruwan Bagaja, ya yi watsi da tadar Larabawa da ya san cewa ba ta da wani alfanu ga mai karanta Hausa. Ba nan kadai ya tsaya ba, ya kuma shiga cikin gonar adabin baka na Hausa inda ya tsamo tatsuniyoyi da labaran Hausawa da suka yi tashe a wancan lokaci ya gina zubin littafin. Da kuma ya natsu sai ya nemo rayuwar Malam Zurke da Alhaji Imam daga rayuwa ta yau da kullum. Shi dai Zurke wani mahaukaci ne da aka yi a cikin birnin Katsina a lokacin da Imam ke karatu a can, Alhaji Imam kuwa ba kowa ba ne marubucin ne da kansa. Sunansa Imam, mahaifinsa sunansa Shehu, shi ya sa Himma dan Shehu ya zama lakabinsa. Sai dai ya dace a lura ko da ya je ga rayuwar yau da kullum domin neman gina malam Zurke da Alhaji Imam, amma kuma siffofin wadannan mutane a zahiri ya same su ne daga littafin Maqamatul Hariri, inda Harisu da Abu Zaid suka taka rawa irin ta Zurke da Alhaji Imam, sai dai su Harisu dabaru da wayon wanikiki da suka yi a cikin Maqama cike suke da al’adun Larabawa, dole ta sa Imam ya mayar da su na Hausawa, cikin ban dariya da sosa rai. Idan kuma muka dubi Magana Jan Ce (1-3) sai mu ga cewa nan Imam ya nuna gwanancewa fiye da a Ruwan Bagaja, ko ba komi a nan ya san da wa yake magana, ya kuma san dalilin yin rubutun da abin da yake son rubutun nasa ya yi ga wadanda aka yi wa rubutun. Tun da farko, nan ba gasa ba ce, an nemi a yi rubutu ne don yara ‘yan firamare, domin a samar musu abin karatu da kuma tarbiyya. Nan ma Imam sai da ya nemi samfur da zai gina nasa tunanin, amma kamar kullum sai da ya canza wa duk wani tubali da ya tsinto daga wasu wurare siffa ko kuma kama, don su dace da tada ko al’adun yara ‘yan kasar Hausa. Ya dai dubi tsarin Alfu Lailah, ya gina budewar Magana Jari Ce, ya kuma yi amfani da littafin The Parrot ya gina batun Aku mai magana, ya nemo labaran Andersen Fairy Tales na kasar Denmark da labaran Aesop Fables na Girkawa da labaran Grimms Fairy Tales na Jamusawa da labaran Shakespeare na Ingila da tatsuniyoyin Hausa masu tarin yawa domin su kasance masa ‘ya’yan da ke tafiya da uwar labarin Magana Jari Ce. Ya yi haka ne cikin tunanin masu karatunsa da neman shirya musu mafita da samar da tasiri na gari. Saboda haka duk inda ya hadu da maganar barayi sai ya yi huduba kan sata da rashin kyan sata, yana kuma bayyana cewa bai son bayar da labarin barayi ba don komi ba sai don gudun kada yara su sami abin kwaikwaya. Shi ya sa kuma duk inda ya kawo labarin barayi to bai barin barayi su yi nasara kan mutanen kwarai. Kai ba wannan kadai ba, duk inda aka yi mugun abu sai ya nuna horon da aka yi wa wanda ko wadanda suka yi mugun abun domin ya kasance darasi. Imam ya san darajar rubutu, ya kuma san illar rubutu, shi ya sa tun farkon shiga cikin wannan harka kamar yadda ya fada a cikin tarihinsa, ya shiga da zuciya daya. Ga abin da yake cewa a cikin littafin tarihinsa na rayuwa game da matsayin rubutu. Ya ce, East ya koya masa cewa ‘kada ka yarda ka bar mugu ya yi nasara a cikin gina labarinka, domin tasirin barin haka zai iya rusa al’umma.’ Wannan shi ne ke cikin zuciyar yawancin ayyukan adabin da Imam ya gina a cikin Magana Jari Ce. Misali, duk inda ya ji ana maganar itaciyar Yeuw (mai kwankwamai) sai ya mayar da ita itaciyar tsamiya. Gidan Turawa na ginin bene, ba zaure don baki da sa kwat da duk wasu abubuwan jin dadi na rayuwa, irin na Turawa, canza su ya yi da na Hausawa, bai yarda bakon malam Bahaushe ya shigo har cikin gida ba, domin masaukin bako ai zaure ne in ji Hausawa. Haka abinci da abin sha da abin hawa da sauran makamantan su, ba don komi ba sai don wadanda yake wa rubutun su karu da ilimin da ke ciki da kuma inganta kyawawan al’adu. Kila, wani ya ce a wancan zamani da su Imam suke raye ne ai ake yin hakan, yanzu fa, yaya al’adun