Wednesday 3 July 2013

Bayani Kan Rubutaccen Labarin Hausa

SHARHI KAN SAMUWAR ZUBE DA YADDA YA SAUYA KAMANNU A TSAKANIN SHEKARUN 1920 ZUWA 1980 ZUBE DA RABE –RABENSA A HAUSA Zube kalma ce ta Hausa da ke da fuskoki guda biyu, da farko akwai fuskar lugga sa’annan akwai fuskar zahiri. A zahirance zube na nufin abu ne a watse ko wanda bai da wani tsari ko dokoki da ke tafiyar da shi, alal misali kara a zube, na nufin yadda karan ke warwatse ba tare da wani shiri ko tsari ba. Ke nan zube na iya nufin duk wani abu da aka yi shi ko aka tsara shi ba bisa bin wasu ka’idoji ko tsari ba. Amma idan ana magana kan zube na lugga, yana nuna abin ya samo asali daga aikatau zuba, wato kamar ka zuba ruwa a kwano ko kasa, wannan shi ya haifar da kalmomi irin su zubar da ko zubewa ko zube ko kuma zubo daga cikin kalmomin aikatau na harshen Hausa, duk dai wadannan na nufin abin da aka aikata na watsarwa ko yasarwa ko makamantan haka. A adabance kuwa zube na nufin guntattakan jawabai ko bayanai da ke zuwa kara zube ba tare da wasu dokoki ko ka’idoji ba, sa’annan ana yin su ne domin a sa nishadi ko jin dadi ga mutane. A nan ana iya bambanta zube da waka da wasan kwaiwayo ta fuskar adabi, wato ana iya cewa a waka da wasan kwaikwayon sai an tsara, an kuma shirya, sa’annan kuma a daidaita tunani kafin a aiwatar da su alhali kuwa a zube ba a bukatar wadannan abubuwa. Ke nan zube na na nufin abubuwa irin su tatsuniya da karin magana da tarihi da tarihihi da kirari da zambo da almara da kissa da karangiya ko salon magana ko bakar magana. Bari mu dauki wasu daga cikin wadannan domin mu ga yadda fasalinsu ya kasance. ZUBE A ZAMANIN ZUWAN TURAWA Ko da Turawa suka shigo sassan kasar Hausa ba su shigo kasar a jahilce ba, domin suna da wata masaniya a kan mutanen wurin da kuma yanayin kasar. Labaran farko sun je gare su ne daga ayyukan matafiya da suka ratsa Kasar Hausa, suka wallafa littattafai game da kasar da mutanenta, daga cikin irin wadannan marubuta da masana akwai Ibn Batuta da kuma Leo Africanus. Shi Leo Africanus a cikin littafinsa na 7 ya bayyana labarin abubuwan da ya gani ko ya ji a lokacin ziyarar da ya kai Afirka. Saboda haka tun a karni na goma sha tara (19) kungiyoyi daga jinsin Turawa, sun aiko da masana don su binciki yadda kasashen Afirka suke da yadda al'adunsu ke gudana da yanayin harsunansu da kuma addinansu. Sa'annan kuma su bincikio hanyoyin sadarwarsu ta ruwa da ta kasa da kuma matakan da suke amfani da su ta fuskar ciniki da saye da sayarwa. Wannan kokarin sanin yanayi da al’ummar nahiyar Afirka da Turawa suka yi ya kawo kakkafa kungiyoyin Turawa masu manufofi daban - daban. A Ingila an samar da Kungiyar Afirka a 1788. Wannan kungiya ita ta turo su Mungo Park da Clapperton da Denham da 'yan uwan nan guda biyu wato Landers Brothers, wadanda suka ziyarci yankunan kasar Hausa. Baya ga wadannan kungiyoyi na neman sanin halayen da kasashen Afirka suke ciki, akwai kuma kungiyoyin Mishau da Turawa suka turo don bincike, musamman kan al'adu da harsuna da addinan kasashen Afirka a tsakanin karni na 18 da na 19. Shahararru daga cikin wadannan 'yan mishau su ne Barth da Schon. Ta fuskar ayyukan Barth da Schon ne labaran kasar Hausa da jama'arta suka isa Turai, kai tsaye. Barth ya wallafa littafi mai dauke da bayanan abubuwa da ya ji, ko ya gani a arewaci da tsakiyar Afirka a tsakanin shekarar 1857 zuwa 1859. Ya kuma wallafa wani littafi mai dauke da bayanan harsunan Hausa da Fulani da Barebari da Wangala da Bagurma a shekarar 1862. Wanda ya wanzar da rubutun adabin Hausa sosai ta fuskar amfani da haruffan Romanci shi ne J.F. Schon. Ya zo Yammacin Afirka ne a karkashin kungiyar Mishau ta C.M.S, inda a 1832 ya ziyarci Senegal. A takanin 1841 har zuwa 1847 ne ya ziyarci kasar Hausa da wasu