Saturday, 13 July 2013

Rubutu Tamkar Mace Mai Ciki Ne

Rubutu Tamkar Mace Mai Ciki Ne? Tare Da Nyambura Kiarie Rubutu tamkar mace ce, mai haihuwa. Dukkan matakan da mace mai ciki ke bi kafin ta haihu su marubuta ke bi wajen yin rubutu. Tun da farko dai sai an yi cikin da za a haifa, a shiga wahalar nakuda daga baya a haifi abin da aka dauka na tsawon watanni. Abin nan da aka haifa, wato rubutun, kowa ne iri ne, tamkar jinjiri ko jinjirar da za a haifa ne, za su zo cikin duniya suna kuka, da bubbuga kafafu, suna ta fafutukar yadda za su rayu a cikin doron kasa; ana so ko ba a so; ana murna da zuwan su ko ba a murna. Yadda ake haihuwar jarirai da wata tangarda, haka shi ma rubutu ake haihuwarsa da tangarda irin tasa; wata tangardar za a gan ta a fili da zarar an haife shi, wata kuwa boye take, sai an fado hannun unguwar zoma ko mai amsar haihuwa za a ga tangardar. Sai dai a lura kamar abin da aka haifa ne; shi ma rubutu da zarar ya shaki iskar duniya to ba ya komawa cikin mahaifa domin a gyara tangardar da aka gani a jikinsa. Idan abin da aka haifa ya zo da hanci nakusasshe ko da baki wangalalle, ba a mayar da shi cikin mahaifa a sake masa kama; to shi ma haka rubutu yake, da zarar aka kammala shi to ba a sake masa kama; yana nan yadda yake; har abadan. Matsalar rubutu ke nan, da zarar aka haife shi to rayuwa ta zama jazaman, yana nan biye da mahaifansa ko dai ya sa a dinga ce da su Alla-sam-barka ko kuma a dinga yi musu tofin Alla-tsine. Rubutu tamkar dan da aka haifa ne ba tare da wata gata ta musamman ba; idan ya diro a doron kasa ba dole ba ne a yi shewa da ayyururui, tamkar dai dan da aka haifa mahaifinsa ya yi watsi da shi; ya ki nuna masa soyayya irin ta mahaifi. Komin runtsi, komin wahala sai ya rayu. Duk kamannun da ya zo da su dole a tarbe shi haka nan. A lura da kyau, idan aka haifi rubutu da ciwon noma ba abin da unguwarzoma za ta iya yi masa, sai dai a yanka na yankawa a bar na bari; a binne na binnewa. Rubutu kamar nakuda yana tafe da nasa zafi da wahala da rashin jin dadi, amma ba zai hana a ci gaba da daukar ciki da kuma wata wahalar haihuwar ba, dole ne a ci gaba da haihuwa; yawan bari kamar na mai haihuwa ba zai hana marubuta ci gaba da shirin wanzuwar wani sabon rubutun ba. Kullum marubuta, bayan kowace haihuwa ko bari suna cike da alwashin sake yin ciki da haihuwar wata sabuwar halittar; komin runtsi. Marubuta suna da zuciya irin ta mahaifiya ne, mai tausayi da kula da abin da aka haifa. Kamar kuma kowace mahaifiya, marubuta ba sa iya hana makwabta zagin abin da aka haifa wanda daga baya ya girma ya kasance takadari. Suka da zagi da mangari dole ne wannan abu da aka haifa ya tashi cikinsu. Daga karshe duk yadda wasu suka so ba a iya hana haihuwar rubutu, ba a iya kuma hana rubutu ya yi ta kwakwakwa-da-kwakwazo a doron kasa, domin an haifi rubutu ne ya bayar da labarin abin da ke wakana cikin doron kasa. Ke nan duk ranar da tawadar rubutu ta kare, duk ranar da aka hana marubuta haihuwa, duk ranar da aka hana marubuta bayyana ra’ayoyinsu tamkar an sa wuka ne an fafe cikin al’ummar duniya ne. Haka kuma ranar da aka hana marubuta yin rubutu tamkar an hana mace daukar ciki ne. Ken an marubutan da aka hana yin rubutu sun zama tamkar mace ce da ba ta iya daukar ciki balle ta haihu, ina amfanin badi ba rai? Nyambura Kiarie 2013©

Wednesday, 3 July 2013

Me Ya Sa Muke Yin Rubutu?

DON ME MUKE YlN RUBUTU? Kwalwa ita ce kandamin da ke ajiye da duk wani tunani na dan Adam. Daga cikinta ne ake tsara da shirya da kuma luguden dukkan abin da ake so ya kasance na rayuwar yau da kullum. Idan har an kammala dafuwar ne sai harshe ya shigo domin idar da sako.Kamar yadda aka sani, harshe shi ne injin din da ke sarrafar da kuma aiwatar da duk tunani da kwalya ta shirya ko ta tsara a cikin kowace irin al’umma. Da harshe ne ake fiddo yawancin al’adu da adabi da ma duk wani ilmi na rayuwar dan Adam, ta fuskar bayyanawa ta baki ko kuma a rubuce. Wannan dama ce ta sa ake ba harshe muhammanci, ta yadda wadanda ba su da shi sukan kasance nakasassu, wadanda kuma suke amfani da wani abu makamancin sa, ake musu kallon wadanda ba su cika ba a cikin al’umma. A nan ina magana ne kan bebaye ko kuma masu kama da su da kuma masu amfani da hito a matsayin hanyar sadarwa a tsakanin mutane, misali al’ummar Mazatec da ke kasar Mexico, haka wannan yanayi yake ko a cikin rubutaccen harshe. Duk wadanda ke da hanyar rubuta harshensu, ana yi musu kallon wadanda suka ci gaba, suka fi sauran al’ummomi na duniya wayewar kai da sanin abin da duniya take ciki. Wannan shi ne fasali na farko da aka fara amfani da shi wajen gane bambancin da ke tsakanin Turawa da bakaken fatar Afirka, dab da za a yi mana mulkin mallaka. Rubutu, ko kuma in ce harshe a takarda shi ne ya sanya wa Turawa ji da kai da kuma tokabo, har suke ganin cewa ba wata hujja da bakaken fatar Afirka za su kyamace su dangane da zuwan su nahiyar a madadin ‘yan jari hujjar wancan lokaci. Ba sai an fada ba, harshe a magance da kuma rubuce ya kara sanya wani wagegen gibi tsakanin Turawa da mutanen Afirka, domin kuwa ko da suka yi amfani da alburusai da bindigogi wajen cin wannan nahiya ta Afirka, daga cikin rubutaccen harshe aka samo wannan tunanin. Saboda haka ko da masana irin su Jahn (1963) ke bayanin cewa, ai ko da Turawa suka zo Afirka sun iske mu da wayewar kanmu da tunaninmu da kuma ci gaban zamani irin namu, shi kuma Rodney (1973) ya kara jaddawa ta hanyar cewa ai zuwan Turawan ma ya dakushe ne a maimakon ya taimaka wajen ciyar da nahiyar Afirka gaba, kuma ko kafin zuwan Turawa akwai wasu al’ummomi da suke da harshensu a rubuce, akwai kuma wadanda ke da hanyar sadarwa ta gargajiya; irin ‘yan ma’abba da kuma kida da ganguna ko makamantan haka wajen sadarwa; wannan bai nuna mana irin yadda tunanin jama’ar nahiyar Afirka ya kasance ba a zahiri. Domin kuwa mulkin mallaka abin da ya mayar da hankali shi ne sanya mutumin Afirka ya dinga tunani da rubutu a cikin harshen da ba nasa ba, a cikin harshen da zai sanya Bature ya dinga ci gaba da mulkin Afirkawa ko da kuwa bayan ya nade tabarmarsa ya bar nahiyar a tsawon shekaru. Wannan shi ne a halin yanzu ke faruwa a yawancin kasashen da ake yi wa lakabi da masu tasowa ko kuma wadanda ba su ci gaba ba, ba wai a nahiyar Afirka kadai ba, har da sassan duniya da makircin mulkin danniya da mallaka ya shiga cikinsu ya yi kaka-gida. Shi ya sa yau kasar Ingila da masu magana da rubutu da harshen Ingilishi a matsayin harshen uwa ba su wuce ka kwana ka kirge su ba, amma kuma masu magana da Ingilishi a duniya sun fi kowa yawa a doron kasa, shi ya sa ma ake wa harshen lakabi da harshen duniya, ko kuma harshen danniya! An fadi haka ne saboda sanin irin yadda tunani da Ingilishi da rubutu da Ingilishi yake nakasa kowace al’umma da ta ba wannan abu muhimmanci fiye da harshen uwa ko harshen gida. Ba yadda za a yi al’umma ta ginu ta kuma ci gaba ba tare da kare harshenta da kuma rubuce-rubucenta ba; duk irin yadda mutum zai yi ya ciyar da kasarsa gaba ta hanyar amfani da ilmi da ke cikin littafin da ba a harshensa yake ba, zai kasance cikin matsala da kuma kunci, domin zai zamanto mai yaki da tunani iri biyu, na baki da kuma nasa na gida, wannan na daga cikin abubuwan da suka cunkushe harkar ilminmu da kuma halin da ilmin yake ciki da kuma rubuce-rubucenmu a yau. Wannan abu da muke fama da shi yau, shi ne kuma Turawa suka yi fama da shi tsakaninsu da Larabci, a lokacin da Larabcin yake cikin ganiyarsa. Kusan duk wani ilmi na kimiyya ko fasaha ko kuma na ci gaban al’umma a Larabce yake kafin Turawa su gaje, su kuma mallake shi daga baya. A lura, ba don Turawa na so ba ne suka debi ilmin Larabcin suka yi amfani da shi, dole, kanwar na ki ce ta sa Turawa suka yi amfani da tunani da nakaltar Larabci don cin moriyar ilmin da ke kimshe a cikin littattafan Larabawa da ke mulkin duniya a wancan lokaci. Daga baya ne Turawa suka fahimci cewa ai yawancin ilmin da Larabawa ke takama da shi su ma sun kwaso wasu ne daga littattafan Girkawa, don haka suka yi watsi da na Larabawa suka koma wa na ainihin, wato Girkanci, ta haka ne mallakar da Larabawa suka yi wa duniya ta fuskar ilmi ta subuce ta koma ga Turawa, musamman na Ingila. Wannan ba wani abu ya nuna mana ba sai cewa gadon gida halal ne ga raggo. Ba ta yadda za a kai ga kololuwar ilmi da ci gaba ta amfani da bakon harshe, domin kuwa komai iya nakaltar harshen wasu da ka yi, ba za ka taba zama kamar su ba, kuma za ka kasance ne a kullum kana magana da bakin ne, ba mutanen cikin gida ba ko kuma ‘yan uwanka, domin kuwa kashi 7 cikin 10 na mutanenmu ba su san da wannan bakon harshen ba, idan kuwa haka ne, to mu da wa muke magana a rubuce-rubucenmu idan mun kimshe al’amarunn cikin harshen Ingilishi ko kuma mun jona tunanin bakuwar al’ada da adabi da addini a cikin rubuce-rubucenmu? Tambayar farko da zan soma da ita, ita ce, shin marubutan baya, wato kafin mu, haka suka yi? Yaya tasirin amfani da bakon harshe da al’ada da adabi wajen gina tunani da rayuwarmu zai kasance ga masu gudanar da wannan harka, musamman ga ci gaban al’ummarmu da kuma kasarmu? A tuna, su kan su Turawan mulkin mallaka sun san irin tazarar da Larabci ya yi wa sauran harsunan duniya ne, shi ya sa suka yi amfani da dabashiri kafin su durkusar da shi, su maye gurbinsa da nasu, shi ya sa duk inda suka sami kan su a matsayin masu mulkin mallaka, a Afirka ko Asiya ko Amurka ba su yi wasa da cusa tunaninsu da kuma akidojinsu ga al’ummomin da suka ci karo da su ba. Sun yi haka ne da sani, domin ta haka ne kurum za su iya yin zaman darshen a cikin harkokin kasashen da suke yi wa sukuwar salla a wancan lokaci. Shi ya sa tsarin ilmin nasu da littattafan da suka shigo da su domin horaswa, suka kasance cikin harshen ‘yan mallakar, a wasu wurare suka matsa sai a yi komi tamkar a Turai, a wasu wuraren kuwa a kaikaice, wasu kuma ba ka iya bambanta su da masu mulkarsu ta kowace irin fuska, dubi Amurkawa ka kwatanta su da mutanen Indiya ko Pakistan da kuma bakaken fatar Afirka, musamman a tsakanin inda Faransa ta yi turke da kuma inda Birtaniya ta kafa tata lemar. Ma’ana, wannan rarrabuwar ita ce ta taimaka wajen gane illar mulkin mallaka da kuma yadda aka rarraba kawuna domin a ji dadin mulki. Bisa wannan tafarki ne Leopord Senghor na Senegal ke nuna bakin cikinsa game da irin ilmin da ya samu ta hanyar Turawan Faransa, yana cewa, ‘a lokacin da nake fafutukar karatu a gida da waje, ‘yan uwana da na bari a gida ba su yi boko ba, sun kasance ‘yan kasa na gari, ni kuwa a kullum da na bar makarantar Firamare na shiga Sakandare, na wuce zuwa Jami’a, sai kara hannun riga na dinga yi da al’ummata da kuma kasata.’ Ya ci gaba cewa ‘a daidai lokacin da nake karatu, sai na kara sanin tarihi da yanayin kasashen Turai, ina kuma kara jahilcewa game da tarihin al’ummata da kuma kasata.’ Daga karshe ya ce ‘a lokacin da na dawo gida daga Faransa, sai na ga na kasance bako cikin jama’ata, tsararrakina da na bari ba su yi karatu ba, suka kasance malamaina.’ Wannan haka ya kasance dangane da yawancin marubuta da shugabanni a nahiyar Afirka, musamman wadanda suka kasance karkashin mulkin kasar Faransa. A bangare daya kuwa, wadanda suka zauna cikin inuwar mulkin Birtaniya ba haka abin ya kasance ba, ga wasu, kamar yadda Mista East ya bayyana game da Abubakar Imam a matsayinsa na marubuci, ya ce, ’Abubakar (Imam) ‘yana daya daga cikin ‘yan kalilan da ya kasance duk da cewa ya sami ilminsa ta hanyar horaswa cikin Ingilshi da littattafan Ingilishi, daga kuma Turawan Ingilishi, bai yi watsi da harshensa ba, domin kuwa yana bayyanar da tunaninsa cikin harshen nasa, ba cikin Ingilishi ba kamar yadda saura ke yi.’ Tambaya. Me ya bambanta Senghor da Imam? Ba wani abu da ya wuce cewa shi Imam bai yarda Ingilishi ya kasance masa harshen tunani ba, bai yarda bakin al’adu sun yi masa katutu, ba ma Ingilishi kadai ba, kusan duk wani bakon abu da ya ci karo da shi a lokacin da yake nadar ilmi da ya gina masa rayuwa bai cika amsar sa kai tsaye, sai ya yi bita da nakaltar irin tasirin da zai yi masa. Shi kuwa Senghor ya tashi ne cikin wani tsari da ya fifita tunani da al’adun Faranshi bisa na bakar fata, haka al’adu da addini da kuma tsarin ilmin baki daya. Bai sami damar bambance barcin makaho ba ko kuma duma daga kabewa, ba don komi ba kuwa saboda irin yadda aka rene su tun daga gida. Imam ya sami ilmin addini mai zurfi ko kafin ya hadu da Bature da makircin da ya shigo da shi, saboda haka bai yarda wani makiri ya yi masa wayon wanikiki ba, tun yana karami. Ko da ya shiga dakin ajiyar littatafai na makarantar Elemantare da Midil a Katsina domin ya yi nazari don shiga gasar rubuta littatafai da aka shirya a 1929 da kuma 1933, bai yarda ya yi amfani da duk abin da ya ci karo da shi ba, sai dai ya karanta, ya jinjina kamar mai sayen kaza, amma yana bukatar mai kwai. Haka kuma sai ya auna abin da abin da addininsa da kuma tadojinsa na kwarai suka aminta da su, sa’annan ya kattaba shi a cikin nasa aikin. Saboda haka muna iya cewa bai taba yarda da tasirin bakin al’adu ko addinai da ya yi nutso a cikin su, sun ja masa akala wajen yin rubutunsa ba. Haka su Tafawa Balewa da Ahmadu Bello da Aminu Kano da Sa’adu Zungur da Mu’azu Hadeja da Mudi Sipikin da Alkali Bello Gidadawa da Gambo Hawaja da Shekara Sa’ad da wasu da dama daga cikin marubutanmu na da suka yi, kuma wannan shi ya haifar da akidar nan ta goya wa talaka baya da nema masa mafita daga al’amurran da suka kasance suna sa masa kunci da dabaibaye shi ta fuskar siyasa da mulki da tattalin arziki da sauran al’amurran zamantakewa na yau da kullum. Bari mu yi bitar wasu daga cikin ayyukan daya daga cikin mashahuran marubutan kasar Hausa wato Abubakar Imam, domin mu gani ko za mu iya samun haske dangane da irin abubuwan da aka yi a da, da yadda suka yi tasiri har zuwa yau, kafin mu koma ga ainihin batun namu na yau, shin mu wa muke yi wa rubutu, don me