Hausawa suke, yaya za a iya bambanta na ainihi da wanda yake bako? Abin nuni shi ne zamani ai riga ne, in Imam ya hana bako wucewa cikin gida sai dai zaure, za mu ga cewa ya yi daidai da zamaninsa, kila mu yanzu, bakon har cikin dakunan masu gida yake shiga, shi ma sai a bayyana dalilin yin haka, da zamani ya zo da shi, ba wai a turbude shi tamkar shi ne mafita ga al’umma ba. Shi ya sa a yawancin rubuce-rubucen marubutan kwarai za a ga ba su yarda mugu ya sha daga muguntarsa ba, ba su barin azzalumai su wuce da zaluncinsu, ba su barin kunci ya tabbata a cikin rayuwa. Duk yadda za su yi za su nuna wa masu karatu, kyau da rashin kyawun abu, irin wannan shi ya bi ya gina tunanin marubutan kwarai da adabi mai walwala. Wannan kuma shi ya sa, har yau har kwanan gobe ayyuka irin wadannan da marubutan suka rubuta da kewar mutanensu da tunanin mutanensu da neman inganta rayuwar mutanensu suke kasancewa kamar yau ne aka yi su duk da cewa sun yi shekara dari da dabbakawa. Darussan da ke cikin irin wadannan ayyukan adabi har yau suna da tasiri a rayuwar jama’ar yau din, ba wa sai na jiyan ba, za su kuma ci gaba da wanzuwa a haka har gobe da yardar Allah. Tambayar da kila wasu ke faman yi ya zuwa yanzu ina jin ba ta wuce to mu wa muke wa rubutu ba, don me mu muke yin rubutu? Muna yin rubutun ne don mu samu na cefane, wato mu sami abin da za mu ciyar da kanmu da iyalanmu? Ko kuwa muna yin rubutun ne don gwamnati ta san da mu ta ba mu kwangila ko lambar yabo? Ko kuwa muna yin rubutun ne don talakawa masu karantawa su sami abin nishadi ko kuwa don dai kawai rubutu maganin wani ciwo ne, idan ba mu yi shi ba, ba za mu samu saukin radadin ciwon ba? Kafin na bayar da wannan amsa, zan so in dan mazaya tukun, domin ta haka ne nake jin za mu sami haske game da irin rubutunmu da wadanda muke wa rubutun. Rubutu baiwa ce, Allah ke sa ilminsa in da ya so ga wanda ya so, yadda ya so a lokacin da ya so. Wasu kuma haye suke masa, su kuma kasance ‘yan gida a cikinsa, ta yadda duk abin da dan gado zai iya yi, su ma za su iya, kila ma har su fi ‘yan gida. Saboda haka kowace irin dama mutum ya samu ya zama marubuci, abin da ke da muhimmanci shi ne ya san tasirin irin rubutun da yake yi da kuma inganci ko akasin haka. Masana rubutu na yin kirari da cewa alkalami ko biro ko ma dai wane irin abin rubutu ya fi takobi kaifi a fagen juyin-juya-hali ko canjin lamurran rayuwa. Ke nan alkalami ko wani abin rubutu babban makami ne na sauya lamurran rayuwa, idan an yi amfani da shi yadda ya dace. Ke nan abin da ya dace mutum ya fara da shi a fagen rubutu shi ne sanin wadanda yake wa rubutu. Kai da ke karanta wannan bayani a yau, tambayi kanka wa kake yi wa rubutu? Hausawa ko Turawa ko Larabawa ko wasu baki? Idan Hausawa kake magana da su a rubutunka, to ya dace rubutun nan naka a cikin jarida ne ko mujalla kake yin sa ko kuma labari ne ko waka ko kuma wasan kwaikwayo ka gwanance kai, to ya kasance a cikin harshen da mutanenka za su gane, za su fahimta, za su kuma iya yin aiki da shi yake. Saboda haka kai da ke nan tare da mu wa kake wa rubutu? Mutumin Garun-Ali ko kuma Yorkshire ko Manchester Makka ko Madina ko Lahore ko ina? Kai da ke ta fafutukar rubuta waka ko rera ta. Kai da ke tsara da kuma rubuta da aiwatar da wasan kwaikwayo. Kai da ke ta faman zayyana labarai cikin fasaha kala-kala. Kai da ke ta faman rubutu cikin jarida ko mujalla ko Intanet da. Kai da ke faman sai ka wallafa littafi a kowace rana ta Allah, don me kake wannan hankoro, domin kedafare ko kuwa don a san ka a matsayin marubuci? Me ya sa kake rubutu? Wa kake wa rubutun? Wace ribar kake nema daga rubutu? Mu hadu a aji ranar Lahadi mai zuwa 23 ga watan Yuni, 2013 domin samun karin haske ko kuma mafita!

No comments:

Post a Comment