yankunan kasar Neja. Wadannan yawace-yawace da Schon ya yi sun sa ya iya wasu harsuna da yawa har ya sami kwarewa a cikinsu, musamman harsunan wuraren da ya ziyarta. Ta haka ne kuma ya sami damar yin nazari da rubuce-rubuce a kan wasu harsunan, musamman harshen Hausa. Ya wallafa littattafai kan kalmomin Hausa a 1843 da Kamus na harshen Hausa a 1876 da Littafin Karin Maganganu da Labarai da Tatsuniyoyin Hausa a 1886 da kuma Littafin Magana Hausa (1885) da wasu da dama da suka shafi addinin Kirista. Ayyukan da su Schon suka gabatar sun bada haske wajen samar da wata kafa ta mayar da adabin bakan Hausa a rubuce. Domin haka, tun kafin a kafa mulkin mallaka a kasar Hausa aka mayar da wasu sassan adabin bakan Hausa a rubuce cikin haruffan Romanci. Misalan wadannan rubuce-rubuce sun kunshi tattara labarai da tatsuniyoyi da karin maganganu da sauran maganganun azanci da al'adun Hausawa wuri guda a takarda. Daga shekarar 1891 aka sami littattafai da yawa da suka kunshi irin wannan fasali. Daga cikin littattafan da suka yi fice akwai Specimens of Hausa Literature na C.H. Robinson (1896) da kuma Hausa Stories and Riddles na H.C. Harris (1908) da Littafi na Tatsuniyoyi na Frank Edgar (1924) da Hausa Sayings and Folklore na Fletcher, R.S (1912) da sauran su. Wannan tafarki da Turawa suka bi shi ne ya wanzar da abubuwan amfani dangane da rubutun bokon Hausa. Ta haka aka sami damar zama don kyautata nazari da kuma rarraba sigogin rubuce-rubucen zuwa azuzuwa mabambanta. Shi ya sa ko da Turawa suka mallake kasar Hausa, ayyukan adabi ta fannin tatsuniyoyi da labarai da maganganun azanci sun sami karbuwa ta amfani da haruffan Romanci. Dangane da haka, zuwan Turawa kara taimakawa ya yi wajen kafa makarantun koyar da nazarin ilmi, inda ta haka ne aka dada fadada hanyoyin wanzar da rubutun Hausa. A wannan lokaci ba a yi wani tanadi dangane da tsarin da za a bi na kyautata ilmin boko ko kuma yadda za a yi da na Musulunci da aka iske ba. Abin da Turawa suka mayar da hankali a kan sa shi ne, tattaunawa kan batutuwan da suka shafi gudanar da ilmi, ba kokarin wanzarwa ba, sai dan abin da ba rasa ba da masu aikin Mishan suka yi Lokwaja da Wusasa Zaria kafin tabbatuwar mulkin mallaka. ZUBE DA SAMUWAR HUKUMOMIN INGANTA ADABI Hukumomin inganta adabin Afirka ba su da wata fuska takamaimiya sai wadda gwamnatin mulkin mallaka ta samar a kowace kasa da take mulki, sai dai domin abubuwa su daidaita an samar da hukumar Kasa da Kasa Ta Nazarin Harsuna da Al’adun Afirka da Kungiyar Afrika da kuma Mujallar da take bugawa ta Afrika tun daga 1908. Wadannan hukumomi sun taimaka wajen dora harsashin samar da adabin Afirka a cikin boko, musamman na Hausa da aka fara jin duriyarsa tun daga 1929. A wannan shekara ce hukumar Kasa da Kasa Ta Nazarin Harsuna da Al’adun Afirka ta shirya gasar rubutun Hausa (kagagge ko zube). Tun da farko an tsara abin ne daga London karkashin kulawar shugabannin Hukumar Nazarin Harsuna da Al’adun Afrika. Wannan hukuma da hadin kan hukumomin kula da ilmi na kasashen Afirka daga farkon shekarun 1920 sun shirya gasar rubutu tsakanin dalibai da malaman makarantun kasashen a cikin harsuna ‘yan gida kan zube da kagaggun labarai. A kasar Hausa yawancin wadanda suka shiga gasar malaman makarantun boko ne. Alal misali gasar da aka yi a 1929, littattafan da aka samu har guda 37 ne, 10 a cikin harshen Hausa, 15 a cikin harshen Suto, 9 a cikin harshen Ganda da 2 a cikin harshen Madingo da kuma 1 a cikin harshen Mende. Littafin Komane mai taken Esela e isang phethehong a cikin harshen Suto da kuma na Lwanga mai taken Ebyafayo bya Baganda a cikin harshen Ganda, su ne suka zo na biyu, ba wanda ya yi nasarar zama na daya, saura kuwa duk sun sami yabo ne kurum. LABARUN HAUSA NA FARKO-FARKO A RUBUCE