muke yin rubutu, me kuma muke so rubutunmu ya yi a rayuwar da muke ciki! A cikin ayyukan da Abubakar ya yi na adabi ba daya da ya zauna ya shirya a cikin ransa da nufin ya nishadantar kurum ko kuma ya burge kawai ko kuma dai don a san da shi a cikin harkar rubutu ko kuma rayar da ilmi. Bai yi haka a lokacin rubuta littafin Ruwan Bagaja ba, duk da cewa a lokacin da ya yi rubutun yana da shekara 22 a doron kasa. Ko da ya shiga dakin ajiyar littattafai na makarantarsu domin ya sami samfur na irin yadda zai tsara labarin nasa, ya kuma ci karo da littafin The Water Of Cure na ‘yan uwa Grimms daga Jamus, ba haka nan ya bi shi ya kwashe komi da komi ba da ya ci karo da shi a cikin littafin, kamar yadda labaran suke a kasar Jamus, tun asalinsa ba, sai da ya bi ya nakalci labaran, ya yi musu kwaskwarima ya debe al’adun Jamusawu da suka yi hannun riga da na kasar Hausa, sa’annan ya maye gurbin wadanda ya karanto da na Hausawa. Saboda haka za a ga ya cire addinin Kiristanci, ya shigo da Musulunci, al’adun Jamusawa suka bada wuri domin na Hausawa. Da kuma ya shiga cikin littafin Alfu Lailah yai nutso da ninkaya ya debo hikayar Abdussamad da ‘yan uwansa, ita kuma ya kwashi wani gefe ne da ya dace da tunanin malam Bahaushe ya jefa a cikin littafin Ruwan Bagaja, ya yi watsi da tadar Larabawa da ya san cewa ba ta da wani alfanu ga mai karanta Hausa. Ba nan kadai ya tsaya ba, ya kuma shiga cikin gonar adabin baka na Hausa inda ya tsamo tatsuniyoyi da labaran Hausawa da suka yi tashe a wancan lokaci ya gina zubin littafin. Da kuma ya natsu sai ya nemo rayuwar Malam Zurke da Alhaji Imam daga rayuwa ta yau da kullum. Shi dai Zurke wani mahaukaci ne da aka yi a cikin birnin Katsina a lokacin da Imam ke karatu a can, Alhaji Imam kuwa ba kowa ba ne marubucin ne da kansa. Sunansa Imam, mahaifinsa sunansa Shehu, shi ya sa Himma dan Shehu ya zama lakabinsa. Sai dai ya dace a lura ko da ya je ga rayuwar yau da kullum domin neman gina malam Zurke da Alhaji Imam, amma kuma siffofin wadannan mutane a zahiri ya same su ne daga littafin Maqamatul Hariri, inda Harisu da Abu Zaid suka taka rawa irin ta Zurke da Alhaji Imam, sai dai su Harisu dabaru da wayon wanikiki da suka yi a cikin Maqama cike suke da al’adun Larabawa, dole ta sa Imam ya mayar da su na Hausawa, cikin ban dariya da sosa rai. Idan kuma muka dubi Magana Jan Ce (1-3) sai mu ga cewa nan Imam ya nuna gwanancewa fiye da a Ruwan Bagaja, ko ba komi a nan ya san da wa yake magana, ya kuma san dalilin yin rubutun da abin da yake son rubutun nasa ya yi ga wadanda aka yi wa rubutun. Tun da farko, nan ba gasa ba ce, an nemi a yi rubutu ne don yara ‘yan firamare, domin a samar musu abin karatu da kuma tarbiyya. Nan ma Imam sai da ya nemi samfur da zai gina nasa tunanin, amma kamar kullum sai da ya canza wa duk wani tubali da ya tsinto daga wasu wurare siffa ko kuma kama, don su dace da tada ko al’adun yara ‘yan kasar Hausa. Ya dai dubi tsarin Alfu Lailah, ya gina budewar Magana Jari Ce, ya kuma yi amfani da littafin The Parrot ya gina batun Aku mai magana, ya nemo labaran Andersen Fairy Tales na kasar Denmark da labaran Aesop Fables na Girkawa da labaran Grimms Fairy Tales na Jamusawa da labaran Shakespeare na Ingila da tatsuniyoyin Hausa masu tarin yawa domin su kasance masa ‘ya’yan da ke tafiya da uwar labarin Magana Jari Ce. Ya yi haka ne cikin tunanin masu karatunsa da neman shirya musu mafita da samar da tasiri na gari. Saboda haka duk inda ya hadu da maganar barayi sai ya yi huduba kan sata da rashin kyan sata, yana kuma bayyana cewa bai son bayar da labarin barayi ba don komi ba sai don gudun kada yara su sami abin kwaikwaya. Shi ya sa kuma duk inda ya kawo labarin barayi to bai barin barayi su yi nasara kan mutanen kwarai. Kai ba wannan kadai ba, duk inda aka yi mugun abu sai ya nuna horon da aka yi wa wanda ko wadanda suka yi mugun abun domin ya kasance darasi. Imam ya san darajar rubutu, ya kuma san illar rubutu, shi ya sa tun farkon shiga cikin wannan harka kamar yadda ya fada a cikin tarihinsa, ya shiga da zuciya daya. Ga abin da yake cewa a cikin littafin tarihinsa na rayuwa game da matsayin rubutu. Ya ce, East ya koya masa cewa ‘kada ka yarda ka bar mugu ya yi nasara a cikin gina labarinka, domin tasirin barin haka zai iya rusa al’umma.’ Wannan shi ne ke cikin zuciyar yawancin ayyukan adabin da Imam ya gina a cikin Magana Jari Ce. Misali, duk inda ya ji ana maganar itaciyar Yeuw (mai kwankwamai) sai ya mayar da ita itaciyar tsamiya. Gidan Turawa na ginin bene, ba zaure don baki da sa kwat da duk wasu abubuwan jin dadi na rayuwa, irin na Turawa, canza su ya yi da na Hausawa, bai yarda bakon malam Bahaushe ya shigo har cikin gida ba, domin masaukin bako ai zaure ne in ji Hausawa. Haka abinci da abin sha da abin hawa da sauran makamantan su, ba don komi ba sai don wadanda yake wa rubutun su karu da ilimin da ke ciki da kuma inganta kyawawan al’adu. Kila, wani ya ce a wancan zamani da su Imam suke raye ne ai ake yin hakan, yanzu fa, yaya al’adun Hausawa suke, yaya za a iya bambanta na ainihi da wanda yake bako? Abin nuni shi ne zamani ai riga ne, in Imam ya hana bako wucewa cikin gida sai dai zaure, za mu ga cewa ya yi daidai da zamaninsa, kila mu yanzu, bakon har cikin dakunan masu gida yake shiga, shi ma sai a bayyana dalilin yin haka, da zamani ya zo da shi, ba wai a turbude shi tamkar shi ne mafita ga al’umma ba. Shi ya sa a yawancin rubuce-rubucen marubutan kwarai za a ga ba su yarda mugu ya sha daga muguntarsa ba, ba su barin azzalumai su wuce da zaluncinsu, ba su barin kunci ya tabbata a cikin rayuwa. Duk yadda za su yi za su nuna wa masu karatu, kyau da rashin kyawun abu, irin wannan shi ya bi ya gina tunanin marubutan kwarai da adabi mai walwala. Wannan kuma shi ya sa, har yau har kwanan gobe ayyuka irin wadannan da marubutan suka rubuta da kewar mutanensu da tunanin mutanensu da neman inganta rayuwar mutanensu suke kasancewa kamar yau ne aka yi su duk da cewa sun yi shekara dari da dabbakawa. Darussan da ke cikin irin wadannan ayyukan adabi har yau suna da tasiri a rayuwar jama’ar yau din, ba wa sai na jiyan ba, za su kuma ci gaba da wanzuwa a haka har gobe da yardar Allah. Tambayar da kila wasu ke faman yi ya zuwa yanzu ina jin ba ta wuce to mu wa muke wa rubutu ba, don me mu muke yin rubutu? Muna yin rubutun ne don mu samu na cefane, wato mu sami abin da za mu ciyar da kanmu da iyalanmu? Ko kuwa muna yin rubutun ne don gwamnati ta san da mu ta ba mu kwangila ko lambar yabo? Ko kuwa muna yin rubutun ne don talakawa masu karantawa su sami abin nishadi ko kuwa don dai kawai rubutu maganin wani ciwo ne, idan ba mu yi shi ba, ba za mu samu saukin radadin ciwon ba? Kafin na bayar da wannan amsa, zan so in dan mazaya tukun, domin ta haka ne nake jin za mu sami haske game da irin rubutunmu da wadanda muke wa rubutun. Rubutu baiwa ce, Allah ke sa ilminsa in da ya so ga wanda ya so, yadda ya so a lokacin da ya so. Wasu kuma haye suke masa, su kuma kasance ‘yan gida a cikinsa, ta yadda duk abin da dan gado zai iya yi, su ma za su iya, kila ma har su fi ‘yan gida. Saboda haka kowace irin dama mutum ya samu ya zama marubuci, abin da ke da muhimmanci shi ne ya san tasirin irin rubutun da yake yi da kuma inganci ko akasin haka. Masana rubutu na yin kirari da cewa alkalami ko biro ko ma dai wane irin abin rubutu ya fi takobi kaifi a fagen juyin-juya-hali ko canjin lamurran rayuwa. Ke nan alkalami ko wani abin rubutu babban makami ne na sauya lamurran rayuwa, idan an yi amfani da shi yadda ya dace. Ke nan abin da ya dace mutum ya fara da shi a fagen rubutu shi ne sanin wadanda yake wa rubutu. Kai da ke karanta wannan bayani a yau, tambayi kanka wa kake yi wa rubutu? Hausawa ko Turawa ko Larabawa ko wasu baki? Idan Hausawa kake magana da su a rubutunka, to ya dace rubutun nan naka a cikin jarida ne ko mujalla kake yin sa ko kuma labari ne ko waka ko kuma wasan kwaikwayo ka gwanance kai, to ya kasance a cikin harshen da mutanenka za su gane, za su fahimta, za su kuma iya yin aiki da shi yake. Saboda haka kai da ke nan tare da mu wa kake wa rubutu? Mutumin Garun-Ali ko kuma Yorkshire ko Manchester Makka ko Madina ko Lahore ko ina? Kai da ke ta fafutukar rubuta waka ko rera ta. Kai da ke tsara da kuma rubuta da aiwatar da wasan kwaikwayo. Kai da ke ta faman zayyana labarai cikin fasaha kala-kala. Kai da ke ta faman rubutu cikin jarida ko mujalla ko Intanet da. Kai da ke faman sai ka wallafa littafi a kowace rana ta Allah, don me kake wannan hankoro, domin kedafare ko kuwa don a san ka a matsayin marubuci? Me ya sa kake rubutu? Wa kake wa rubutun? Wace ribar kake nema daga rubutu? Mu hadu a aji ranar Lahadi mai zuwa 23 ga watan Yuni, 2013 domin samun karin haske ko kuma mafita!

Bayanin Wasan Kwaikwayon Hausa A Takaice

BAYANIN WASAN KWAIKWAYO A HAUSA A TAKAICE MA'ANAR WASAN KWAIKWAYO A HAUSA Ba da an tsawaita bincike ba ana jin cewa ma’anar wasan kwaikwayo a Hausa a bayyane take daga lura da kalmomin da suka gina shi, wato abu ne mai alamun wasa da kuma kwaikwayo. Shi dai wasa na nufin duk abin da ba gaskiya ba, yana kuma dauke da raha da ban dariya da nishadi, akwai kuma kwaikwayo, wanda ke nuni da aikata wanin abu don kwatanta yadda yake, ko yadda ake yin sa, ko don a kyansa ko kuma muninsa. Abin la'akari a nan shi ne, za a ga cewa wasan kwaikwayo a Hausa ba kamar su daya da drama, a Ingilishi ba, domin su Turawa sun dauki drama ko wasan kwaikwayo a matsayin wata basira da za a shirya a rubuce ta fuskar zube ko waka, mai nuni da yadda rayuwa take gudana ko halayen wadansu, ta hanyar fadi-in-fada da alamtarwa, an kuma fi gudanar da shi a dandali. Duk da cewa akwai ‘yar tazara tsakanin wasan kwaikwayon Hausa da yadda yake a cikin Ingilishi, za a fahimci cewa abubuwan nan da Hausawa suka fi mayar da hankali a kai wajen gane wannan abu, suna nan rakube a cikin dukkan wani wasa mai kama da haka a kowane harshe ko al'ada ta duniya. Yaya wasa yake a cikin wasan kwaikwayo, shi kuma kwaikwayo yaya ya kasance? Duk irin wasan kwaikwayo na gargajiya da ka yi nazarin kayan cikinsa za ka ga alamun nan biyu na wasa da kwaikwayo a cikinsa. Misali: Wasan langa Wasan ‘yar tsana Wasan kalankuwa Ko Wasan Marafa (a rubuce) Dangane da haka duk wani tsarin wasa da aka sa gaba idan bai da wadannan siffofi to ba wasan kwaikwayo ba ne. Haka kuma dole ya kasance da wadannan kamannu. 1) Sake kama ko canza tufafi ko murya. 2) A sami wani wuri na musamman (wato dandali ko dandamali) 3) Ya kasance yana dauke da wani sako 4) Dole a sami tanka-in-tanka BAMBANCIN WASA DA WASAN KWAIKWAYO Wasan Kwaikwayo Wasa Koya darussa Nishadi da jin dadi Akwai kwaikwayo Ba kwaikwayo Canza kamanni Ba canzawa A dandali don a gani Ba dole don a gani ba Ba daukar lokaci mai tsawo Ana daukar lokaci mai tsawo Akwai lokutan gabatar da shi Ba wani lokaci tsayayye Wannan ya nuna cewa, ta hanyar kwaikwayo ne dan Adam yake koyon magana da kuma dabarun sarrafa harshe, hakan kuma ta kwaikwayo ne yake koyon yadda ake sarrafa abubuwan da ke kusa da shi, ta hanyar samar da muhalli, tufafi, makamai da sauran su. Kuma ta kwaikwayo ne dan Adam yake koyon sana’a kamar noma, farauta, kira da sauran su. Ke nan wasan kwaikwayo dadaddiyar al’ada ce a cikin rayuwar Hausawa, saboda haka ana kallon sa ta hanyoyi da dama. A ra’ayin wani masani Ibrahim Yaro Yahaya, ya ce “a al’adance ko a gargajiyance wasan kwaikwayo na nufin dukkan abubuwan nishadi da ban dariya, da tsokana da annashuwa, da kuma motsa jiki, da akan yi a wurare daban-daban, musamman a wuraren bukukuwa, da bakin kasuwa, domin a nishadantar ko kuma a fadakar da al’umma”. Haka kuma a wani hadin gwiwa a tsakanin masana biyu, a nasu ra’ayi, watau Abdulkadir Dangambo da Ibrahim Yaro Yahaya sun ce “wasan kwaikwayo wasa ne inda akan aiwatar da wata matsala ta rayuwa cikin siffar yakini ko kuma a rubuta shi”. Haka Abdulkadir Dangambo ya ce “wasan kwaikwayo kamar yadda sunansa ya nuna, wasan ne da ake gina kan kwaikwayon wani labari ko wata matsala ta rayuwa da ake son nuna wa ga jama’a”. Shi kuwa Tanimu ‘Yar ‘aduwa ya bayar da ma’anar wasan kwaikwayo kamar haka, “wasan kwaikwayo kamance ne na wasu halaye ko yanayin rayuwa, wadda masu hikima sukan shirya su gabatar da shi ta hanyar annushuwa da raha da nishadi don cimma wata manufa”. A wani aiki da su Sadiya Omar Bello suka yi wa edita, sun ce “wasan kwaikwayo wani tsararren abu ne wanda ake kwatanta wata rayuwa ta wani yanayi don bayyana wa mutane ta hanyar wasa”. Har wa yau Atiku Dunfawa ya ce “wasan kwaikwayo shi ne duk abin da aka tsara kwaikwayonsa don nuna cewa jama’a su gani, kuma shi wannan abin da za a nuna yana iya kasancewa ya taba faruwa, yana kuma kasancewa bai taba faruwa ba, sai dai an zauna ne an kago shi da kwakwalwa don nuna wa jama’a”. Bugu da kari, za mu iya fahimtar cewa wasan kwaikwayo ba abu ne na gaskiya ba, kirkirarsa ake yi, don haka idan muka dauki wadannan kalmomi guda biyu, wasa da kuma kalmar kwaikwayo za su tabbatar mana da cewa, wasa dai wani abu ne da Hausawa ke nufin duk wani abu da aka gabatar wanda ba gaskiya ba ne, sannan kuma kowa ya amince ana yin sa ne domin samar da raha, da ban dariya, ba don cin mutunci ko cin zarafin wani ko wata kungiya ba. Shi kuma kwaikwayo na nufin aikata wani abu ta hanyar canza kama, ko murya, ko jiki, ko siffa, ko muhallin yin aikin, da nufin nuna kwaikwayo ko nunin abin da ake so juya. A bisa wadannan bayanai za mu iya fahimtar wasan kwaikwayo yana da siffofi biyu a al’adar al’ummar Hausawa. Da farko dai akwai wasu al’adu masu tsari irin na wasan kwaikwayo. Na biyu kuma, akwai wasan kwaikwayo irin wanda muka sani ana shiryawa, ana gudanarwa a dandamali, ko a gidan rediyo da talbijin. TAKAITACCEN TARIHIN WASAN KWAIKWAYO A HAUSA Shi dai wasa irin na nishadi ko na kwaikwayo ko kuma na motsa jiki dadaddiyar al'ada ce a kasar Hausa kamar yadda muka yi bayani a baya, musamman ganin cewa ya