Monday, 1 July 2013

WAIWAYE ADON TAFIYA


WAIWAYE ADON TAFIYA!
Idan kila muna son mu fahimci abin da ya sa Turawa kafin bayyanar mulkin mallaka suka ga ya dace su shigo cikin kasahe irin namu sai mun yi nazarin tunanin nasu kafin su famtsama domin assasa mulkin mallakar. Kamar yadda wani masani (Harmand, 1971) ya bayyana, ba wani abu ya sa Turawa fita domin mulkin wasu sassan duniya ba sai don sun fi su ‘wayewa’, wannan wayewar ita ta sa dole su mulki sauran al’ummomi a duniya. Turawa sun fi sassan da suka mulka sanin makamar tattalin arziki da dabashirin yaki da kuma ilmin zamani. Wannan ya sa dole mu mulki saura, mu nuna musu yadda za a gudanar da lamurra.
Nazarin wannan batu da irin sa zai nuna mana cewa Turawa sun yi aune ne kurum, amma ba wani abu da ya kawo su nahiyoyin da suka mulka sai kwadayin abin duniya. Ba su fi sauran sassan duniya wayewa ba. Ba su fi si iya tattalin arziki ba. Ba su fi ilmi ba. Ba wani abu ya kawo su nahiya, musamman irin ta Afirka ba face neman sabuwar kasuwar hajar su da ta yi kwantai. Abin da ya kai su nahiyar Arewacin Amurka da da Kanada da Niyuzilan da kuma nahiyar Asiya da kuma Afirka.
Duk da cewa son kai da neman kasuwa ya kawo Turawa Afirka, duk da haka zuwan nasu ya canza lamurran wannan nahiya, sun zo da ilmin zamani, wanda kamar yadda aka sani ba sun kawo ba ne don taimakon Afirkawa, sai dai don taimakon kan su kurum. Duk wani bayani da suka yi ta yayatawa na cewa Afirkawa ‘jahilai’ ne bai da tushe balle makami. Duk hada-hadar samar da hanyoyin rubutu da suka yi ba wai don Afirkawa ba su da hanyar rubuta tunanisu ba ne. Ko kafin zuwan Turawa Afirkawa na da tsarin ilmi da na rubutunsu, ba wai dole sai rin na Turawan ba. Shi ya sa ma masana irin su Jahn(1968) ke nuni da cewa duk wata wayewa da Turawa suke takama da ita kafin su shigo nahiyar Afirka don mulkin mallaka, dodorido ce, domin kuwa da sun bar Afirkawa yadda suka same su kafin karni na 15 da wayewa da ilminsu da su ma sun mulki wasu sassan duniya.
Saboda haka duk wata farfagandar cewa Turawa sun Afirka domin su taimaki Afirkawa maganar iska ce. Kasuwanci ne ya kawo su. Idan kuma cikin neman kazamar ribar Bayibul ya maye gurbin wadansu abubuwa to ribar kafa ce! Ba Baturen da ya baro Turai domin ya taimaki Afirkawa. Idan sun ba Afirkawa magunguna don su sami lafiya, ba don Allah ba ne, don wanda bai da cikakkar lafiya ina zai iya noma abin da za su kwashe! Idan har sun ilmantar da Afirkawa ba wai don ci gaban mutanen Afirka ba ne. Da sun masakan Kabba da ke Arewacin Nijeriya sun ci gaba da yin sakar da suka gwanance da sai dai su yi kankankan da masakun birnin Manchester. Idan da taimako ya kawo su, me ya hana su sassaka hanyar dogo tun daga Lagos har Sakkwato da Maiduguri da Katsina, amma sai suka dakile shi kurum a Kano da Gusau da Funtua da Kaura Namoda da Nguru? Ba abin da za su tsinto a Sakkwato ko Maiduguri ko Katsina, tun da ba auduga ko gyada ko fatu a can.
ME YA SA TURAWA SUKA NEMI KASHE ADABIN HAUSAWA?
Mun bibiyi wannan tarihi ne domin mu gane yadda lamurran suka samo asali domin mu gane yadda Turawa suka hana adabin Hausawa ya motsa da kyau, suka kuma shigo da ilmin boko da tsarin rubutu da suke ganin zai amfane su ba Hausawa ba. Abin da ya dace a sani shi ne ko da Turawa suka shigo kasar Hausa adabin Hausawa na gargajiya da na zamani kafada da kafada suke tafiya da na ‘wayayyu’ Turawa. Amma da suka zo kasar Hausa maimakon su dora Hausawa bisa turbar da ta dace, sai suka dakile nasu tunanin. Duk abin da suka koya wa Hausawa ta fannin rubutun adabi, wanda suka bari ne a baya a kasar su shekara 100 da suka wuce. Ke nan duk abin da Hausawa za su yi, ba za su taba kamo Turawan ba ta fannin tsara ayyukan adabi, domin kuwa kafin su kammala nakaltar wannan darasi, su sun sha gaban su.
Ba su ba adabin gargajiyar Hausawa muhimmanci ba domin su a ganin su bai da amfani, alhali kuwa kowace al’umma ta duniya da shi ta fara ta zama wani abu. Da suka kawo mana nasu tsarin kuma ba su bari Hausawa sun nakalce harkar yadda ya kamata ba, domin yin haka zai iya zama barazana a gare su. Sun koya wa Hausawa abin da suke ganin shi ne daidai ko da kuwa nan gaba zai zama musu mugun abu.
Ba wai nufina ba ne in ce a koma ga abin da Hausawa ke yi ta fuskar gargajiya kafin Turawa su kunno kai, ko kadan, abin da muka ya dace shi ne a nazarci wannan abu da suka zo da shi da irin inda illolinsa suke da yadda za a kawar da illolin, tun an fahimci babarodo ne aka yi wa Hausawa. Wannan na daya daga cikin manufofin assasa wannan Makaranta.
WACE SHUKAR AKA YI A CIKIN GONAR ADABIN HAUSAWA?
Idan aka yi nazarin tarihin adabin Hausa zamunna uku ke da muhimmanci da za a iya gani a zahiri.
Rubutacciyar waka ta riga ta zauna da gindinta tun zamanin zuwan Larabawa, saboda haka ko da Turawa suka zo riga suka canza mata, daga rubutacciya cikin Larabci da Ajami zuwa rubuttatta cikin Boko. A kula, bayar canza rigar kuma an yi walankeluwa da tunanin marubuta wakokin ta yadda sun bar turbar addinin Musulunci da al’adun gargajiya aka shiga gonar zamani da duk wani tambelensa.
Shi kuwa rubutun zube, irin wanda Bature ya kira kirkirarren labari a rubuce, Baturen ne ya shi go da daga farkon karni na 20 domin kuwa Hausawa ba su da irin wannan fasali.
Wasan Kwaikwayo ko a rubuce kuwa duk da cewa akwai alamunsa, amma irin na zamani bai taka kasar Hausar ba sai a farkon karni na 20 shi ma. Kuma kamar yadda aka sani Turawan ne dai suka shigo da shi.
A darussan da ke biye za mu tattauna wadannan batutuwa daya bayan daya domin kara tantance inda aka fito da in da ake da kuma in da aka dosa.

3

No comments:

Post a Comment