Idan aka yi nazarin littattafan da suka sha yabo daga harshen Hausa za a ga cewa sun kasance kamar haka; akwai na H.B.G. Nuhu mai taken Hausa Stories da na Malam Dodo shi ma Hausa Stories, sai na Malam Ahemet Metteden, mai suna Zaman Dara da na Malam Bello Kagara mai taken Littafin Karatu Na Hausa, sai kuma na Malam Nagwamatse, mai suna Takobin Gaskiya. Daga wannan gasa mun fahimci cewa tuni wadanda za su yi wani abin a-zo-a-gani game da kagaggen adabin Hausa sun fara bayyana;Malam Bello Kagara yana daga cikin wadanda suka cinye gasar da hukumar fassara ta shirya a tsakanin 1932 zuwa 1933 da littafinsa Gandoki, shi kuma Malam Nagwamatse duk da cewa bai ci wani abu a gasar 1932/1933 ba, amma ya sha yabo da littafinsa na Boka Buwaye. ZAMANIN HUKUMAR FASSARA Daga abin da muka gani a sama ko da shekarar 1929 ta karasa cika akwai hukumar Fassara a kasar Hausa, domin ita ce ta kasance unguwarzoma a lokacin waccan gasa ta farko. Saboda haka karuwar makarantu da dalibai na gwamnati, ya kara sabon nauyi ne ga hukumar ta Fassara. Saboda a sami hanyar samar da littattafan karantawa da sauran kayan aiki a wadannan makarantu, aka yi shawarar kafa wannan hukuma wadda za ta kula da wannan al'amari a tsarin hukuma ta dindindin. Tun daga 1924 wannan batu ya kunno kai, jami’o’in kula da sababbin makarantu na kasar Hausa sun sha aike wa da rahotanni zuwa Kaduna dangane da amfanin da ke tattare da manufar kafa wata hukuma da za ta samar da kayan aiki na ma’aikatar ilmi da kuma raya adabi, amma hakan ba ta faru ba, sai a 1929, lokacin da aka kafa Hukumar Fassara. Wannan hukuma ta fassara ta fara zama ne a cikin ofisoshin makarantar Dan Hausa da ke Kano. Hukumar ba ta sami mazauninta na musamman ba sai a 1930, inda aka gina shi a Kofar Tukur-Tukur, Zariya. Babban aikin wannan Hukuma shi ne shirya littattafan Hausa don karatu da koyarwa a makarantu. Hukumar ta soma gudanar da ayyuka ne karkashin jagorancin Mista C.E.J. Whitting wanda ya hannunta aikin gudanar da hukumar ga Mista R.F.S.Parry (Jami'i mai kula da ilmi da ke Zariya). A ran 2/4/1931, Kyaftin F.W. Taylor ya amshi ragamar shugabancin hukumar tare da ma'aikata 'yan kasa da suka hada da Malam Sule Isa da Malam Tafida da Malam Umaru, da kuma Malam Shekarau. A shekarar 1931 Hukumar Fasssara ta fuskanci aikin fassara gadan-gadan tare da shirya littattafai don samar da abin karantawa da koyarwa a makarantun gwamnati. Littattafan da wannan hukuma ta fara fito da su sun ta’allaka ne kan tarihin kasar Hausa, inda aka shirya littafin Hausawa da makwabtansu da kuma fassara littafin Koyar Da Kiwon Lafiya (I). Daga nan kuma aka tsara littafin Jimlolin Hausa Zuwa Ingilishi. Akwai kuma littafin Koyarwa na Lissafi da Littafin karantawa na fari. Har wa yau, a shekara ta 1931 aka tsara littafin Labaru Na Da Da Na Yanzu (NAK/KAD/EDU/746). A ranar 18 ga Fabrairu 1932, Kyaftin Taylor ya ajiye aikin shugabancin hukumar fassara, wannan ya sa aka rufe hukumar na wani lokaci, sai a ran 17 ga watan Mayu aka sake bude hukumar a Katsina, a karkashin shugabancin Mista R.M. East. Daga watan Disamba na 1931 zuwa watan Fabrairu na 1932, hukumar fassara ta samar da littattafai da suka hada da Darussan Koyarwa Don Makarantun Elementare da littafin Bayani Kan Cututtuka da kuma Magaurayi. A wannan shekara kuma aka kammala fassara littafin Koyar Da Kiwon Lafiya (II), aka kuma sake wa Aljaman Yara fasali, aka sake buga shi. Hukumar ta yi gyare-gyare ga littafin Labaru Na Da Da Na Yanzu, inda aka fassaro sassan tarihin kasar Hausa da suke rubuce cikin harshen Larabci, aka zuba su a cikin wannan littafi. Tun daga shekarar 1932 R. M. East ya soma nuna damuwarsa dangane da yadda hukumar fassara ke gudanar da ayyukanta. A nasa tunanin, ya ga cewa ayyukan da ya kamata hukumar