girmi rubutacce,. Ke nan dole ne a amince cewa tun fil azal akwai wasan kwaikwayo a rayuwar kowace al'umma kafin zuwan rubutu. Saboda haka idan aka koma kan batun tarihin wasan kwaikwayo a kowace al'umma ya dace ne a koma ga al'adu da adabin gargajiya domin ganin ko akwai masu kamannu da irin wannan abu, a nan abin da ke da muhimmanci ba yanayin da ake sami abin ba, wato a rubuce ko a ka, irin amfanin wannan abu a tsakanin jama'a. Haka kuma ba maganar rana ko wata ake yi ba, a’a, lokacin da ake jin cewa ya samu ginuwa a tsakanin al’ummar. Saboda haka a takaicce za mu iya cewa wasan kwaikwayo ya samo asali ne tun farkon ginuwar al'ummar Hausawa. Ita wannan al’umma tana tafiya ne da al’adunta na gargajiya da suka hada da wasannin gargajiya da sauran wasanni. Saboda haka za mu iya karkasa wasannin zuwa gida-gida kamar haka: • Wasannin gargajiya na wasa kurum: Wasan kura ko na maciji ko na kunama. • Wasannin sana'a da suka hada da wasan gardawa (hawan kaho) da na ‘yan tauri (wasan tauri) da na ‘yan kama da na ‘yan dabo. • Wasannin dandali ko wasannin yara da suka hada da A sha ruwan tsuntsaye da Dan akuyana da na ‘Yar tsana. • Wasannin bukukuwan al'ada da suka kunshi wasan Giwa sha laka da Bikin budin daji da na Kallankuwa da wasan bori. Sai dai kafin mu shiga cikin takaitaccen bayani kan tarihin wasan kwaikwayon Hausa bari mu dubi asalinsa da alakarsa da sauran na sassan duniya. Kusan duk an yarda cewa wasan kwaikwayo shi ne ginshikin hanyoyin da dan Adam ke bi yana koyon yadda zai rayu. Watakila, ke nan za a iya danganta asalin wasan kwaikwayo da farkon bayyanar dan Adam a doron kasa. Akwai ra’ayoyi da dama game da asalin samuwar wasan kwaikwayo, akwai masu ra’ayin addini shi ne asalin wasan kwaikwayo. Masu wannan ra’ayi suna ganin cewa wasan kwaikwayo ya samo asali ne ta hanyar bautar gumaka da kabilun Girkawa ke yi a wani biki wanda ya dimanci addininsu. Suna gudanar da wannan bauta a wani kayyadajjen lokaci na shekara. Kuma wannan biki a gaban ‘yan kallo ake gudanar da shi. Haka kuma akwai wani ra’ayi mai nuna cewa a Gabas ta tsakiya da kuma kasar Indiya har ma da wasu sassa na Afirka mutanen sukan yi wani abu mai kama da wasan kwaikwayo musamman a lokacin da suke yin ta’azziyar bikin mutuwar muhimmin mutum don nuna girmamawa a gare shi. Saboda haka wasan kwaikwayo na nishadi, ko wanda ake yi don motsa jiki, ko na addini abu ne wanda ya samo asali da dadewa a kasar Hausa. Wasan kwaikwayo ya samu ne tun wanzuwar al’ummar Hausawa. Kuma muna hangen cewa abubuwan gargajiya sun girmi na zamani ko wadanda ake rubutawa. Abin nufi a nan shi ne wasan kwaikwayo ya samu ne ga al’ummar Hausawa tun kafin wanzuwar ilmin zamani na karatu da rubutu. Da dadewa akwai wasu al’adu da yara ko samari suke gabatarwa ta hanyar kwaikwayo a tsakaninsu, shekaru aru-aru kafin al’ummar Hausawa su fara hulda da cudanya da wasu al’umman da ba su ba, wato na ketare. Daga cikin irin wadannan al’adu na Hausawa akwai: wasan langa; a cikin wannan wasa yara za su kwaikwayi yadda ake yaki. A nan yara za su kasu gida biyu ne wannan langon da wannan, kuma kowane gida yana kokarin ture langon dan uwansa ko abokin wasansa. Kuma su wadannan gidaje biyu suna daukar kansu a matsayin abokan gaba na garuruwa guda biyu. Sannan kowane gari yana karkashin sarkinsa. Da ganin wasan kansa yaran na kwaikwayon dabi’ar yaki ne a cikin wasa. Bayan wannan akwai bikin ‘yartsana: galibi yara ‘yan mata su ne suke yin wannan wasan. Wasa ne wanda idan yarinya ta mallaki ‘yartsana, sai ta rinka yi mata raino irin na gaske, ta rika kwaikwayon ciyar da ita, tana yi mata wanka, idan ta girma ta yi mata kunshi, ta yi mata ado na tufafi da sauransu har ta kai fagen yi mata aure da sauran hidimomi. A irin wannan wasa ‘yanmata na kokarin su kwaikwayi yadda ake renon mutum tun yana karami har ya girma, har a yi masa aure a cikin wasa. Babu ko tantama tunda aka sami wasa da kuma kwaikwayo, to ya zamo wasan kwaikwayo ke nan. Bayan wannan hasali ma manya da kansu baya ga irin wadannan wasannin gargajiya na yara, akwai wadansu al’adu da sukan yi masu siffar wasan kwaikwayo. A cikin irin wadannan al’adu, akwai: Bori: wannan wata al’ada ce a kasar Hausa wadda Hausawa kan yi don neman kubuta daga wata cuta da ta kama mutum tana wahalar da shi. Idan ana neman waraka daga wannan cuta mai rikitarwa, to wani lokaci a ce sai an yi wa mutum mai irin wannan cuta girka kafin ya sami waraka. To sai ‘yan bori su taru ana yi musu kida da goge, ko garaya, ko molo, ko duma, ko dundufa. Su ko sai su hau bori suna tuma suna faduwa. Ta wannan haujin sukan kwaikwayi iskokin da ke tare da su ta hanyar jirkita magana da siffofinsu. Haka kuma akwai wasan kallankuwa: Kallankuwa wani wasa ne da samari da ‘yanmata kan shirya suna kwaikwayon aikin mulki da gudanar da shari’a a karkara da kuma yanayin zamantakewa a cikin kaka. Akan gabatar da irin wannan wasan a gaban manyan gari da sauran mutanen gari a matsayin masu kallo. Kuma akan tanadi wuri na musamman don gudanar da wannan wasa, kuma a cikin wannan wasa akan kwaikwayi wasu halayya da dabi’un mutane. Kuma masana na hangen cewa tun a wajen sana’ar Bahaushe ta farko, watau farauta akwai birbishin wasan kwaikwayo a ciki. Wannan yana da alaka da irin abubuwan da suke faruwa can daji idan an je wurin farauta. Domin wani lokaci akan sami ‘yan farauta da irin su Bikin budin daji ko Shan kabewa da sauran su. Kamar yadda tarihi ke maimaita kansa, wasan kwaikwayo ya samu ginuwa a tsakanin al’ummar Hausawa tun azal. Wannan shi ne ya sa aka rarraba shi zuwa gida uku kamar haka: Na daya akwai wasannin gargajiya na Hausa. Na biyu wasannin dandali watau wanda samari maza da ‘yan mata ke yi. Na uku, wannan ya kunshi bukukuwa . ZUWAN LARABAWA DA MATSAYIN WASAN KWAIKWAYON HAUSA Larabawa dai sun shigo kasar Hausa ta hanyoyi mabambanta, da farko dai a lokacin shigo da addinin Musulunci wanda aka ce ya samu karbuwa tun nwajajen karni na 8 zuwa na 9, daga baya kuma ta hannun masu cinikin bayi da saye da sayarwa addinin Musulunci ya zaunu sosai a kasar Hausa. Daga tsakanin karni na 13 zuwa na 15 kuwa addinin Musulunci ya warwatsu zuwa garuruwa da kauyukan kasar Hausa, ta yadda kusan kowane sashe na kasar Hausa ana gudanar da addinin Musulunci. Wannan ya sanya ilmin addinin Musulunci da makarantun allo suka wanzu a kusan ko’ina a fadin kasar Hausa. Wannan ne ya sa al’ummar yankin suka nakalci harshen Larabci ta yadda har suka iya rubutu da shi, suka samar da hanyar rubutu ta ajami. Saboda haka har zuwa lokacin da aka jaddada addinin Musulunci a kasar Hausa a karni na 19, za a ga cewa yawancin Hausawa sun iya karatu da rubutu cikin Larabci da ajami ta yadda aka samar da rubutaccen adabin Hausawa ta wadannan hanyoyin rubutu. Yawancin ayyukan adabin da aka samar sun fi a fagen waka da kuma zube. Ke nan wannan ya nuna mana cewa ba a samar da wasan kwaikwayon Hausa a rubuce a cikin Larabi ko kuma ajami ba. Kila tambayar da wani ka iya yi ita ce me ya sa wasan kwaikwayo a rubuce a zamanin zuwan Larabawa ko cikin rubutun ajami bai samu tagomashi ba? a) Ajami ya zo ne da addini, addini ba wasa ne ba, sai aka dinga wa'azi da amfani da waka, b) Su kan su Larabawa wasan kwaikwayo bai je gare su ba sai a karni na 18, wanda a lokacin addinin Musulunci da Larabci da ajami sun dade da ginuwa a kasar Hausa. c) Addinin musulunci ya hana al'adu na wasannin banza da labaru na karya da wake-wake na hululu. d) Lokutan koyar da karatu a makarantun allo ba a da wani wuri na koyar da wasan ko yin wasan. Bayan zuwan ajami da Larabawa suka kawo, sai zuwan masu jihadi, su ma ba su bada karfi wajen rubuta wasan kwaikwayo ba. Saboda suna ganin rubutun ajami, rubutun addinin Musulunci ne, babu wasa a cikinsa. Amma an sami wani mawallafi a dab da zuwan Turawa kasar Hausa a 1902, mai suna malam Muhammadu Ajingi, wanda ya yi rubutu a kan tafiye-tafiyensa a tsakanin kasar Hausa da kuma Afirka ta Arewa kasashen Larabawa, wanda suka kama da wasan kwaikwayo a rubuce, kamar yadda U.B Ahmed ya bayyana ya samar da wasannin Turbar Turabulus da Turbar Kudus da ‘Yan matan Gaya . ZUWAN TURAWA DA SAMUWAR WASAN KWAIKWAYON HAUSA Ko da da turawa suka zo sun yi kokari ne su mayar da wasannin gargajiya da na kwaikwayo su kasance na zamani wato a rubuce. Wannan ne ya sanya wasan kwaikwayo zamani ya kasu kashi biyu. Akwai rubutaccen wasan kwaikwayo na zamani. wanda aka rubuta kurum ba a dab'a ba da wanda aka rubuta aka buga ko aka yi wa dab'i. Kamar yadda muka yi bayani a can baya kafin zuwan Turawa dukkan wasan Hausa na gargajiya ne ba a kuma rubuta su ba ko da ajami, Da yake a can Turai al'adar rubutu ta dade, sun koyi dabbakar da ita a rayuwarsu ba abin mamaki ba ne da suke mamaye kasar Hausa suka assasa wannan al'ada, sai dai ba kai tsaye ne aka samar da rubutaccen wasan kwaikwayon Hausa irin na Turawa ba. A lokacin da Turawa suka kafa hukumar fassara a 1929 aikin wannan hukuma ya hada da samar da littattafai don karantawa, bisa wannan tsari ne shugaban hukumar Dr. R. M. East da malam Abubakar Imam da masinjar hukumar malam Basankare suka tsara wasan kwaikwayo na farko da Hausa a shekarar 1936, wanda suka sa wa suna Six Hausa Plays (Wasannin Hausa guda shida). Daga cikin dalilan da ya sa aka soma wannan al'ada bai wuce neman nuna wa jama'a yadda ake tsara wasannin kwaikwayo a rubuce ba, musamman ta hanyar canza tatsuniyoyi da tarihi da tarihihin kasar Hausa zuwa wasannin kwaikwayo. Ganin wannan littafi ya amsu, yara kuma suna karantawa ga kuma lokutta da aka ajiye a azuzuwa domin yin wasannin da kuma shirya wasannin kwaikwayo, sai wannan al'ada ta shige rayuwar jama'a, daga wannan lokaci yara da malammai suka shiga rubuta da aiwatar wasannin kwaikwayo a makarantu da lokutan karatu da bukukuwa Daga cikin daliban farko da suka rubuta wasannin kwaikwayo aka gabatar sun hada da irin su malam Aminu Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule, Alhaji Abubakar Dogondaji da Alhaji Abubakar Tunau Mafara, Wasu kamar na malam Aminu Kano Kai Wanene a Kasuwar Kano? Da Gudumar dukan en-en Kano, ba buga su ba, sai littafin Alhaji Abubakar Tunau Mafara, Wasan Mafara (1949) da na Alhaji Abubakar Dogon Daji, malam Inkuntum, (1953), wadanda aka buga daga baya. Daga wannan lokacin aka shiga cin kasuwar rubutun wasan kwaikwayo, aka kuma ci gaba da samar da su daga madaba'u daban-daban har zuwa yau da ake da wasannin kwaikwayon Hausa a rubuce masu tarin yawa: Marubuci Littafi Shekara Madaba’a 1. R.M. East Six Hausa Plays 1936 Lagos 2. A.A. Tunau Wasan marafa 1949 Gaskiya, Zaria 3. A.A. Dogondaji Malam Inkuntum 1954 Norla, Zaria 4. A.S. Makarfi Zamanin Nan Namu 1959 Gaskiya, Zaria 5. A.S. Makarfi Jatau Na Kyallu 1964 Gaskiya, Zaria 6. A. Muhd Sada Uwar Gulma 1971 NNPC, Zaria 7. A. Dangoggo da Dauda Kano Tabarma Kunya 1971 NNPC, Zaria 8. Umar Dembo Wasannin Yara 1971 NNPC, Zaria 9. I.Y. Yahaya Daren sha Biyu (Fassara) 1971 NNPC, Zaria 10. Umaru B. Ahmed Bora da Mowa 1972 NNPC, Zaria 11. Bello Muh’d Malam Muhamman 1974 NNPC, Zaria 12. Bashari F. Roukbah Matar Mutum Kabarinsa 1974 NNPC, Zaria 13. Umaru Ladan da Dexter Lyndersy Shaihu Umar(Daga Kagaggen Labari) 1975 NNPC, Zaria 14. Ahmed Sabir Mutanen Kogo (Fassara) 1976 NNPC, Zaria 15. Hasan U Kome Nisan Jifa 1978 NNPC 16. Katsina U. D Kulba Na barna 1979 NNPC 17. Ladan U Zaman Duniya Iyawa Ne 1980 NNPC 18. Idris D Matsolon Attajiri (Fassara) 1981 NNPC 19. Alkanci H Soyayya Ta Fi Kudi 1982 NNPC 20. Ahmed U.B Amina Sarauniyar Zazzau 1984 NNPC 21. Katsina U.D Ai Ga Irin ta Nan 1986 NNPC 22. Yaro A.K Bar Ni da Mugu 1986 NNPC 23. Maigari G. I Mugunta Guzurin Wuya 1986 NNPC 24. Sorondinki A. Gani Ga wane 1990 NNPC 25. Mahmoud Barau Bambale Kukan Kurciya... 1994 NNPC Baya ga wadannan kuma an samar da kungiyoyin wasan kwaikwayo masu yawa a makarantu da hukumomin al'adu na gwamnati da kungiyoyin taimakon kai, ta haka ake ci gaba da raya da gudanar da wasannin kwaikwayo a rubuce da kuma a aikace ire-iren wadannan kungiyoyi suna da tsari irin na shugabanci, sun kuma rubuta wasanni suna aiwatarwa daga lokaci zuwa lokaci, wasu da taimakon hukumomin al’adu na jiha da na tarayya, wasu don kashin kan su. Ire-Iren Wasan Kwaikwayon Hausa Game da irin fadin da ma’anar wasan kwaikwayo ke da shi, za mu iya cewa akwai al’adu da dama wadanda ke da dangantaka da wasan kwaikwayo tun kafin a fara rubuta littattafan wasan kwaikwayo cikin Hausa. Wadannan al’adu akwai wadanda yara samari ko ‘yanmata ke kwaikwayo a tsakanin su. Wasan Yara Maza da Mata Langa: A irin wannan wasan yara maza su ke kasuwa gida biyu, kuma kowane gida yana kokarin ture lagon dan uwansa. Watau a nan yara sukan kwaikwayi yadda ake yaki ne. Don haka wadannan kungiyoyi guda biyu suna daukar kansu garuruwa ne masu gaba da juna suka zo filin daga na yaki. Kuma kowane gari yana karkashin sarkinsa mai suna ruwa da kuma barden yakin sarki wanda ake kira ko aka lakabawa suna dokin ruwa. Kuma duk kungiyar da ta bari aka ture lagonsu to an fi su karfi kuma an cinye su da yaki ke nan. Dan akuyana: A irin wannan wasa yara maza kan yi da’ira ne rirrike da hannun junansu, ma’ana suna zagaye fili ke nan. A cikin da’irar za a sami yaro daya wanda aka ritsa da shi a ciki. Wannan wasan yana siffanta da’irar da rumbun hatsi ne, shi kuma yaron da aka ritsa da shi ciki dan akuya ne wanda ya riga ya yi barnar hatsi. Kuma wannan yaro da aka rutsa yana son ya fita kuma ga shi ko’ina an gewaye shi, don gewayen matsayin rumbu shi ke, don haka idan yana son fita sai ya yi wani babban yunkuri ko kuwa ya sha duka. Wasan ‘Yar Tsana: Yara ‘yanmata zalla su ne suke yin wannan wasan. Yarinya takan mallaki ‘yartsana sai ta rinka yi mata reno irin yarinya ta gaske, ta rika yi mata wanka da kwaikwayon ciyar da ita. Har yarinya ta girma. Idan ta girma ta yi ma ta kunshi da ado da tufafi wanda teloli suka dinka da kyallaye. Daga haka har yarinya ta kai fagen aure, sai ta raba goro ga kawayenta, ta gaya musu ranar biki. Sai ta tanadi kananan kwanuka da tasoshi, har ma da gado, da matasan kai. Su kuwa kawayenta su zo ranar kamu, su siffanta duk abubuwan da manya suke yi na bukukuwan aure tun daga ranar kamu har ya zuwa kunshi da kuma tarewa zuwa gidan miji. Kawaye kan kawo nasu tallafi ko gudummuwa ga uwar diya. Hasali ma sukan bi duk wani tsarin bikin aure su siffanta shi a cikin bikin auren ‘yartsana. Wasannin Tashe Wadannan wasanni yara suke shirya su dai-dai a cikin watan azumi bayan shan ruwa da daddare su rinka bi gida-gida suna wasa manya na kallo suna nishadi da raha. Misalin irin wadannan wasanni su ne masu siffanta irin wadansu halaye na tausayi, kamar su: Tsoho da gemu: Kungiyar masu tashe sai su yi wa waninsu ado irin na tsofaffi a cikin tsohuwar riga, rawani, gemun kada, sanda da carbi. Su bi shi suna cewa wannan tsoho ga shi nan da gemunsa, ba shi da karfin ciyar da kansa, saboda sai an tallafe shi da abin da zai ci. Shi kuwa ya dinga wani yakunewa yana ‘yan tari da mamular baki kamar na marar hakora, yana yi yana jan carbi, masu kallo suna dariya. Jatau Mai Magani: A nan yara masu tashe suna siffanta ko nunin yadda boka yakan lakanci magunguna. Bokan shi ne ake kira Jatau. Yara samari kamar hudu ko fiye da hakan suke raka dan uwansu zuwa gida-gida yana nuna tsirrai, saiwowi da kunshe-kunshen magani, da layu da guntayen fatu da kasusuwa. Yana nuna wa mutane wadannan daya bayan daya yana kuma fadin sunayen su da irin maganin da suke yi. Mairama da Daudu: ‘Yan mata suke da wannan wasa. Yara ‘yan mata kamar shida ko fiye, suna biye da yarinyar da suka yi wa lullubi (amarya, Mairama) da kuma wadda suka sanyawa kayan maza (ango, Daudu) suna bin su da kayan daki kamar su kwanuka da tabarmi da kujeru. Su kuma ‘yanmatan duk sun ci ado irin na ‘yan biki. Idan sun shiga gida sai su yi wa Daudu shimfida can waje daya, su sa Maryama tana daukar abinci tana kai masa, tana mai nuna yadda ya kamata mace ta yi wa mijinta, kamar murmushi, ladabi da sauransu. Kuma duk jama’a gida sun taru suna kallo ana raha. Bayan irin wadannan wasannin gargajiya na yara ’yan mata da samari, akwai kuma wadansu al’adu na manya da sukan yi masu siffar wasan kwaikwayo. A cikin irin wadannan al’adu na gargajiya akwai: Bori: Hanyar addinin gargajiya ce na Hausawa tun asali. Hausawa kan yi amfani da Bori don neman biyan buka ta ko kubuta daga wata cuta. Idan muka dauki hawan bori da kuma irin yanke-yanken da ake yi wa iskoki don neman waraka daga wata cuta wadda ta shige wa mutane duhu. Irin wannan biki na bori da kuma girka za a iya kwatanta shi da bikin addinin Girkawa na bauta wa wadansu irin gumaka, wanda sukan yi lokaci-lokaci na shekara, kamar lokacin hunturu da kuma lokacin bazara. Kuma wannan al’ada ta Girkawa (Greeks) tsohuwar al’ada ce kwarai, don ana ganin wannan ya fara ne a wajan karni na 5 (biyar) watau kafin haihuwar Annabi Isah (ma’ana sama da shekara dubu biyu). Idan aka dubi cikin Encyclopaedia Britanica, a littafi na 15 (sha biyar) kuma a shafi na 983 (dari tara da tamanin da uku) an nuna cewa buduri da ake yi na wannan bautar gumaka a gaban ‘yan kallo shi ne ya haifi asalin wasan kwaikwayo rubutacce na kasar Italiya wanda daga gare shi ne kasashen Turai suka gaji wasan kwaikwayo. Shi kuma Bori irin na kasashen Hausa, wanda ake neman magani ko kubuta daga wata riga ta karuma mutum, musamman na wata cuta mai rikidarwa akan shirya wa majinyacin girka, a yi gagarumin biki, boka da sauran ‘yan bori ‘yan uwansa suna hawa iskoki daban-daban ana kada masu garaya ko goge ko molo. A al’adar girka kowace irin iska da nata irin kida, su kuma da irin magana ko karar da za su yi, mai nuna kwaikwayon irin iskar da ta ke kansu a daidai wannan lokaci. A irin wadannan iskoki akwai kuturu, malam Alhaji, da doguwa, da Halima ‘yar buzaye, danko da kuma sarkin rafi da dai sauransu. Misali idan dan bori ya hau iskar kuturu, sai ya dinga karaji irin na kutare, ya kadandame yatsu kamar kuturu. Irin kidan da ake yi wa masu iskoki yana da tasiri kan fitar da hankalinsu ke yi, suna tumami, suna tsalle, suna karaji, suna faduwa warwas a kasa kumfa na fita daga bakinsu su sandare. A lokacin da suka kai ga hakan to sun fita a matsayinsu na mutane sun zama iskar da take kansu. Dabo-Dabo: Wannan wasa ne na nunin mutum-mutumi. Mutane kimanin hudu ne suke yawo tare da makada ganga biyu suna nuna dabo. A kan yi nunin irin wannan wasa a bakin kasuwa ko wurin taron mutane, su shaci fili su kafa sanduna hudu. Tsakanin kowace sanda akwai fadin kimanin kafa biyar kuma tsawon kowace sanda kimanin kafa biyu da rabi, sai su kawo babbar riga su kifa ta kan wannan tsaikon ta rufe shi sosai ya yi kamar dan daki da kofar rigar a sama. Sai mai nunin dabon ya shiga cikin tsaikon an kewaye shi masu kida na yi, ga masu kallo suna kallo, kowa ya kagara ya ga abin da zai nuna. Lokacin da ya shiga sai ya dinga fito da wadansu ‘yan mutane kamar ‘yan mutum-mutumi sai ka ji suna magana. Wani lokaci ya nuno saurayi da budurwa suna zance, ko ya nuno mutum wanda wani malami ya yaudara ya sa shi yin rawa. Da ya farga da cewa yaudarar shi aka yi, sai ya kai kara wajan alkali wanda zai yanke musu hukunci, ko kuma wannan mai nuni ya nuno ‘yan dambe za su kara. Kalankuwa: Wasan kalankuwa, wasa ne da samari da ‘yan mata kan shirya suna kwaikwayon aikin mulki da shari’a a karkara cikin kaka, bayan an girbe abinci da sauran amfanin kaka an mai suwa gida. Dagacin gari shi ne kan nada sarkin Samari, shi kuma sarkin samari shi ne zai nada mataimakansa kamar su galadima, madaki, waziri, alkali, gwamna da sauran su. ‘Yan mata su suke zabin sarauniya a tsakaninsu. Sai a zabi fili a kofar fada ko bakin kasuwa, ko wani fili. Sai sarkin samari ya zo ya kafa fadarsa, can waje guda kuwa ga makada, ana kida taken sarkin samari da na mataimakansa, ana he, ana ba su kudi. A cikin filin idan wani saurayi ya bata da wani abokinsa ko budurwarsa, sai a kai su gaban sarkin samari wanda zai bi diddigin laifin. Idan ya ga abin sai an hada da shari’a, sai ya aika da su gaban alkali don yanke hukunci. Ana daukar kimanin kwana hudu ana yin wannan bikin kalankuwa na yammacin kowace rana. A cikin kwanaki hudu na kalankuwa dagacin gari kan nemi sarkin samari da su yi wani aikin gayya, kuma akan hukunta duk wanda ya ki yin aikin a lokacin wannan bikin. Sauran misalai: Akwai sauran misalai da dama na al’adun Hausawa masu kama da wasan kwaikwayon Hausa. Misali, ‘yankama da ‘yan gambara sukan kwaikwayi halaye da dabi’u na mutane daban-daban a cikin wasansu don ban dariya. Wawan sarki shi ma yakan kwatanta siffofin abubuwa daban-daban wajen sa sarki raha. ‘Yan hoto kuma su ne masu bi wuri-wuri suna nuna gwanintar sarrafa garma ana yi musu kidan manoma, da dai kama-kaman irin wadannan al’adu da dama na Hausawa. WASANNIN KWAIKWAYO NA MAJIGI DA REDIYO Ci gaban da aka samu dangane da rubuta wasan kwaikwayon Hausa ana kuma aiwatarwa a makarantu da dandali shi ya sa ko da abubuwan zamani irin su majigi da rediyo suka kutso kai a kasar Hausa sai aka sami damar mayar da yawancin wasannin kwaikwayon Hausa zuwa a aikace ko dai a saurara a rediyo ko a gani ta dodon bango, wato majigi. Shi dai majigi shi ne ya fara kutso kai, tun daga shekarun 1950, an kuma zo da shh ne domin yin farfaganda da wayar da kan mutane domin su amince da al’amurran da suka shafi mulkin mallaka, musamman wajen noma da kiwon lafiya. Yawancin shirin wasannin kwaikwayon ana yin su ne don jama’a su ga fa’idar noman kudi ba na ci ba. Alal misali noman audugu da gyada da kuma amfani da takin zamani. Ana gabatar da majigi ne a kofar fadar Sarko ko bakin kasuwa ko filin kwallo ko wani wuri makamancin haka. Su kuwa gidajen rediyo sun zama ruwan dare daga shekarar 1960 sukan tanadi ‘yan wasa masu zuwa su aiwatar da wasannin domin jin dadin jama'a masu saurare, wata sa'a kuma ire-iren wadannan kungiyoyin gama-kai sukan je da nasu wasan don a ba su dama su gudanar, ta haka sai wasannin kwaikwayo suka kara samun martaba da daukaka a idon jama'a, yau a yi wannan sabon shiri da sunan sa daban, gobe wani ya fito, amma jama'a ba sa mantawa da su. Wasannin Gidan Rediyo Irin wadannan wasanni jin su kawai ake yi amma ba a ganin masu aiwatarwa. Watau suna irin wadannan wasanni tsara su ake yi a rubuta a kuma kwatanta su a cikin akwatin rediyo ta hanyar daukar sauti. Misalin irin wadannan wasanni: ‘Yau da Gobe na gidan rediyon Rima, da ke Sakkwato, da Samanja Mazan Fama, da Duniya Budurwar wawa na gidan rediyon tarayya na Kaduna, da kuma ‘Taskira Asirin Mai Daki’ da Bakandamiya na rediyon jahar Katsina. Akwai kuma wasan ‘Duman Kada... na Rima rediyo Sakkwato da sauransu. Su irin wadannan wasanni akan ba su wani suna ne, amma kuma idan wannan wasa ya yi yayi ya gama akan jingine shi a waje guda a kuma sake wani wasa da kuma salon suna wanda zai dace da yanayi da kuma lokacin da ake ciki. Su dai irin wadannan wasannin akan shirya su ne domin ilmantarwa, ko fadakarwa, ko gargadi, ko nishadantarwa ga jama’a a kan fa’ida ko muni ko kuma illar wani abu. Wasanni Gidan Talbijin Wasannin gidan talbijin su ne ake jin sauti kuma a kalli hoto. Irin wadannan wasanni su ma akan rubuta su ne, sa’annan a shirya a aiwatar da su tare da mutane a cikin akwatunan talbijin ko a fina-finan majigi. Ana tsara irin wadannan wasannin domin kwatanta halayyar rayuwar al’umma cikin wasa domin bayyana wadansu matsalolin da ke tattare da rayuwa. Wasannin gidan talbijin irin wadannan sun hada da wasan “Baban Larai da Idon Matambayi na gidan talbijin na Sakkwato, da Taskira da Kuliya manta sabo da Dankurma da Karo da Goma da Kaikayi da kuma Kwaryar Kira na gidan talbijin na Kano. Haka kuma akwai “Bakan Gizo na gidan talbijin na Kano mallakar jiha. Kuma akwai “Baba Soja da Kwashi kwaram da Golobo” na gidan talbijin tarayya da ke Sakkwato. Da yake dama dukkanin wasannin akwai alamar ana zama ne a rubuta su, sa'annan a gabatar, shi ya sa wadansu daga cikin wasannin suka koma littafi daga baya. Alal misali, Zamanin namu da Jatau na Kyallu na Shu;aibu Makarfi, an buga su daga baya. Haka kuma Zaman duniya Iyawa ne na Yusuf Ladan, wannan ya nuna mana cewa kamar yadda ake samu a kasashe da suka ci gaba ta fannin wasan kwaikwayo a gidajen rediyo da talbijin, a kasar Hausa ma wasannin a rubuce suke, ba a dandali kawai ake yi da ka ba, a ci gaba da aiwatarwa. Wani abin la'akari a nan shi ne, yawancin wasannin ba sa kasancewa na dindindin, yau a yi wannan, gobe a yi wancan, wasu su bace su dawo, wasu su bace har abada, sai dai su bar sunayen gwanaye ko wadanda suka yi suna a wasan, suna watayawa, alal misali: Kasimu Yero - Karambana Alh. Usman B. Pategi - Samanja Dauda Galadanchi - Kuliya Mustapha Muhammad - Dan Haki Umaru Ilu Ambursa - Baba Soja Umaru Danjuma Katsina - Kasagi WASANNIN KWAIKWAYO A BIDIYO Sinima ko fim a wasan Hausa sabuwar al'ada ce, wadda ba ta shigo cikin kasar ba sai a tsakanin shekarun 1950-1960. A can da majigi ne da gwamnatocin jihohi ke nunawa a filin kallo, kofar fada ko kuma a makarantun firamare, yawancinsu majigin a wancan lokacin bai wuce na koyar da tsafta ba ko noman gyada da auduga da sauran ayyukan farfaganda na mulkin mallaka. Daga baya sai aka dinga hadawa da na Cow Boy, wato Amurka don a nishadantar da masu kallo. Sha'awar da jama'a suka nuna na kallon wannan majigi, da kuma ‘yan kasa da suka fara fitowa fili wajen gabatar da wasannin majigi, kamar su Baban Larai ya sa wasu masu ido a Naira suka ga ai za su iya samun kudi ta wannan hanya, sai suka shiga gina gidajen sinima a biranen Kano, Kaduna, Katsina, Sakkwato da sauransu. Ta haka ne al'adar zuwa sinima don kallon fim din indiya da Amurka da Chanis ta kafu, ta kuma yi kaka-gida. Yara tun suna kanana sun saba shiga sinima, sun san ‘yan wasan Indiya da Amurka har ma suke kwaikwayon su. Da kasashen da suka ci gaba suka shigo da bidiyo, sai aka raja'a zuwa ga bidiyon domin ta fi saukin gudanar da al’amurra, don ba sai ka je wajen kallo ba a gida da kai da iyalanka za ku yi kallon duk abin da kuke so. Wannan cigaba, shi ya haifar da ‘yan gida masu neman kudi suka ga cewa lallai za a iya samun kudi ta haka, sai yawancin kungiyoyin wasannin kwaikwayon Hausa da kungiyoyin marubuta littatafai, musamman na Adabin Kasuwar Kano suka auka ga wannan sana'a, wadda a halin yanzu ta yi suna da samun karbuwa wajen jama'a. Yawancin fim din bidiyo da ake da su a yanzu sun samu ne ta fuskar littatafan Adabin Kasuwar Kano, wasu kuma an samar da su ne ta hanyar shirya labari mai ban sha'awa, ba tare da tsarin wasan kwaikwayo ba ko kuma labari don dai bidiyon kawai. SAUYIN YANAYIN WASANNIN KWAIKWAYON HAUSA Daga ire-iren wasannin kwaikwayon Hausa da muka nazarta, mun ga cewa, wadansu na baka ne ko kuma na gargajiya, wadansu zamani ya kawo su, wato rubutu (musamman na boko). Wasu ana aiwatar da su a gidajen rediyo da talbijin da bidiyo. Wani abin sha'awa shi ne yadda wadansu marubutan Hausa suka fassaro wadansu littatafan wasannin kwaikwayon Turawa da Larabawa zuwa Hausa, saboda a kwatanta tsarinsu da kara fahimtar sigogin wasan kwaikwayo. 1. Ibrahim Yaro Yahaya ya fassara Twelfth Night na Shakespeare daga ingilishi zuwa Hausa a matsayin Daren Sha Biyu. 2. Ahmed Sabir ya fassara littafin Ahlul-Kaf na Tawfiq Al-Hakim daga Larabci zuwa Hausa a matsayin Mutanen Kogo 3. Dahiru Idris shi ma ya fassaro littafin Merchant of Venice na Shakespeare zuwa Hausa da sunan Matsolon Attajiri Baya ga wadannan, akwai kuma littattafan labaran Hausa da dama da aka mayar wasan kwaikwayo, aka kuma aiwatar a dandali da gidajen talbijin 1. Shaihu Umar na Tafawa Balewa wanda Umar Ladan da Dexter Lyndersay suka baddalar zuwa Shaihu Umar. 2. Ruwan Bagaja da Ahmad Amfani ya baddala a bidiyo daga Hukumar Fina-finai Ta Jos ta mayar fim. 3. Magana Jari ce da NTA Lagos ta mayar wasan kwaikwayo a talbijin da Ingilishi da kuma na Hausa da NTA Kaduna ta baddalo.