ta yi sun wuce fassara kawai. Shi ya sa yana hawa bisa ragamar shugabancin hukumar ya shiga fiddo da sababbin abubuwa da za su inganta aikin hukumar. Baya ga fassarar ayyukan gwamnati da littattafan Elementare, hukumar ta tsara da buga littattafai da dama, ga kuma buga Jaridar Nijeriya Ta Arewa da aka soma a 1932. Haka kuma a sakamakon wannan tunani na R.M. East na kokarin inganta adabin Hausa ya sa aka soma tunanin yadda za a samar da kagaggun labarai daga ‘yan kasa domin nishadantar da al’umma. Haka kuma an hada har da yin talifi da kuma sayar da littattafai da aka rubuta a cikin harsuna daban-daban na kasar Hausa don samun riba. Hukumar ta tsara yarjejeniya da mawallafa da masu buga littattafai da kuma tsangayoyi na ilmi na Larduna kan tafarkin da ya dace su bi a ga an sayar da littattafan da hukumar ta tsara, ta kuma buga. SAMUWAR LABARIN FATIMA Har zuwa farkon shekarar 1933, hukumar fassara ta ga ba a sami littattafan adabin da take bukata da suka shafi kagaggun labaran Hausa ba. Sai dai wani abin la’akari ko da hukumar ke ta wannan fafutika, su ‘yan Mishau tuni sun yi nisa a wannan fage na samar da kagaggun labarai, domin kuwa W.R.S Miller da kungiyar Mishau ta C.M.S tuni suka fahimci amfanin wannan fasali na kaga labari, domin isar da sako, saboda haka sun fitar da littafin kagaggen labari na farko da aka buga da harshen Hausa mai suna Fatima, na Miller a 1933. Wanda da alama bai gamsar ba, shi ya sa ba a ji amonsa ba a cikin karikitan kagaggun labaran Hausa tun wancan lokaci. Kila ba wani abu ya sa haka sai domin ba ya dauke da komi sai wa’azin kirista da yada manufofin addinin Kiristanci. Watakila ganin irin rawar da C.M.S da Miller suke neman takawa ya sa aka shirya gasa ta biyu da ta taimaka wajen samar da littattafan adabin Hausa na farko ta fuskar zube daga ‘yan gida. An dai shirya wannan gasa ne da manufofi biyu. Da farko a samar da ingantattun littattafan adabi, na biyu a sayar da littattafan, ba a raba kyauta ba kamar yadda aka saba yi a da.25 Wannan gasa ta samar da littattafai da suka inganta tare da kyautata adabin Hausa, an gudanar da ita ne a shekarar 1933. GASAR LABARAN HAUSA TA 1933 Hukumar Talifi ta sami littatttafai da dama da suka amsa kiran shiga wannan gasa. Da yawa daga cikin littattfan da aka rubuto, aka aiko wa hukumar sun dace da tsarin da ta shimida. Lokacin da Hukumar ta zo buga littattfan wadanda suka lashe gansar, sai da ta tace su sosai, musamman ta tattace farkonsu da karshensu, ta kuma sake tsarin wasu daga cikin babobinsu, sa'annan ta buga su. Bayan da Hukumar Talifi ta gama tsara da sake fasalin wadannan littattafai ta fitar da sakamakon gasar kamar haka: (i) Ruwan Bagaja Malam Abubakar Kagara (An buga shi 1935) (ii) Gandoki Malam Bello Kagara (An buga shi 1934) (iii) Shaihu Umar Malam Abubakar Bauchi (An buga shi 1934) (iv) Idon Mtambayi Malam Muhammadu Gwarzo (An buga shi 1934) (v) Jiki Magayi East da Tafida (An buga shi 1934) Duk da cewa wadannan su ne aka zaba a matsayin wadanda suka ci gasar, akwai wasu da suka gamsar, aka tsara su don bugawa, amma ba a sami damar buga su ba, su ne: (i) Boka Buwaye Malam Nagwamatse (ii) Yarima Abba Malam Jumare Zariya. Bayan gasar da littattafan da ta samar, an sake tsara tare kuma da juya sigar wasu littattafai guda biyu wato A handbook On The Teaching Of The Elementary School History and Geography da aka fassara da Koyarwar Labarin Kasa Da Tarihi da littafin Al'amurran Duniya Da Na Mutane. Ganin irin kwazon da Abubakar Imam ya nuna a gasar da aka yi ta 1933 da littafinsa na Ruwan Bagaja da aka buga a 1935 ya sa a shekarar 1936 aka gayyaci Abubakar Imam domin ya wallafa littafin Magana Jari Ce (I-III). Ya dace a yi bayani a nan game da yadda aka yi aka tsara littafin Magana Jari Ce, da