Bayani Kan Rubutaccen Labarin Hausa

SHARHI KAN SAMUWAR ZUBE DA YADDA YA SAUYA KAMANNU A TSAKANIN SHEKARUN 1920 ZUWA 1980 ZUBE DA RABE –RABENSA A HAUSA Zube kalma ce ta Hausa da ke da fuskoki guda biyu, da farko akwai fuskar lugga sa’annan akwai fuskar zahiri. A zahirance zube na nufin abu ne a watse ko wanda bai da wani tsari ko dokoki da ke tafiyar da shi, alal misali kara a zube, na nufin yadda karan ke warwatse ba tare da wani shiri ko tsari ba. Ke nan zube na iya nufin duk wani abu da aka yi shi ko aka tsara shi ba bisa bin wasu ka’idoji ko tsari ba. Amma idan ana magana kan zube na lugga, yana nuna abin ya samo asali daga aikatau zuba, wato kamar ka zuba ruwa a kwano ko kasa, wannan shi ya haifar da kalmomi irin su zubar da ko zubewa ko zube ko kuma zubo daga cikin kalmomin aikatau na harshen Hausa, duk dai wadannan na nufin abin da aka aikata na watsarwa ko yasarwa ko makamantan haka. A adabance kuwa zube na nufin guntattakan jawabai ko bayanai da ke zuwa kara zube ba tare da wasu dokoki ko ka’idoji ba, sa’annan ana yin su ne domin a sa nishadi ko jin dadi ga mutane. A nan ana iya bambanta zube da waka da wasan kwaiwayo ta fuskar adabi, wato ana iya cewa a waka da wasan kwaikwayon sai an tsara, an kuma shirya, sa’annan kuma a daidaita tunani kafin a aiwatar da su alhali kuwa a zube ba a bukatar wadannan abubuwa. Ke nan zube na na nufin abubuwa irin su tatsuniya da karin magana da tarihi da tarihihi da kirari da zambo da almara da kissa da karangiya ko salon magana ko bakar magana. Bari mu dauki wasu daga cikin wadannan domin mu ga yadda fasalinsu ya kasance. ZUBE A ZAMANIN ZUWAN TURAWA Ko da Turawa suka shigo sassan kasar Hausa ba su shigo kasar a jahilce ba, domin suna da wata masaniya a kan mutanen wurin da kuma yanayin kasar. Labaran farko sun je gare su ne daga ayyukan matafiya da suka ratsa Kasar Hausa, suka wallafa littattafai game da kasar da mutanenta, daga cikin irin wadannan marubuta da masana akwai Ibn Batuta da kuma Leo Africanus. Shi Leo Africanus a cikin littafinsa na 7 ya bayyana labarin abubuwan da ya gani ko ya ji a lokacin ziyarar da ya kai Afirka. Saboda haka tun a karni na goma sha tara (19) kungiyoyi daga jinsin Turawa, sun aiko da masana don su binciki yadda kasashen Afirka suke da yadda al'adunsu ke gudana da yanayin harsunansu da kuma addinansu. Sa'annan kuma su bincikio hanyoyin sadarwarsu ta ruwa da ta kasa da kuma matakan da suke amfani da su ta fuskar ciniki da saye da sayarwa. Wannan kokarin sanin yanayi da al’ummar nahiyar Afirka da Turawa suka yi ya kawo kakkafa kungiyoyin Turawa masu manufofi daban - daban. A Ingila an samar da Kungiyar Afirka a 1788. Wannan kungiya ita ta turo su Mungo Park da Clapperton da Denham da 'yan uwan nan guda biyu wato Landers Brothers, wadanda suka ziyarci yankunan kasar Hausa. Baya ga wadannan kungiyoyi na neman sanin halayen da kasashen Afirka suke ciki, akwai kuma kungiyoyin Mishau da Turawa suka turo don bincike, musamman kan al'adu da harsuna da addinan kasashen Afirka a tsakanin karni na 18 da na 19. Shahararru daga cikin wadannan 'yan mishau su ne Barth da Schon. Ta fuskar ayyukan Barth da Schon ne labaran kasar Hausa da jama'arta suka isa Turai, kai tsaye. Barth ya wallafa littafi mai dauke da bayanan abubuwa da ya ji, ko ya gani a arewaci da tsakiyar Afirka a tsakanin shekarar 1857 zuwa 1859. Ya kuma wallafa wani littafi mai dauke da bayanan harsunan Hausa da Fulani da Barebari da Wangala da Bagurma a shekarar 1862. Wanda ya wanzar da rubutun adabin Hausa sosai ta fuskar amfani da haruffan Romanci shi ne J.F. Schon. Ya zo Yammacin Afirka ne a karkashin kungiyar Mishau ta C.M.S, inda a 1832 ya ziyarci Senegal. A takanin 1841 har zuwa 1847 ne ya ziyarci kasar Hausa da wasu yankunan kasar Neja. Wadannan yawace-yawace da Schon ya yi sun sa ya iya wasu harsuna da yawa har ya sami kwarewa a cikinsu, musamman harsunan wuraren da ya ziyarta. Ta haka ne kuma ya sami damar yin nazari da rubuce-rubuce a kan wasu harsunan, musamman harshen Hausa. Ya wallafa littattafai kan kalmomin Hausa a 1843 da Kamus na harshen Hausa a 1876 da Littafin Karin Maganganu da Labarai da Tatsuniyoyin Hausa a 1886 da kuma Littafin Magana Hausa (1885) da wasu da dama da suka shafi addinin Kirista. Ayyukan da su Schon suka gabatar sun bada haske wajen samar da wata kafa ta mayar da adabin bakan Hausa a rubuce. Domin haka, tun kafin a kafa mulkin mallaka a kasar Hausa aka mayar da wasu sassan adabin bakan Hausa a rubuce cikin haruffan Romanci. Misalan wadannan rubuce-rubuce sun kunshi tattara labarai da tatsuniyoyi da karin maganganu da sauran maganganun azanci da al'adun Hausawa wuri guda a takarda. Daga shekarar 1891 aka sami littattafai da yawa da suka kunshi irin wannan fasali. Daga cikin littattafan da suka yi fice akwai Specimens of Hausa Literature na C.H. Robinson (1896) da kuma Hausa Stories and Riddles na H.C. Harris (1908) da Littafi na Tatsuniyoyi na Frank Edgar (1924) da Hausa Sayings and Folklore na Fletcher, R.S (1912) da sauran su. Wannan tafarki da Turawa suka bi shi ne ya wanzar da abubuwan amfani dangane da rubutun bokon Hausa. Ta haka aka sami damar zama don kyautata nazari da kuma rarraba sigogin rubuce-rubucen zuwa azuzuwa mabambanta. Shi ya sa ko da Turawa suka mallake kasar Hausa, ayyukan adabi ta fannin tatsuniyoyi da labarai da maganganun azanci sun sami karbuwa ta amfani da haruffan Romanci. Dangane da haka, zuwan Turawa kara taimakawa ya yi wajen kafa makarantun koyar da nazarin ilmi, inda ta haka ne aka dada fadada hanyoyin wanzar da rubutun Hausa. A wannan lokaci ba a yi wani tanadi dangane da tsarin da za a bi na kyautata ilmin boko ko kuma yadda za a yi da na Musulunci da aka iske ba. Abin da Turawa suka mayar da hankali a kan sa shi ne, tattaunawa kan batutuwan da suka shafi gudanar da ilmi, ba kokarin wanzarwa ba, sai dan abin da ba rasa ba da masu aikin Mishan suka yi Lokwaja da Wusasa Zaria kafin tabbatuwar mulkin mallaka. ZUBE DA SAMUWAR HUKUMOMIN INGANTA ADABI Hukumomin inganta adabin Afirka ba su da wata fuska takamaimiya sai wadda gwamnatin mulkin mallaka ta samar a kowace kasa da take mulki, sai dai domin abubuwa su daidaita an samar da hukumar Kasa da Kasa Ta Nazarin Harsuna da Al’adun Afirka da Kungiyar Afrika da kuma Mujallar da take bugawa ta Afrika tun daga 1908. Wadannan hukumomi sun taimaka wajen dora harsashin samar da adabin Afirka a cikin boko, musamman na Hausa da aka fara jin duriyarsa tun daga 1929. A wannan shekara ce hukumar Kasa da Kasa Ta Nazarin Harsuna da Al’adun Afirka ta shirya gasar rubutun Hausa (kagagge ko zube). Tun da farko an tsara abin ne daga London karkashin kulawar shugabannin Hukumar Nazarin Harsuna da Al’adun Afrika. Wannan hukuma da hadin kan hukumomin kula da ilmi na kasashen Afirka daga farkon shekarun 1920 sun shirya gasar rubutu tsakanin dalibai da malaman makarantun kasashen a cikin harsuna ‘yan gida kan zube da kagaggun labarai. A kasar Hausa yawancin wadanda suka shiga gasar malaman makarantun boko ne. Alal misali gasar da aka yi a 1929, littattafan da aka samu har guda 37 ne, 10 a cikin harshen Hausa, 15 a cikin harshen Suto, 9 a cikin harshen Ganda da 2 a cikin harshen Madingo da kuma 1 a cikin harshen Mende. Littafin Komane mai taken Esela e isang phethehong a cikin harshen Suto da kuma na Lwanga mai taken Ebyafayo bya Baganda a cikin harshen Ganda, su ne suka zo na biyu, ba wanda ya yi nasarar zama na daya, saura kuwa duk sun sami yabo ne kurum. LABARUN HAUSA NA FARKO-FARKO A RUBUCE Idan aka yi nazarin littattafan da suka sha yabo daga harshen Hausa za a ga cewa sun kasance kamar haka; akwai na H.B.G. Nuhu mai taken Hausa Stories da na Malam Dodo shi ma Hausa Stories, sai na Malam Ahemet Metteden, mai suna Zaman Dara da na Malam Bello Kagara mai taken Littafin Karatu Na Hausa, sai kuma na Malam Nagwamatse, mai suna Takobin Gaskiya. Daga wannan gasa mun fahimci cewa tuni wadanda za su yi wani abin a-zo-a-gani game da kagaggen adabin Hausa sun fara bayyana;Malam Bello Kagara yana daga cikin wadanda suka cinye gasar da hukumar fassara ta shirya a tsakanin 1932 zuwa 1933 da littafinsa Gandoki, shi kuma Malam Nagwamatse duk da cewa bai ci wani abu a gasar 1932/1933 ba, amma ya sha yabo da littafinsa na Boka Buwaye. ZAMANIN HUKUMAR FASSARA Daga abin da muka gani a sama ko da shekarar 1929 ta karasa cika akwai hukumar Fassara a kasar Hausa, domin ita ce ta kasance unguwarzoma a lokacin waccan gasa ta farko. Saboda haka karuwar makarantu da dalibai na gwamnati, ya kara sabon nauyi ne ga hukumar ta Fassara. Saboda a sami hanyar samar da littattafan karantawa da sauran kayan aiki a wadannan makarantu, aka yi shawarar kafa wannan hukuma wadda za ta kula da wannan al'amari a tsarin hukuma ta dindindin. Tun daga 1924 wannan batu ya kunno kai, jami’o’in kula da sababbin makarantu na kasar Hausa sun sha aike wa da rahotanni zuwa Kaduna dangane da amfanin da ke tattare da manufar kafa wata hukuma da za ta samar da kayan aiki na ma’aikatar ilmi da kuma raya adabi, amma hakan ba ta faru ba, sai a 1929, lokacin da aka kafa Hukumar Fassara. Wannan hukuma ta fassara ta fara zama ne a cikin ofisoshin makarantar Dan Hausa da ke Kano. Hukumar ba ta sami mazauninta na musamman ba sai a 1930, inda aka gina shi a Kofar Tukur-Tukur, Zariya. Babban aikin wannan Hukuma shi ne shirya littattafan Hausa don karatu da koyarwa a makarantu. Hukumar ta soma gudanar da ayyuka ne karkashin jagorancin Mista C.E.J. Whitting wanda ya hannunta aikin gudanar da hukumar ga Mista R.F.S.Parry (Jami'i mai kula da ilmi da ke Zariya). A ran 2/4/1931, Kyaftin F.W. Taylor ya amshi ragamar shugabancin hukumar tare da ma'aikata 'yan kasa da suka hada da Malam Sule Isa da Malam Tafida da Malam Umaru, da kuma Malam Shekarau. A shekarar 1931 Hukumar Fasssara ta fuskanci aikin fassara gadan-gadan tare da shirya littattafai don samar da abin karantawa da koyarwa a makarantun gwamnati. Littattafan da wannan hukuma ta fara fito da su sun ta’allaka ne kan tarihin kasar Hausa, inda aka shirya littafin Hausawa da makwabtansu da kuma fassara littafin Koyar Da Kiwon Lafiya (I). Daga nan kuma aka tsara littafin Jimlolin Hausa Zuwa Ingilishi. Akwai kuma littafin Koyarwa na Lissafi da Littafin karantawa na fari. Har wa yau, a shekara ta 1931 aka tsara littafin Labaru Na Da Da Na Yanzu (NAK/KAD/EDU/746). A ranar 18 ga Fabrairu 1932, Kyaftin Taylor ya ajiye aikin shugabancin hukumar fassara, wannan ya sa aka rufe hukumar na wani lokaci, sai a ran 17 ga watan Mayu aka sake bude hukumar a Katsina, a karkashin shugabancin Mista R.M. East. Daga watan Disamba na 1931 zuwa watan Fabrairu na 1932, hukumar fassara ta samar da littattafai da suka hada da Darussan Koyarwa Don Makarantun Elementare da littafin Bayani Kan Cututtuka da kuma Magaurayi. A wannan shekara kuma aka kammala fassara littafin Koyar Da Kiwon Lafiya (II), aka kuma sake wa Aljaman Yara fasali, aka sake buga shi. Hukumar ta yi gyare-gyare ga littafin Labaru Na Da Da Na Yanzu, inda aka fassaro sassan tarihin kasar Hausa da suke rubuce cikin harshen Larabci, aka zuba su a cikin wannan littafi. Tun daga shekarar 1932 R. M. East ya soma nuna damuwarsa dangane da yadda hukumar fassara ke gudanar da ayyukanta. A nasa tunanin, ya ga cewa ayyukan da ya kamata hukumar ta yi sun wuce fassara kawai. Shi ya sa yana hawa bisa ragamar shugabancin hukumar ya shiga fiddo da sababbin abubuwa da za su inganta aikin hukumar. Baya ga fassarar ayyukan gwamnati da littattafan Elementare, hukumar ta tsara da buga littattafai da dama, ga kuma buga Jaridar Nijeriya Ta Arewa da aka soma a 1932. Haka kuma a sakamakon wannan tunani na R.M. East na kokarin inganta adabin Hausa ya sa aka soma tunanin yadda za a samar da kagaggun labarai daga ‘yan kasa domin nishadantar da al’umma. Haka kuma an hada har da yin talifi da kuma sayar da littattafai da aka rubuta a cikin harsuna daban-daban na kasar Hausa don samun riba. Hukumar ta tsara yarjejeniya da mawallafa da masu buga littattafai da kuma tsangayoyi na ilmi na Larduna kan tafarkin da ya dace su bi a ga an sayar da littattafan da hukumar ta tsara, ta kuma buga. SAMUWAR LABARIN FATIMA Har zuwa farkon shekarar 1933, hukumar fassara ta ga ba a sami littattafan adabin da take bukata da suka shafi kagaggun labaran Hausa ba. Sai dai wani abin la’akari ko da hukumar ke ta wannan fafutika, su ‘yan Mishau tuni sun yi nisa a wannan fage na samar da kagaggun labarai, domin kuwa W.R.S Miller da kungiyar Mishau ta C.M.S tuni suka fahimci amfanin wannan fasali na kaga labari, domin isar da sako, saboda haka sun fitar da littafin kagaggen labari na farko da aka buga da harshen Hausa mai suna Fatima, na Miller a 1933. Wanda da alama bai gamsar ba, shi ya sa ba a ji amonsa ba a cikin karikitan kagaggun labaran Hausa tun wancan lokaci. Kila ba wani abu ya sa haka sai domin ba ya dauke da komi sai wa’azin kirista da yada manufofin addinin Kiristanci. Watakila ganin irin rawar da C.M.S da Miller suke neman takawa ya sa aka shirya gasa ta biyu da ta taimaka wajen samar da littattafan adabin Hausa na farko ta fuskar zube daga ‘yan gida. An dai shirya wannan gasa ne da manufofi biyu. Da farko a samar da ingantattun littattafan adabi, na biyu a sayar da littattafan, ba a raba kyauta ba kamar yadda aka saba yi a da.25 Wannan gasa ta samar da littattafai da suka inganta tare da kyautata adabin Hausa, an gudanar da