irin yadda rubutun littafin ya jawo sauya sunan hukumar daga ta fassara zuwa ta talifi. Kamar yadda Abubakar Imam ya bayyana a cikin littafinsa na tarihi, ko da aka nemi ya tafi Zaria don aikin Magana Jari Ce ya isa ofishin hukumar ne da tunanin yaya wurin yake.Yana zuwa kuwa abin da ya soma magana kai shi ne sunan hukumar, nan take kuwa ya nuna cewa ya dace a sake dubar sunan,wato na Ofishin Fassare-Fassare,domin kuwa ayyukan hukumar sun fi na fassara kawai, kamar yadda ya gani kuma ga shi ya zo yin aikin talifi ne ba fassara ba. An bada aron Abubakar Imam domin aikin Magana Jari Ce daga 21/5/36 zuwa 19/11/36, saboda haka ko da East a ranar 24/10/1936 ya aika da wasika ga Babban Sakatare Mai Kula Da Harkar Ilmi domin a sauya sunan hukumar ta fassara da alama shawarar Abubakar Imam ce ya dauka, domin kuwa a daidai lokacin Abubakar Imam na tare da East a Zariya, sai dai ba a sami damar yin wannan sauyi ba sai a ranar 2/11/1937, inda aka kira shi da ‘Hukumar Talife-Talifen Harsunan Afirka,’ inda daga baya ya koma Hukumar Talifi a takaice. A shekarar 1937 a sakamakon yarjejeniyar da aka yi da Mishan-Mishan da Hukumar Talifi aka amince su fitar da littattafai don amfani a makarantunsu, musamman a kananan azuzuwa na makarantun Elementare, amma an hana su danganta littattafan da wani addini. Littattafan da aka fara samar wa a karkashin yarjejeniyar sun hada da Ka Koyi Karatu (1938) da Ka Kara Karatu (1938) na kungiyar S.I.M da ke Jos. Wadannan littattafai su suka jawo hankalin Hukumar Talifi ta sake neman Abubakar Imam ya wallafa littattafan karantawa a kananan azuzuwan Elementare don Magana Jari Ce an ga ta yi girma ga wadannan azuzuwa. Ya rubuta littattafai guda biyu a Katsina, su ne Karamin Sani Kukumi Ne (I-II) a cikin watan Satumba, 1938. A shekarar 1938 ne aka soma maganar buga wata jaridar Hausa, wadda za ta kunshi abubuwa daban daga wadanda tsohuwar jaridar Nijeriya ta Arewa ke kunsa, aka kuma nada Mista L.C. Giles a matsayin Edita, Malam Abubakar Imam a matsayin mataimaki, ta fara fitowa a Janairun 1939. Nada Abubakar Imam a bisa wannan mukami ya kara fadada ayyukan Hukumar Talifi. Samar da jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ya bayar da kafa ta inganta ginuwar ayyukan adabin Hausa. Fitowar Gaskiya Ta Fi Kwabo ya sa jama'a suka raja'a kanta, inda a bugun farko a watan Janairu na 1939 aka sayar da kwafe dubu biyar (5,000), a watan Fabrairu aka sayar da kwafe dubu takwas da dari tara (8,900), a watan Maris aka sayar da kwafe dubu goma sha daya da dari biyu, (11,200). KAFA JARIDAR GASKIYA TA FI KWABO DA KAMFANIN GASKIYA Kafa jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ya kara jawo ra'ayin jama'a dangane da saye da karanta ayyukan adabi. A cikin jaridar, akwai filaye da aka fito da su don makaranta wadanda ke aiko wasiku na bayyana ra'ayoyinsu, ana samun irin wadannan wasiku sama da dari (100) a kowane wata. Kuma akan buga wakokin da wasu suka rubuta da amsa gasar wasannin wasa kwakwalwa da sauran su. Haka ayyukan Hukumar Talifi suka ci gaba da gudana har zuwa 1944, lokacin da ayyuka suka fara yawa sosai. Sa'annan ga kuma aikin buga jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo, wadda daga 1940 aka soma buga kwafe dubu sha biyar (15,000), dalilin da ya sa ta koma fitowa sau biyu a wata. Tsara da fassara littattafai, su ma suka yawaita, dalilin da ya sa tun daga 1939 aka dinga daukar kwararrun ma'aikata 'yan kasa don su agaza. Daga cikin wadannan ma'aikata 'yan kasa akwai Malam Nuhu Zariya da Alhaji Sani Kwantagora, wadanda aikinsu shi ne fassara dokokin gwamnati da wasu jawabai da aka yi a majalisar sarakai. A wannan lokaci ne aka samar da fassararrun jawaban gwamnan Arewa zuwa ga sarakuna da wasu da dama. Dukkan wadannan ayyuka da aka gudanar a Hukumar Fassara da ta Talifi ba wata madaba'a da ake da ita ta hukuma. Sau da yawa ana zuwa Ingila ne ko kuma Jos a buga wadannan ayyuka. Wannan ne ya sa gwamnati ta soma tunanin kafa wani kamfani da zai dinga buga wadannan littattafai. Da taimakon gwamnatin Ingila, a shekarar 1945, aka kafa kamfanin Gaskiya (Gaskiya Corporation) a kusa da ofishin hukumar Talifi a Zariya. Daga wannan shekara sai aka mayar da shirya littattafai da fassara da kuma buga su a rumfa daya. Ta haka ne aka samar da littafin Mungo Park Mabudin Kwara da Bala Da Babiya na Nuhu Bamalli da Yawon Duniyar Haji Baba na Tunau Mafara da sauran su. Daga karshen 1949, makarantun boko suka kara yawaita a kasar Hausa. Kuma shirin gwamnatin Arewa na yaki da jahilci ga wadanda ba su sami zuwa makaranta ba ya kankama. Wannan ya sa daga 1950 zuwa 1953 ayyukan yaki da jahilci suka tsayu sosai,domin haka aka kafa kwamitoci da za su gudanar da azuzuwan karatu da hanyoyin da za a bi wajen koyarwa da kuma shirya littattafai don makarantun da aka bude. Wannan yunkuri shi ya haifar da kafa Hukumar NORLA a shekarar 1954. Hukumar ta gudanar da ayyuka da dama, musamman tsara da kuma buga littattafai da buga jaridun Larduna. An wallafa littattafai masu yawan gaske, wadanda suka kunshi darussa daban-daban da suka hada da addinin Musulunci da labarai kamar su Ibada Da Hukunci. Wasu littattafan sun kunshi tarihi kamar, Zuwan Turawa Nijeriya Ta Arewa da Tarihin Fulani da kuma Hanyoyin Koyar da Sana'o'in Hausa da littattfan hira da nishadi daban-daban, tare da wakokin Hausa, nau'i-nau'i. SAMUWAR HUKUMAR NORLA Ana iya cewa Hukumar NORLA ita ce ta habakar da ayyukan adabin Hausa fiye da sauran hukumomin da aka yi a baya. Ta ci gaba da gudanar da wannan aiki har zuwa 1959, lokacin da aka rushe ta, aka mayar da aikinta hannun kamfanin Gaskiya. A wannan lokaci ne aka buga littafin Gangar Wa'azu da Zamanin Nan Namu da Jatau Na Kyallu. Haka aka ci gaba da gudanar da aikin inganta adabi har lokacin da aka samar da yarjejeniya tsakanin gwamnatin Arewa da wani kamfani na Ingila mai suna Macmillan, wanda ya haifar da kamfanin wallafa littattafai na Arewa (NNPC) a 1966. Samuwar wannan kamfani ya sa saiwar gina littattafan adabi ta dasu zuwa wasu sassa na kasar Hausa. A wannan kamfani ne aka sake tsara da buga wasu tsofaffin littattafan da hukumomin baya suka samar. Shi ma wannan kamfani na NNPC ya taka muhimmiyar rawar wajen bunkasa tare da samar da hanyoyin habaka cigaban wanzuwar littattafan adabin Hausa. KAFUWAR HUKUMAR NNPC Haka aka dinga gudanar da aikin inganta adabi har lokacin da aka samar da yarjejeniya tsakanin gwamnatin Arewa da wani kamfani na Ingila mai suna Macmillan, wanda ya haifar da kamfanin NNPC a 1960. Samuwar wannan kamfani ya sa saiwar gina littattafan adabi ta dasu zuwa wasu sassa na kasar Hausa. A wannan kamfani ne aka sake tsara da buga wasu tsofaffin littattafan da hukumomin baya suka samar. Shi ma wannan kamfani na NNPC ya taka muhimmiyar rawar gani wajen bunkasa tare da samar da hanyoyin habaka ci gaban wanzuwar littattafan adabin Hausa. Baya ga ayyukan da ta rinka bugawa kan adabi da sauransu, hukumar ta sa gasa ta kagaggun littattafai a cikin shekarar 1980 inda ta buga uku daga cikin wadanda suka yi nasara. Littattafan da suka fito daga wannan gasa sun hada da Mallakin Zuciyata na Sulaiman Ibrahim Katsina da So Aljannar Duniya na Hafsat Abdulwaheed da kuma Amadi Na Malam Amah na Magaji Danbatta. ABUBUWAN DA SUKA GINA LABARUN ZUBE DAGA 1960 ZUWA 1980 Abin kula daga farko shi ne a fahimci cewa shekarun 1960 sun kasance na samun ‘yancin kai da juyin mulki da kuma yakin basasa. Ma’ana a cikin shekarar 1960 Nijeriya ta samu ‘yancin kanta, saboda haka labaran zube da suka famtsamo daga wannan lokaci