ita ne a shekarar 1933. GASAR LABARAN HAUSA TA 1933 Hukumar Talifi ta sami littatttafai da dama da suka amsa kiran shiga wannan gasa. Da yawa daga cikin littattfan da aka rubuto, aka aiko wa hukumar sun dace da tsarin da ta shimida. Lokacin da Hukumar ta zo buga littattfan wadanda suka lashe gansar, sai da ta tace su sosai, musamman ta tattace farkonsu da karshensu, ta kuma sake tsarin wasu daga cikin babobinsu, sa'annan ta buga su. Bayan da Hukumar Talifi ta gama tsara da sake fasalin wadannan littattafai ta fitar da sakamakon gasar kamar haka: (i) Ruwan Bagaja Malam Abubakar Kagara (An buga shi 1935) (ii) Gandoki Malam Bello Kagara (An buga shi 1934) (iii) Shaihu Umar Malam Abubakar Bauchi (An buga shi 1934) (iv) Idon Mtambayi Malam Muhammadu Gwarzo (An buga shi 1934) (v) Jiki Magayi East da Tafida (An buga shi 1934) Duk da cewa wadannan su ne aka zaba a matsayin wadanda suka ci gasar, akwai wasu da suka gamsar, aka tsara su don bugawa, amma ba a sami damar buga su ba, su ne: (i) Boka Buwaye Malam Nagwamatse (ii) Yarima Abba Malam Jumare Zariya. Bayan gasar da littattafan da ta samar, an sake tsara tare kuma da juya sigar wasu littattafai guda biyu wato A handbook On The Teaching Of The Elementary School History and Geography da aka fassara da Koyarwar Labarin Kasa Da Tarihi da littafin Al'amurran Duniya Da Na Mutane. Ganin irin kwazon da Abubakar Imam ya nuna a gasar da aka yi ta 1933 da littafinsa na Ruwan Bagaja da aka buga a 1935 ya sa a shekarar 1936 aka gayyaci Abubakar Imam domin ya wallafa littafin Magana Jari Ce (I-III). Ya dace a yi bayani a nan game da yadda aka yi aka tsara littafin Magana Jari Ce, da irin yadda rubutun littafin ya jawo sauya sunan hukumar daga ta fassara zuwa ta talifi. Kamar yadda Abubakar Imam ya bayyana a cikin littafinsa na tarihi, ko da aka nemi ya tafi Zaria don aikin Magana Jari Ce ya isa ofishin hukumar ne da tunanin yaya wurin yake.Yana zuwa kuwa abin da ya soma magana kai shi ne sunan hukumar, nan take kuwa ya nuna cewa ya dace a sake dubar sunan,wato na Ofishin Fassare-Fassare,domin kuwa ayyukan hukumar sun fi na fassara kawai, kamar yadda ya gani kuma ga shi ya zo yin aikin talifi ne ba fassara ba. An bada aron Abubakar Imam domin aikin Magana Jari Ce daga 21/5/36 zuwa 19/11/36, saboda haka ko da East a ranar 24/10/1936 ya aika da wasika ga Babban Sakatare Mai Kula Da Harkar Ilmi domin a sauya sunan hukumar ta fassara da alama shawarar Abubakar Imam ce ya dauka, domin kuwa a daidai lokacin Abubakar Imam na tare da East a Zariya, sai dai ba a sami damar yin wannan sauyi ba sai a ranar 2/11/1937, inda aka kira shi da ‘Hukumar Talife-Talifen Harsunan Afirka,’ inda daga baya ya koma Hukumar Talifi a takaice. A shekarar 1937 a sakamakon yarjejeniyar da aka yi da Mishan-Mishan da Hukumar Talifi aka amince su fitar da littattafai don amfani a makarantunsu, musamman a kananan azuzuwa na makarantun Elementare, amma an hana su danganta littattafan da wani addini. Littattafan da aka fara samar wa a karkashin yarjejeniyar sun hada da Ka Koyi Karatu (1938) da Ka Kara Karatu (1938) na kungiyar S.I.M da ke Jos. Wadannan littattafai su suka jawo hankalin Hukumar Talifi ta sake neman Abubakar Imam ya wallafa littattafan karantawa a kananan azuzuwan Elementare don Magana Jari Ce an ga ta yi girma ga wadannan azuzuwa. Ya rubuta littattafai guda biyu a Katsina, su ne Karamin Sani Kukumi Ne (I-II) a cikin watan Satumba, 1938. A shekarar 1938 ne aka soma maganar buga wata jaridar Hausa, wadda za ta kunshi abubuwa daban daga wadanda tsohuwar jaridar Nijeriya ta Arewa ke kunsa, aka kuma nada Mista L.C. Giles a matsayin Edita, Malam Abubakar Imam a matsayin mataimaki, ta fara fitowa a Janairun 1939. Nada Abubakar Imam a bisa wannan mukami ya kara fadada ayyukan Hukumar Talifi. Samar da jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ya bayar da kafa ta inganta ginuwar ayyukan adabin Hausa. Fitowar Gaskiya Ta Fi Kwabo ya sa jama'a suka raja'a kanta, inda a bugun farko a watan Janairu na 1939 aka sayar da kwafe dubu biyar (5,000), a watan Fabrairu aka sayar da kwafe dubu takwas da dari tara (8,900), a watan Maris aka sayar da kwafe dubu goma sha daya da dari biyu, (11,200). KAFA JARIDAR GASKIYA TA FI KWABO DA KAMFANIN GASKIYA Kafa jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ya kara jawo ra'ayin jama'a dangane da saye da karanta ayyukan adabi. A cikin jaridar, akwai filaye da aka fito da su don makaranta wadanda ke aiko wasiku na bayyana ra'ayoyinsu, ana samun irin wadannan wasiku sama da dari (100) a kowane wata. Kuma akan buga wakokin da wasu suka rubuta da amsa gasar wasannin wasa kwakwalwa da sauran su. Haka ayyukan Hukumar Talifi suka ci gaba da gudana har zuwa 1944, lokacin da ayyuka suka fara yawa sosai. Sa'annan ga kuma aikin buga jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo, wadda daga 1940 aka soma buga kwafe dubu sha biyar (15,000), dalilin da ya sa ta koma fitowa sau biyu a wata. Tsara da fassara littattafai, su ma suka yawaita, dalilin da ya sa tun daga 1939 aka dinga daukar kwararrun ma'aikata 'yan kasa don su agaza. Daga cikin wadannan ma'aikata 'yan kasa akwai Malam Nuhu Zariya da Alhaji Sani Kwantagora, wadanda aikinsu shi ne fassara dokokin gwamnati da wasu jawabai da aka yi a majalisar sarakai. A wannan lokaci ne aka samar da fassararrun jawaban gwamnan Arewa zuwa ga sarakuna da wasu da dama. Dukkan wadannan ayyuka da aka gudanar a Hukumar Fassara da ta Talifi ba wata madaba'a da ake da ita ta hukuma. Sau da yawa ana zuwa Ingila ne ko kuma Jos a buga wadannan ayyuka. Wannan ne ya sa gwamnati ta soma tunanin kafa wani kamfani da zai dinga buga wadannan littattafai. Da taimakon gwamnatin Ingila, a shekarar 1945, aka kafa kamfanin Gaskiya (Gaskiya Corporation) a kusa da ofishin hukumar Talifi a Zariya. Daga wannan shekara sai aka mayar da shirya littattafai da fassara da kuma buga su a rumfa daya. Ta haka ne aka samar da littafin Mungo Park Mabudin Kwara da Bala Da Babiya na Nuhu Bamalli da Yawon Duniyar Haji Baba na Tunau Mafara da sauran su. Daga karshen 1949, makarantun boko suka kara yawaita a kasar Hausa. Kuma shirin gwamnatin Arewa na yaki da jahilci ga wadanda ba su sami zuwa makaranta ba ya kankama. Wannan ya sa daga 1950 zuwa 1953 ayyukan yaki da jahilci suka tsayu sosai,domin haka aka kafa kwamitoci da za su gudanar da azuzuwan karatu da hanyoyin da za a bi wajen koyarwa da kuma shirya littattafai don makarantun da aka bude. Wannan yunkuri shi ya haifar da kafa Hukumar NORLA a shekarar 1954. Hukumar ta gudanar da ayyuka da dama, musamman tsara da kuma buga littattafai da buga jaridun Larduna. An wallafa littattafai masu yawan gaske, wadanda suka kunshi darussa daban-daban da suka hada da addinin Musulunci da labarai kamar su Ibada Da Hukunci. Wasu littattafan sun kunshi tarihi kamar, Zuwan Turawa Nijeriya Ta Arewa da Tarihin Fulani da kuma Hanyoyin Koyar da Sana'o'in Hausa da littattfan hira da nishadi daban-daban, tare da wakokin Hausa, nau'i-nau'i. SAMUWAR HUKUMAR NORLA Ana iya cewa Hukumar NORLA ita ce ta habakar da ayyukan adabin Hausa fiye da sauran hukumomin da aka yi a baya. Ta ci gaba da gudanar da wannan aiki har zuwa 1959, lokacin da aka rushe ta, aka mayar da aikinta hannun kamfanin Gaskiya. A wannan lokaci ne aka buga littafin Gangar Wa'azu da Zamanin Nan Namu da Jatau Na Kyallu. Haka aka ci gaba da gudanar da aikin inganta adabi har lokacin da aka samar da yarjejeniya tsakanin gwamnatin Arewa da wani kamfani na Ingila mai suna Macmillan, wanda ya haifar da kamfanin wallafa littattafai na Arewa (NNPC) a 1966. Samuwar wannan kamfani ya sa saiwar gina littattafan adabi ta dasu zuwa wasu sassa na kasar Hausa. A wannan kamfani ne aka sake tsara da buga wasu tsofaffin littattafan da hukumomin baya suka samar. Shi ma wannan kamfani na NNPC ya taka muhimmiyar rawar wajen bunkasa tare da samar da hanyoyin habaka cigaban wanzuwar littattafan adabin Hausa. KAFUWAR HUKUMAR NNPC Haka aka dinga gudanar da aikin inganta adabi har lokacin da aka samar da yarjejeniya tsakanin gwamnatin Arewa da wani kamfani na Ingila mai suna Macmillan, wanda ya haifar da kamfanin NNPC a 1960. Samuwar wannan kamfani ya sa saiwar gina littattafan adabi ta dasu zuwa wasu sassa na kasar Hausa. A wannan kamfani ne aka sake tsara da buga wasu tsofaffin littattafan da hukumomin baya suka samar. Shi ma wannan kamfani na NNPC ya taka muhimmiyar rawar gani wajen bunkasa tare da samar da hanyoyin habaka ci gaban wanzuwar littattafan adabin Hausa. Baya ga ayyukan da ta rinka bugawa kan adabi da sauransu, hukumar ta sa gasa ta kagaggun littattafai a cikin shekarar 1980 inda ta buga uku daga cikin wadanda suka yi nasara. Littattafan da suka fito daga wannan gasa sun hada da Mallakin Zuciyata na Sulaiman Ibrahim Katsina da So Aljannar Duniya na Hafsat Abdulwaheed da kuma Amadi Na Malam Amah na Magaji Danbatta. ABUBUWAN DA SUKA GINA LABARUN ZUBE DAGA 1960 ZUWA 1980 Abin kula daga farko shi ne a fahimci cewa shekarun 1960 sun kasance na samun ‘yancin kai da juyin mulki da kuma yakin basasa. Ma’ana a cikin shekarar 1960 Nijeriya ta samu ‘yancin kanta, saboda haka labaran zube da suka famtsamo daga wannan lokaci za a ga suna da sifofin kwatar ‘yanci da kishin kasa da kuma gwagwarmayar rayuwa bayan samun mulkin kai. Saboda haka baa bin makaki ba ne marubuta su yi amfani da wannan dama su kalli rayuwar al’ummarsu ta wannan lokaci. Da kuma aka yi juyin mulki a shekarar 1966 aka kashe ‘yan siyasar farko na Arewacin Nijeriya sai abubuwa suka canza a farfajiya da tunanin al’ummar wannan yanki. Da kuma aka yi rikicin A-Ware bayan juyin mulki a arewacin Nijeriya, wanda ya jawo sake yin juyin mulkin Gowon sai al’amurra suka canza fasali. Wannan shi ya jawo rikicin Nijeriya day a kai gay akin Basasa daga 1967 zuwa 1970. Wannan takaddama da ta faru za ta yi tasiri a rayuwar al’ummar Arewa da kuma musamman marubutanta. Dangane da haka baa bin mamaki ba ne idan labarun zuben da da aka rubuta a wannan tsakani ko kuma wadanda suka biyonsu suka kasance masu dauke da wannan ruhi, na rikice-rikice da fadace-fadace da halbe-halbe da uma siyasar irin ta kishin kasa. Alal misali labarai irin Kitsen Rogo na Abdulkadir Dangambo da Karshen Alewa Kasa na Bature Gagare da Zabi Naka na Munir Mohammed Katsina, suna dauke da irin wadannan fasaloli. Alhali kuma rayuwar da ta shafi ginuwar tattalin arziki da ilmin boko da zamantakewar yau da kullum ta wannan zamani ta taimaka wajen samuwar wasu rubutattun zube. Ma’ana, yadda aka samu garabasar man metur daga farkon shekarun 1970 da yadda kuma aka ga bullar dalibai masu tarin yawa daga shirin UBE na 1976, wanda daliban farko suka antayo cikin al’umma da kishirwar son karatu da kuma bullar kayan kallo irin na talbijin da bidiyo a daidai wannan lokaci shi ma ya kara sa wa marubuta kaimi na rubutun zube, musamman daga rayuwar da suka tsinkaya. Labarai irin su So Aljannar Duniya da Tauraruwar Hamada da Tauraruwa Mai Wutsiya da Turmin Danya da wasu da dama bisa wannan tafarki suka wanzu. A ciki ne za a ga rayuwar sumogal da soyayya da ilmin zamani da yadda zamantakewar al’umma baki daya. Saboda haka duk yadda aka so ba zai yiwu ba a canza tunanin marubuci daga abin da ya riska ko ya riske shi ko kuma tsinkayar yadda lamurra za su kasance a cikin labaran da yake rubutawa. WASU HANYOYIN NAZARIN LABARAN ZUBE Hanyoyin nazari uku za mu bi domin mu aza misalin yadda za a iya kallon rubutun zube. Akwai Jigo da Warwarar Jigo da kuma Nazarin Salo. JIGO Jigo kalma ce Bahaushiya da ke da ma’anoni mabambanta. Tun da farko Hausawa na yi mata kallon ginshiki da e cikin daki ko kuma gini. Haka suna kallonta a matsayin tubali ko tushe ko fandashin da ke dauke da gini. Haka kuma suna yi mata kallon wani muhimmin kayan aikin da masu noman fadama ke amfani da shi wajen ban ruwa. Idan aka yi dubi wadannan ma’anoni da Ba haushe ya bayyana game da jigo za a ga cewa ba wani abu suke nufi ba face mazaunin abu, ko mafarinsa ko kuma abu mai muhimmanci da kila in ba shi a cikin tsari wani abu ba zai wanzu ba. Misali ginin da bai da fandeshin da wuya ya yi karko, mai noman fadama da bai da kwaryar da take kai ruwa ga gona, da wuya noman ya dore. Haka kuma dakin da bai da ginshiki da wuya ya yi karko. Ke nan wannan abu jigo da masu adabi suka aro sun mayar da shi ne a matsayin sako, manufa, ko abin da waka ko zube ko wasan kwaikwayo suka kunsa. A nan ana maganar abin da labarin ya kunsa ko yake magana kai ko kuma ruhinsa. Wato dai duk wani abu da in ba shi a cikin labarin to da wuya labarin ya zauna ko ya yi armashi. Saboda haka idan ana magana kan jigon labarin zube, ana nuni ne ga babbar manufar marubucin, wato wadda ita ce a zuciyarsa a lokacin da yake kokarin tsara labarin. Alal misali labarin Ruwan Bagaja babban jigon bai wuce shashantarwa ba, ko kuma a ce nishadantarwa. Wato an gina labarin domin a sa dariya da nishadi. Ko kuma littafin Jiki Magayi da ya kasance bisa tunanin soyayya, ko kuma Shaihu Umar da ke fadakarwa ko labarin Amina ko Mace Mutum da ke neman ‘yancin mata. Abin da za a kara a nan shi ne baya ga babban jigo kuma ana da kananan jigogi da suke taimakawa wajen gina labarin, su wadannan kuma kowane mai nazari da yadda yake kallon su. Alal misali a cikin lbarin Ruwan Bagaja akwai karamin jigon kara da ilmi da yawon bude ido da wasu da dama. Haka ma a labarin Shaihu Umar an sami kananan jigogi irin na ilmi da soyayya da makamantan su. WARWARAR JIGO Abin da ake nufi da warware jigo kuwa bai wuce mai nazari ya bi zaren da ya dinke labarin ba yana yi masa kulli ta yadda zai sami hadi guda, wato ya bude labarin nasa, sa’annan ya ja zaren ta amfani da babban jigon domin ya tabbatar sakon bai fandare ba. Ana iya ganin haka a cikin labarin So Aljannar Duniya inda aka dinke zaren da kitsa soyayyar Badodo da Yasir. Ko kuma ban dariyar da ke cikin labarin Ruwan Bagaja har zuwa karshen labarin da za a dire da wani abu na daban. SALO Shi kuwa nazarin salo a labaran zube hanyoyi uku suke yi masa jagora. • Zabin kalmomi • Dabara • Mutum ZABIN KALMOMI Idan ana son a fahimci salo to ya dace a gane irin siffofinsa na asali. Ba wani abu ba ne salo face irinkalmomin da mai rubutu ya zaba da gangan domin ya gina labarinsa ko waka ko kuma wasan kwaikwayo. Idan aka ce salo zabi ne na kalmomi ana nufin gwaninta ce mutum ya zabi kalmomin da za su burge ko su sa tunani a wajen mai karatu. Alal misali a waka: ‘Yar budurwa son ki nake Kin bugan sarka a wuya In na yo carar zakara Kyarkyarata gun ki take Shi ko wancan son da yake Duk bidar zakinki yake Daga wadannan baitoci za a ga cewa mai wakar ya zabi kalmomi ne da gangan domin ya gina wakar cikin armashi da burgewa. Kalmomi irin su Sarka da carar zakara da kyarkyara da zakinki duk an zabe su ne su dace da irin salon da aka yi amfani da shi. Haka batun yake a cikin tsarin rubutun zube. Dubi yadda marubucin Kifin Rijiya ya bayyana wahalar da Shaihu Aboki ya sha a duniya: ‘Irin wahalolin da ya sha, da kulli-kucciyan da ya sha yi da hadurra...’ Ta yaya ake yin kulli-kucciya, wannan zabin kalmomi na musamman domin gina salo. Ko kuma yadda aka bayyana cin hanci a cikin labarin Ruwan Bagaja ta sakaya cin hancin ta amfani da dabara. DABARA Haka ana ganin salo a matsayin dabara ko gwaninta ko iyawa ko wata hanya ta burgewa a lokacin isar da sakon marubucin. Dabarar nan tana iya zuwa ta fuskoki daban-daban. Ko dai ta hanyar bude labarin ko gina cikinsa ko kuma dire shi. Alal misali akwai salon da aka saba wajen bude labari irin: A wata kasa... a A wani gari... ko kuma A wani shudadden zamani ko Wata rana... da sauran su. Amma sai a ga marubuci ya kauce wannan tsari da gangan, ya kitsa nasa. Misali a cikin labarin Karshen Alewa Kasa an bude ne da wani salo na musamman: Til kwal! Tin kwal!! Tin kwal!!! Kai za ka dauka daka ne ake yi ba labari ba. SALO MUTUM NE Idan an ce mutum ne salo, a nan ana magana ne bisa irin yadda Ubangiji ya tsira kowane dan Adam. Ba mutum biyu da suke kama da juna ta kowace irin fuska ko hali. Haka kuma tunanin kowane mutum daban yake da na dan uwansa. Ke nan abin da wani ya kitsa a labarinsa yana tafiya da salon nrayuwarsa ne. Duk irin yadda mmarubuci yake gudun sanya halinsa ko rayuwarsa ba zai yiwu ba. Wannan ya kara tabbatar mana da cewa halayyar dan Adam ita ke gudanar da salon da ake gani a cikin labarin da marubucin ya rubuta. Allal misali, salon ban dariya na Abubakar Imam a cikin Ruwan Bagaja ko salon kaddara na Abubakar Tafawa Balewa a cikin Shaihu Umar ko salon tashin hankali a cikin labarin Karshen Alewa Kasa na Bature Gagare abubuwa ne da suke ginu bisa rayuwar marubutan. Dangane da haka ake ganin salon kowane mutum na bayyana ne daga ginuwar rayuwarsa.

Mene Ne Adabin Kasuwa?

MENE NE ADABIN KASUWA? Tare da Bashir Abusabe Kamar yadda muka sania rayuwar adabin Hausa ta biyo zanguna mabambanta, wannan ba sai an yi dogon sharhi ba, domin kuwa daga tashin Hausawa na zaman gargajiya har zuwa lokacin da suka cudanya da baki an sami sauye-sauye da adabin Hausawa ya yi ko dai ta fuskar sauyawar riga daga ta gargajiya zuwa ta zamani (Larabci ko Ingilishi ko Faranshi) ko kuma ta sauyawar kayan cikin adabin saboda haduwa da sababbin ladubban rayuwa . Irin sauye-sauyen da aka samu daga gargajiya zuwa zamani abu ne da masana sun sha ambaton sa, kila abin da ba a fi mayar da hankali kai sosai ba shi ne yadda gwamutsuwa da bakin al’amurra ke haifar da sababbin batutuwa da ke bukatar kara bincike da nazari. Batutuwan da suka yi tashe a cikin ‘yan shekarun nan, musamman abin da ya shafi kagaggun labaran Hausa, bai wuce batun nan na Adabin Kasuwar Kano ba, wato littattafan da yawancinmu ke kira Labaran Soyayya da suka tuzgo daga sassa daban-daban na kasar Hausa da ke hedikwata a birnin Kano. Samuwa da watsuwa ko kuma karbuwa da kuma ce-ce-ku-ce da wannan sabon salon adabi ya samu kansa a ciki, tsakanin marubuta da manazarta da masana a kasar Hausa da ma sassan duniya daban-daban ya jawo ayyukan nazari da musayar miyau mai tarin yawa. Abin da za mu yi kokarin yi a nan shi ne shimfida tabarmar nazari game da wannan fage ta hanyar neman sanin yadda adabin kasuwa yake ta hanyar tambayar ko akwai wani abu wai shi adabin kasuwa? Idan akwai shi to a yaya yake? Shin ana iya samun sa a kasashe masu tasowa kamar Nijeriya? Ko kuwa dai wanda ake da shi da ake kira Adabin Kasuwar Kano, an sa masa sunan ne domin cin mutunci da batunci ko son rai? Abin da za mu sa gaba bai wuce amsa wadannan da ma wasu tambayoyi da ka iya biyo baya ba, ta haka kila haske ya karu game da wannan fage na tarihin adabi da zai bayyana mana bambancin da ke tsakanin adabi na zahiri da wanda ake kira na kasuwa da kuma yadda irin fasali ya samu ginuwa a kasar Hausa. Yanayin Gangariyar Adabi Da Adabin Kasuwa A duk lokacin da aka soma batun da ya shafi Adabin Kasuwa abubuwa da dama ke zuwa zuciyar mai nazari ciki kuwa har da tunanin nan da ke nuni da cewa idan har akwai adabin kasuwa to ke nan ashe akwai wani adabin da ba na kasuwa ba. Idan kuma ka dauki ma’anar Adabin Kasuwa a luggance da ke nufin adabi na kowa da kowa ko na yayi ko abin da ke jan hankalin jama’a a kodayaushe, ke nan ana iya cewa akwai adabin da ke da akasin haka, ma’ana adabin da ba na kowa da kowa ba, adabin manya, masu ilmi ko sarauta ko daraja a tsakanin al’umma, a takaice dai adabin da ke shimfide a wani wuri domin manazarta da masana ko kuma wanda fagensa ba na kowane dan tagaja-tagaja ba ne wajen saye da karantawa da nazari, wato abin da ake wa lakabi da gangariyar adabi. Saboda haka kokarinmu a nan shi ne mu bambanta tsakanin gangariyar adabin da wanda ake wa lakabi da na kasuwa, domin ta haka ne za a gane yadda tunanin samuwar Adabin Kasuwar Kano ya tusgo, yake kuma gudana. Adabi dai kamar yadda masana suka yi nuni, kundi ko hoto ko madubi ne, (dubi Dangambo, 1984, da Gusau, 1995 da Malumfashi, 2002) da ke dauke ko nuna hanyar gudanar da rayuwar al`umma. Za a iya fahimtar irin wannan adabi ta yin la`akari da abubuwa guda biyu; Na farko shi ne harshen da ake amfani da shi, wanda yake makunshin tarihi, kuma linzamin bayyana tunani ko kuma wata manufa. Na biyu kuma ita ce fasaha, wadda ita ke bayyana tunanin da ke cikin zuciya a aikace, kamar yadda Muhammad, (2001) ya bayyana. Shi kuma Cuddon,(1999) da yake kokarin fitar da ma’anar adabi a luggance, cewa ya yi adabi na iya kasancewa abubuwa da dama da suka hada da wasan kwaikwayo da waka da gajerun labarai da rubutattun litattafai da dai sauransu. Ya ci gaba da cewa idan har aka ce wannan aikin adabi ne, to makunshiyar aikin ta bambanta da sauran kwashe-kwashe na yau da kullum, musamman idan abin ya shafi gaskiyar lamari ko kuma fadar tarihi, ke nan adabi yana da wasu siffofi da suka bambanta shi da wasu ayyuka da ba su da tasiri irin nasa. Duk da haka akwai ayyuka ko rubuce-rubuce da dama wadanda ba a yi su don su kasance na adabi ba ne, amma kuma za a iya sanya su cikin aikin adabi; saboda ingancin aikin da asalinsa ko kuma irin kyawo da kuma fasahar da aka nuna wurin rubuta shi, kamar yadda (Cuddon, 1999) ya nuna. Daga wannan hasashe za a iya cewa adabin da ke da wadannan siffofi da aka ambata a sama, shi ne ke kasancewa gangariyar adabi, akasin haka kuma sai ya zama wani abin, kila ma na kasuwa ko kuma gwanjo ko makamancin haka. Kamar yadda kowane sashe na duniya yake da gangariyar adabi, to haka a wasu sassan duniya ake da adabin kasuwa, (Market Literature) ko kuma adabin yayi (Popular Literature). To amma idan muka ce adabin kasuwa, nan zai iya kasancewa na yayi, domin kuwa duk abu daya suke tattaunawa. Duk abin da ya kasance na kasuwa to yana da alaka da yayi. Kasuwa dai wuri ne da ake saye da sayarwa na dukkan abubuwan rayuwa, duk wanda ke cikin wannan al`umma yana iya zuwa cikinta domin yin kasuwancinsa. Saboda haka adabin kasuwa wani bangare ne na adabin al’umma da kowa zai iya shiga cikin kogin ya yi iyo ko kurme; masani ko malami ko manazarci ko akasin haka. Ke nan irin wannan adabi wani abu ne ko dai waka ko wasan kwaikwayo ko kananan labarai, ko rubutattaun litattafai da aka tsara a wani zangon rayuwar jama’a, ake kuma tsintar su a tsakanin jama’ar ba tare da wani kandagarki ba. Ta fuskar sayar da su ba a yi wani tanadi na wurin da ya dace ba, ko dai a same su a kasuwa ko wurin hirar matasa ko tsakanin matan aure ko makarantu ko kuma ma duk inda jama’a ke tururuwa domin karatu da rubutu. Haka kuma idan aka ce adabi na yayi ne ana nufin cewa zai rayu daga wani lokaci zuwa wani, wato akwai lokacin da yake tashe, akwai kuma lokacin da yake sallacewa, sai a bar masana da yin rubdugu kansa, (Malumfashi, 2002). Sai dai ya kamata a lura cewa akwai lokutta kuma da ake kallon irin wannan adabin na kasuwa ko yayi a matsayin adabin talakawa ko marasa shi, wato ya kebanta ne ga wasu gungun jama’a a cikin wani zamani da ba su damu da adabin da ke gudana ba, kila ko don ba su da kudin sayen sa ko kuma ya kasance na masu gari. Idan aka fadada tunani a nan za a ga cewa shi wannan adabi na kasuwar ko yayin, saboda canzawar zamani ta sa ake masa wani sabon kallo, musamman da yake ba a damu sosai da yi masa gangariyar nazari ba. Kai ba wannan ba ai masana da dama ba su dauki aikin adabi irin wannan abin tokabo ba, shi ya sa ba a damu da sanin inda ya sa gaba ba. Sai dai ko da aka soma nazarin nasa daga baya, an kuma shigo da ayyukan adabi da mutum na iya cewa ba irin na adabin kasuwa ko yayin da aka saba ji da gani ba ne. A halin yanzu daga cikin ayyukan adabin kasuwa ko na yayi da ake da su an sanya irin kagaggun labaran da a da ba su cikin irin wannan rukuni, wato irin wadanda suka hada da labaran bincike ko tsafi ko na ban tsoro ko soyayya ko na Amurkawan dauri ko na ban dariya ko kimiyya, wato dai kagaggun labarai da milyoyin jama’a ke saye da karantawa a sassan duniya daban-daban ko da kuma ba a nazarin su a ajin adabi ko jami’o’i, musamman daga shekarun 1930. Har yau takaddama ba ta kare ba dangane ko wadannan irin ayyukan adabi na gangariyar adabi ne ko kuma kwamacala. Ga masana kamar yadda aka bayyana a (eNotes.com), irin wannan aikin adabi na kasuwa bai da nasaba da aikin kwarai, ana nuni da cewa dabara ce kurum ta samun kudi da suna, amma ba adabin da za a ta da jijiya wajen karatu ko nazari ba ne. Fasalin Adabin Kasuwa A Duniya Daga nazarin da aka gudanar an fahimci cewa adabin kasuwa ko na yayi yana tafiya ne kafada da kafada da gangariyar adabin al’umma. Shi gangariyar adabin yana kasancewa ne tsakanin masu ilmi ko hannu da shuni ko kuma iyayen kasa. Duk wani abu da ba na wannan gungun mutane ba, yawanci shi ake wa lakabi da adabin kasuwa ko yayi. Alal misali kusan duk yawancin ayyukan adabi da suke da wannan siffa a Turai ko Amurka ko sauran sassan duniya an samar da su ne tsakanin karni na 16 da 17 da na 18, daidai lokacin da fasahar dab’i ko buga littattafai ta yi tashe a duniya. Kamar yadda bayanai suka yi nuni , yawancin jama’a da masana idan ana maganar adabin karni na 16 da 17 da na 18, ana maganar gangariyar adabi ne ko na masu ilmi ko mulki ko dukiya, amma ba su kadai ne suka kwashi nasu kason ba daga rayuwar adabi, akwai adabin talakawa ko na kasuwa, wato na kowa da kowa. Ma’ana, an samar da adabin da aljihun talaka zai iya biya, ya saya don karantawa. Wannan dama ta samu ne domin an samar da injinun buga littattafai na bakin hanya da suka ba talaka damar ya sami gurbin da zai buga nasa adabin. Ire-iren wadannan ayyukan adabin su ne ake ba sunaye daban-daban da suka hada da Grub Street Literature ko Chapbooks. Wadannan lakabobi sun wanzu ne saboda la’akari da irin yadda aka samar da adabin ko wuraren da ake samar da littattafan ko kuma yanayin buga da sayar da su. Su dai Grub Street Literature su ne ayyukan adabin da aka samar daga wuraren buga littattafai da ke kan Titin Grub a Landon. Da yake a tsakanin karni na 16 da 17 da na 18 an samar da marubuta na kwarai, sai dai rubutun nasu ya fi mayar da hankali ne ga masu-fada-a-ji, bai ta’allaka ga sauran jama’a ba, ga shi kuma sun fi sauran jama’ar yawa, wannan ya sa aka shiga neman wasu da za su agaza da nasu rubutun. Sai dai yawancin irin wadannan marubuta ba su da sanayya ta zamani game da fasahar rubutu da kaga labarai, shi ya sa idan sun yi rubutu ake biyan su kudade kadan, wannan ya sa suke rayuwa a cikin talauci da kunci. Shi kansa inda suke zama a bakin titin domin yin aikin nasu na adabi, wuri ne na kazanta da yawan lalata da tashin hankali; nan ake samun barayi da mabarata da dai ire-irensu; nan ne marubutan da injinan buga ayyukansu suka daura aure. Su kuwa Chapbooks littattafai ne da ake wa lakabin littattafai masu arha, su ne ayyukan adabin da suka kasance na yayi ko na jama’a a karo na farko a wancan zamani na karni na 17 da 18. Ba ruwansu da kamfanonin hukuma ko na gwamnati, ba kuma ruwansu da manyan kamfanonin dab’i