za a ga suna da sifofin kwatar ‘yanci da kishin kasa da kuma gwagwarmayar rayuwa bayan samun mulkin kai. Saboda haka baa bin makaki ba ne marubuta su yi amfani da wannan dama su kalli rayuwar al’ummarsu ta wannan lokaci. Da kuma aka yi juyin mulki a shekarar 1966 aka kashe ‘yan siyasar farko na Arewacin Nijeriya sai abubuwa suka canza a farfajiya da tunanin al’ummar wannan yanki. Da kuma aka yi rikicin A-Ware bayan juyin mulki a arewacin Nijeriya, wanda ya jawo sake yin juyin mulkin Gowon sai al’amurra suka canza fasali. Wannan shi ya jawo rikicin Nijeriya day a kai gay akin Basasa daga 1967 zuwa 1970. Wannan takaddama da ta faru za ta yi tasiri a rayuwar al’ummar Arewa da kuma musamman marubutanta. Dangane da haka baa bin mamaki ba ne idan labarun zuben da da aka rubuta a wannan tsakani ko kuma wadanda suka biyonsu suka kasance masu dauke da wannan ruhi, na rikice-rikice da fadace-fadace da halbe-halbe da uma siyasar irin ta kishin kasa. Alal misali labarai irin Kitsen Rogo na Abdulkadir Dangambo da Karshen Alewa Kasa na Bature Gagare da Zabi Naka na Munir Mohammed Katsina, suna dauke da irin wadannan fasaloli. Alhali kuma rayuwar da ta shafi ginuwar tattalin arziki da ilmin boko da zamantakewar yau da kullum ta wannan zamani ta taimaka wajen samuwar wasu rubutattun zube. Ma’ana, yadda aka samu garabasar man metur daga farkon shekarun 1970 da yadda kuma aka ga bullar dalibai masu tarin yawa daga shirin UBE na 1976, wanda daliban farko suka antayo cikin al’umma da kishirwar son karatu da kuma bullar kayan kallo irin na talbijin da bidiyo a daidai wannan lokaci shi ma ya kara sa wa marubuta kaimi na rubutun zube, musamman daga rayuwar da suka tsinkaya. Labarai irin su So Aljannar Duniya da Tauraruwar Hamada da Tauraruwa Mai Wutsiya da Turmin Danya da wasu da dama bisa wannan tafarki suka wanzu. A ciki ne za a ga rayuwar sumogal da soyayya da ilmin zamani da yadda zamantakewar al’umma baki daya. Saboda haka duk yadda aka so ba zai yiwu ba a canza tunanin marubuci daga abin da ya riska ko ya riske shi ko kuma tsinkayar yadda lamurra za su kasance a cikin labaran da yake rubutawa. WASU HANYOYIN NAZARIN LABARAN ZUBE Hanyoyin nazari uku za mu bi domin mu aza misalin yadda za a iya kallon rubutun zube. Akwai Jigo da Warwarar Jigo da kuma Nazarin Salo. JIGO Jigo kalma ce Bahaushiya da ke da ma’anoni mabambanta. Tun da farko Hausawa na yi mata kallon ginshiki da e cikin daki ko kuma gini. Haka suna kallonta a matsayin tubali ko tushe ko fandashin da ke dauke da gini. Haka kuma suna yi mata kallon wani muhimmin kayan aikin da masu noman fadama ke amfani da shi wajen ban ruwa. Idan aka yi dubi wadannan ma’anoni da Ba haushe ya bayyana game da jigo za a ga cewa ba wani abu suke nufi ba face mazaunin abu, ko mafarinsa ko kuma abu mai muhimmanci da kila in ba shi a cikin tsari wani abu ba zai wanzu ba. Misali ginin da bai da fandeshin da wuya ya yi karko, mai noman fadama da bai da kwaryar da take kai ruwa ga gona, da wuya noman ya dore. Haka kuma dakin da bai da ginshiki da wuya ya yi karko. Ke nan wannan abu jigo da masu adabi suka aro sun mayar da shi ne a matsayin sako, manufa, ko abin da waka ko zube ko wasan kwaikwayo suka kunsa. A nan ana maganar abin da labarin ya kunsa ko yake magana kai ko kuma ruhinsa. Wato dai duk wani abu da in ba shi a cikin labarin to da wuya labarin ya zauna ko ya yi armashi. Saboda haka idan ana magana kan jigon labarin zube, ana nuni ne ga babbar manufar marubucin, wato wadda ita ce a zuciyarsa a lokacin da yake kokarin tsara labarin. Alal misali labarin Ruwan Bagaja babban jigon bai wuce shashantarwa ba, ko kuma a ce nishadantarwa. Wato an gina labarin domin a sa dariya da nishadi. Ko kuma littafin Jiki Magayi da ya kasance bisa tunanin soyayya, ko kuma Shaihu Umar da ke fadakarwa ko labarin Amina ko Mace Mutum da ke neman ‘yancin mata. Abin da za a kara a nan shi ne baya ga babban jigo kuma ana da kananan jigogi da suke taimakawa wajen gina labarin, su wadannan kuma kowane mai nazari da yadda yake kallon su. Alal misali a cikin lbarin Ruwan Bagaja akwai karamin jigon kara da ilmi da yawon bude ido da wasu da dama. Haka ma a labarin Shaihu Umar an sami kananan jigogi irin na ilmi da soyayya da makamantan su. WARWARAR JIGO Abin da ake nufi da warware jigo kuwa bai wuce mai nazari ya bi zaren da ya dinke labarin ba yana yi masa kulli ta yadda zai sami hadi guda, wato ya bude labarin nasa, sa’annan ya ja zaren ta amfani da babban jigon domin ya tabbatar sakon bai fandare ba. Ana iya ganin haka a cikin labarin So Aljannar Duniya inda aka dinke zaren da kitsa soyayyar Badodo da Yasir. Ko kuma ban dariyar da ke cikin labarin Ruwan Bagaja har zuwa karshen labarin da za a dire da wani abu na daban. SALO Shi kuwa nazarin salo a labaran zube hanyoyi uku suke yi masa jagora. • Zabin kalmomi • Dabara • Mutum ZABIN KALMOMI Idan ana son a fahimci salo to ya dace a gane irin siffofinsa na asali. Ba wani abu ba ne salo face irinkalmomin da mai rubutu ya zaba da gangan domin ya gina labarinsa ko waka ko kuma wasan kwaikwayo. Idan aka ce salo zabi ne na kalmomi ana nufin gwaninta ce mutum ya zabi kalmomin da za su burge ko su sa tunani a wajen mai karatu. Alal misali a waka: ‘Yar budurwa son ki nake Kin bugan sarka a wuya In na yo carar zakara Kyarkyarata gun ki take Shi ko wancan son da yake Duk bidar zakinki yake Daga wadannan baitoci za a ga cewa mai wakar ya zabi kalmomi ne da gangan domin ya gina wakar cikin armashi da burgewa. Kalmomi irin su Sarka da carar zakara da kyarkyara da zakinki duk an zabe su ne su dace da irin salon da aka yi amfani da shi. Haka batun yake a cikin tsarin rubutun zube. Dubi yadda marubucin Kifin Rijiya ya bayyana wahalar da Shaihu Aboki ya sha a duniya: ‘Irin wahalolin da ya sha, da kulli-kucciyan da ya sha yi da hadurra...’ Ta yaya ake yin kulli-kucciya, wannan zabin kalmomi na musamman domin gina salo. Ko kuma yadda aka bayyana cin hanci a cikin labarin Ruwan Bagaja ta sakaya cin hancin ta amfani da dabara. DABARA Haka ana ganin salo a matsayin dabara ko gwaninta ko iyawa ko wata hanya ta burgewa a lokacin isar da sakon marubucin. Dabarar nan tana iya zuwa ta fuskoki daban-daban. Ko dai ta hanyar bude labarin ko gina cikinsa ko kuma dire shi. Alal misali akwai salon da aka saba wajen bude labari irin: A wata kasa... a A wani gari... ko kuma A wani shudadden zamani ko Wata rana... da sauran su. Amma sai a ga marubuci ya kauce wannan tsari da gangan, ya kitsa nasa. Misali a cikin labarin Karshen Alewa Kasa an bude ne da wani salo na musamman: Til kwal! Tin kwal!! Tin kwal!!! Kai za ka dauka daka ne ake yi ba labari ba. SALO MUTUM NE Idan an ce mutum ne salo, a nan ana magana ne bisa irin yadda Ubangiji ya tsira kowane dan Adam. Ba mutum biyu da suke kama da juna ta kowace irin fuska ko hali. Haka kuma tunanin kowane mutum daban yake da na dan uwansa. Ke nan abin da wani ya kitsa a labarinsa yana tafiya da salon nrayuwarsa ne. Duk irin yadda mmarubuci yake gudun sanya halinsa ko rayuwarsa ba zai yiwu ba. Wannan ya kara tabbatar mana da cewa halayyar dan Adam ita ke gudanar da salon da ake gani a cikin labarin da marubucin ya rubuta. Allal misali, salon ban dariya na Abubakar Imam a cikin Ruwan Bagaja ko salon kaddara na Abubakar Tafawa Balewa a cikin Shaihu Umar ko salon tashin hankali a cikin labarin Karshen Alewa Kasa na Bature Gagare abubuwa ne da suke ginu bisa rayuwar marubutan. Dangane da haka ake ganin salon kowane mutum na bayyana ne daga ginuwar rayuwarsa.

No comments:

Post a Comment