da ke neman kazamar riba. Ana kuma shirya da buga irin wadannan littattafai domin isar da sako ga talakawa ko masu sha’awar adabi, amma ba su da kudin sayen gangariyar adabin da ke wanzuwa a lokacin. Wannan damar ce marubutan da masu karatu ke amfani da ita domin su isar da sako ga sauran jama’a ba tare da kamfanin dab’i ya sa baki ba, yawancin abubuwan da ake samarwa sun hada da wake-wake da labarai da ayyukan addini da sakonnin siyasa da makamantansu. Tarihi ya nuna cewa ko da hada-hadar dab’i da rubuce-rubuce ta kankama daga karni na 15 da na 16 akwai ire-iren wadannan ayyuka masu arha, yawancinsu sun fita kasuwa ne daga karni na 17 da na 18 a Ingila, an nuna cewa sun kai kokoluwa ne a shekarar 1775, ta yadda ake samar da littattafai sama da 200,000 a kowace shekara. Wadannan littattafai sun taimaka wajen raya ayyukan adabin Ingila a wancan lokaci, sun sanya son karatu ga wadanda ba su yi nisa a karatun ba, ko suka yi karatun suka watsar daga baya. Yawancin wadannan littattafai ba su da yawan shafi, ba a yi musu bugun kwarai, sa’annan ana sayar da su da arha, daga wannan titi zuwa wancan, a maimakon wuraren da aka tanada domin sayar da gangariyar adabi. Domin ganin yadda wannan fasali ya kasance, bari mu dubi yadda na zamanin Elizabeth ya kasance a Ingila. Adabin Kasuwar Sarauniya Elizabeth A Ingila Da yake mun ga yadda wannan adabi ya kasance da kuma tasirin da ya yi tsakanin al’umma a Ingila, zai dace a nan mu fadada kan wannan batu domin mu ga yadda fasalin adabin kasuwar ya kansance ta hanyar bayar da misalai. Da yake tun da farko mun yi nuni da cewa harkar ta adabin kasuwa ta samo tushe ne daga Ingila, ya dace mu fahimci yadda al’amarin ya kasance, kafin mu shiga wasu sassan na duniya mu ga su kuma irin nasu fasalin. Daga nazarin da aka yi an fahimci cewa akwai bambance-bambancen da aka samu a tsawon zamanin aikin adabin Ingilishi, tunanin farko dai ya fara ne daga `yan Sukotlan ba daga Ingila ba, shi wannan adabin ne ya ci gaba da watayawa a tsakanin karni na goma sha biyar zuwa farko, da tsakiyar karni na goma sha shida. Wannan ne ya samar da gagarumin aikin Tottel a shekarar 1557. Shi dai wannan littafin ya shahara ne saboda dalilai da dama; Na farko dai abin da ya fi jan hankalin sababbin makaranta a wannan lokacin shi ne mafi yawan abin da littafin ya kunsa abu ne wanda ba a san da shi ba ba, haka kuma akwai hasashe ba yakini ba a cikin labarin, wanda kuma wannan shi ya fi burge masu karatun ayyukan adabin wannan lokacin, ba kamar ayyukan wasu da suka wallafa ba wadanda ko dai sun mutu ko kuma sun dade kwarai da yin rubutun, (Saintsbury,1920). Wannan zamani na Sarauniya Elizabeth kamar yadda muka yi bayani akwai aikin manyan masana a kasar Ingila, kamar fitaccen marubucin nan na wasan kwaikwayo, Christopher Marlowe da marubuta wakoki irin su Edmund Spenser, da kuma shahararrun masana kimiyya irin Francis Bacon. Marubuta da dama na wannan lokacin sun ji dadin yadda `yan majalisar Sarauniya ke amsar su in sun kai ziyara, duk da cewa suna daga cikin talakawa, (Saintsbury, 1920). Wannan kuwa ya faru ne domin tun farkon mulkin Sarauniya Elizabeth, ita ta kasance tamkar Uwar kungiyar, kuma mai bada taimako ga marubuta labaran wasan kwaikwayo, kai har aiwatar da wasan kwaikwayon ake yi a gabanta. A shekarun 1560 aka fitar da wasan Kwaikwayo na Blank Verse Tragedies, wanda za a iya cewa shi ne ya bude kofa wurin samuwar kimiyyar wasan kwaikwayon da ake nazari har zuwa yau. A shekarar 1568 ne aka aiwatar da wasan kwaikwayon a gaban sarauniya a bisa dandamali. Irin yadda aka samar da litattafai da ayyukan adabin Elizabeth ya taimaka kwarai wurin ceton adabin Ingilishi daga shiga cikin hadari na kwasar ayyukan da ‘yan kasuwa suke yi, wadanda kuma ake samarwa da tsada. Misali, a lokacin da Tottel ya fiddo littafin shi na Miscellany ba dukkan mawallafa na lokacin suka san da wannan hanyar ta fiddo da littafin kai tsaye ba, wato ba tare da an mika shi ga masu wallafar zamani ba, (Saintsbury,1920). Ta bangaren rubutun zube ma, lokacin mulkin sarauniya Elizabeth ya samu tagomashi sosai, saboda a lokacin ne aka samu ayyukan adabi wadanda suka yi tashe ko kuma suka zama na yayi, domin a lokacin malaman da ke koyarwa a Jami`ar Kambirij (Cambridge) sun taimaka kwarai da gaske wurin samar da ayyukan masana irin su Ascham da Wilson, da sauransu ta fuskar zube. Duk da cewar akwai ayyukan magabata irin su Thomas Hoby, amma dai za a iya cewa Roger Ascham shi ne ya fara bude fagen da littafinsa Toxophilus da ya rubuta aka kuma wallafa shi a shekarar 1545, amma dai littafinsa da ya fi tashe, wato Schoolmaster bai fito ba sai bayan da ya mutu, (Saintsbury,1920). Shi dai Ascham fitacce, kuma shahararren malami ne domin har sarauniyar Ingilar ma sai da ya koyar da ita a makaranta. Kamar yadda muka gani a sama, Adabin Elizabeth na Ingila ya ratsa zangunan mabambanta. Misali, mun dai ga cewar akwai ayyukan adabi da aka yi kafin lokacin Elizabeth din kamar na su Thomas More wanda ya yi rubuce-rubuce, musamman na wakoki da kuma Wyatt da sauransu. Ko a lokacin mulkin Sarauniya Elizabeth din ma, ayyukan adabi da suka fi tashe su ne wakoki da wasan kwaikwayo da kuma kagaggun labaran, amma dai masu sarrafa wakokin da wasan kwaikwayo sun fi yawa da tashe, wato kamar masana irin su Edmund Spenser da sauransu, (Saintsbury,1920). A bangaren wasan kwaikwayo da kagaggun labarai kuwa dole ne masana irin su Shakespeare su shige gaba, sannan ga Marlowe wanda zakakuri ne, wanda ayyukansa suka yi tashe, ga kuma Ben Jonson wanda ya kwaikwayi ayyukan magabatansa, ya samar da nasa. Ta bangaren kagaggun labarai kuwa akwai marubuta irin su Philip Sidney da Richard Hakluyt da Francis Bacon da sauransu da dama. Daga wannan takaitaccen bayani mun fahimci cewa a kasar Ingila ne aka samar da wannan fasali na adabin jama’a ko na kasuwa, mun dai fahimci cewa irin wannan adabi na yayi ko kasuwa ya wanzu tsakanin karni na 16 da na 17 lokacin da adabin sarauniya Elizabeth ya yi tashe tsakanin shekarar 1558 zuwa 1603. Shi dai adabin Elizabeth ba yana nufin ita Sarauniyar ce ta wallafa ko buga shi ba (kodayake ita ma ta jefo wakokinta da aka karanta, musamman On Monsiuer’s Departure), sai dai ana iya cewa a lokacin mulkinta ne aka samar da yawancin ayyukan adabin da ake wa lakabi da na yayi ko kasuwa, duk kuwa da cewa ayyuka ne na kwarai. Abin da ya sa wannan gangariyar adabi ya kasance adabin kasuwa shi ne ya samu karbuwa a hannun yawancin jama’ar Ingila a cikin kankanen lokaci, (Wikipidia.org). Duk da cewa akwai kagaggun labarai cikinsa, abin da ya fi yin tashe shi ne wasan kwaikwayo da wakoki. Adabin Elizabeth ya somo ne daga zamanin su Tottel da suka wanzu da wakokinsu zuwa masu tsara labarai na zamanin Caroline, (Saintsbury,1920). Ba wani abu ya sanya wannan zamani ya kasance na ayyukan adabin al’umma ba sai ganin manyan mashahuran marubutan da suka yi tashe a wancan zamani sun wanzu ne a lokacin, kuma har yau suna tashe a fagen nazari da sharhi. Akwai marubuta ayyukan adabi da suka hada da William Shakespeare da Christopher Marlowe da Ben Johnson da Edmund Spencer da John Fletcher da Thomas Kyd da Thomas Middleton da Thomas Nashe da John Webster da John Donne da Philip Sidney da sauransu, duk a wannan zamani suka wanzu. An kira wadannan mutane da ayyukan adabinsu a matsayin na yayi a wancan lokaci, saboda sun kasance mutane ne ko kuma ayyukansu da jama’a ke rububi. Sa’annan kuma yawancin ayyukan nasu kwafe-kwafe ne ko dai daga wasu can da aka yi a baya da suka shahara ko kuma tsakanin marubutan wannan zamani. Misali, Thomas Kyd da aikinsa na The Spanish Tragedy, shi ya ba Shakespeare hasken rubuta Hamlet, ba kuma nan kadai Shakespeare ya tsaya ba, ya shiga cikin taskar tarihin zamanin da, da kuma zamanin da ya rayu ya kwafo abubuwan da suka taimaka ya gina nasa adabin. Bincike ya nuna cewa wakokin Sonnet da Thomas Wyatt ya kaddamar su ne kuma Shakespeare da wasu na zamaninsa suka ci gaba da tallatawa, kuma sun ja ra’ayin Thomas Campion wanda ya rubuce su a takarda, aka shiga rububinsu a gidajen al’ummar wancan zamani, (Wikipidia.org). Ke nan ba kamar yadda ake tunani ba, yawancin ayyukan adabin zamanin Sarauniya Elizabeth ta 1, ba wai rashin kyau ko ma’ana ko kuma rashin goyon bayan hukuma ba ne matsalar da ta sa aka kira su na yayi, ba kuma domin ana rubutun domin talakawa ba ne kadai, sai dai domin yanayin samuwarsu, wato yadda jama’a ke ta wawason su da kuma shiga cikin harkar saye da karantawa da rubutawa, ciki har da masu gari, Sarauniya. Babban abin da ya fi fitowa fili game da wannan zamani shi ne yadda gamade da kwashe-kwashen ayyukan wasu ke taimakawa wajen gina sabon adabin da ya burge al’ummar wancan zamani. Saboda haka daga abin da aka tattaro dangane da adabin Sarauniya Elizabeth na Ingila mu iya cewa mafi yawan ayyukan adabi na kwarai, an samar da su ne a wannan lokaci, cikin wadannan shekarun ne aka samar da rubuce-rubucen adabi, musamman abin da ya shafi zane da wakoki, wasan kwaikwayo da sauransu. Adabin Kasuwar Kitsch a Jamus Duk da an ce samuwa da ginuwa na adabin jama’a ko yayi ya tusgo ne daga kasar Ingila, amma ba a kasar Ingila irin wannan rayuwar adabin kasuwa ko yayi ya samu gindin zama ba kawai, a can Jamus a cikin karni na 18 da na 19, an sami irin wannan adabi da ake wa lakabi da Kitsch. A cikin harshen Jamusanci ko Yiddish, kalmar Kitsch na nufin duk wani aikin adabi ko zane da bai da tagomashi ga masu mulki ko tajirai ko ya kasance lami ko kwashe-kwashen ayyukan wasu da aka yi a baya, (Wikipidia.org). Adabin Kitsch ya soma watayawa sosai da sosai a kasar Jamus a karni na 19, musamman a kasuwannin birnin Munich a tsakanin 1860 zuwa 1870, inda ake kiran duk wani aikin adabi da ke da arha ko na yayi ko mai karbuwa a tsakanin al’ummar da aka yi domin su ko yake ja a cikin kasuwar sayar da ayyukan adabi da sunan na Kitsch. Shi wannan adabin na Kitsch ba wai na talakawa ba ne kadai, na sababbin matsakaitan tajirai ne da suke da kudin sayen irin wadannan ayyuka, amma karfinsu bai kai na sayen adabin masu gari ba, sun yi haka ne domin a tunaninsu sayen wannan aikin adabin zai sa su tafi kafada-kafada da sarakuna da tajiran Jamus, masu sayen ayyukan adabi na kwarai. Duk da cewa Kitsch ya samu karbuwa a tsakanin jama’a, duk da haka bai wuce adabin kasuwa ko yayi ba ga sauran jama’a, musamman masu sarauta da tajirai, domin kuwa ba a yi aikin da kyau ba ko kuma takardun da aka zayyana hoton ko buga aikin adabin sun kasance na banza, ba su da aminci. Ke nan adabin Kitsch bai wuce adabin Jamus da bai da mazaunin kwarai ba a tsakanin masu mulki da tajirai ko kuma yana magana kan abubuwan da ba su ne aka sa gaba ba a tsakanin al’ummar, ko kuma dai gwanjon adabi ne ko adabi ne da ke kwaikwayon wani adabi, ba tunani ko kirkirar wanda ya samar da shi ba ne ko da kuwa ya samu karbuwa tsakanin wasu gungun mutane, (Cuddon, 1999). Saboda haka kamar yadda muka gani a baya, Kitsch wani nau`in adabi ne da wanzu a kasar Jamus wanda yake nufin duk wani aiki na zane ko aikin adabi wanda masu mulki ko masu kudi ba su yi na`am da shi ba. An samar da wannan adabi ne mai suna Kitsch domin a mai da martani ko ya yi jayayya da ayyukan adabi da aka samar a karni na 18 da na 19 wanda yake ana masa kallo na masu mulkin kasaita da fitattun masu kudi ne. Shi dai wannan salon adabin yana da matukar alaka da adabin da ke tashe ko kuma na yayi, ba wani abu ya sa aka kira shi da haka ba kuwa sai ganin cewa aikin da aka yi na zanen ko aikin adabin ba a yi shi yadda za a iya cewa ya ginu ko tsaru ba. Ke nan adabin Kitsch an samar da shi ne domin matsakaitan masu kudi ko masu mulkin da ba su kai su yi gogayya da wadanda suka yi fice ba, duk da haka su ma wadanda suka yi ficen, ganin karko ko kuma yanayin da wannan adabi ya fita da yadda mutane ke rububinsa ya sanya suka fara saye da karanta shi. Za mu iya cewa adabin Kitsch ya kasance na kasuwa ne kawai domin ganin fasalin yadda aka samar da shi ba mai aminci ba ne, ma`ana kayan da aka yi aiki da su wurin samar da wadannan zane ko ayyukan adabin ba su da inganci, kuma an samar da su ne ganin cewa wadanda suke sayen shi ba su iya sayen manyan ayyukan adabi, wato wannan yana da saukin kudi ga masu sayen shi, kusan kowa zai iya sa kudi ya saye shi Wannan ya sa ake danganta adabin Kitsch, (Wikipedia.org) da duk wani aikin adabi ko zane da aka samar maras kyau, wanda zai iya biya wa mai saye da bukatarsa, ma`ana zai kashe masa kishirwa daga abin da yake so ya gani ko ya karanta, musamman cikin wata sabuwar kama ko siffa, a ayyukan adabin wanda aka kwaikwaya daga wanda ya gabace shi ko suke rayuwa tare. Wannan ne ya sa irin wannan tsari ko fasali ya sha suka daga masana, fitattun daga cikin su kuwa su ne; Gabriel Thuller da wanda ya goyi bayan cewa wannan adabi na Kitsch bai dace da zamanin ba, domin ba gwanaye ke yin sa ba. Haka kuma wani fitaccen masani a fannin zane Georg Wilhelm Friedrich Hegel ya jaddada cewa zane-zanen wannan zamani yana da alaka da wani yanayi na lokacin da aka samar da shi, ba abin damuwa ba ne, in dai ya samu karbuwa daga masu karatu. Adabin Kasuwa Na Larabawa Shi ma adabin Larabci kamar sauran ya sha kwaramniya har zuwa lokacin da aka samar da na zamani wanda yake da alaka da na Yammacin Dauri, (Neo-Classical), wanda ya nemi ya canza fasalin adabin Larabci gaba daya, wato wanda za a ce ya samo kayan aikinsa daga wanda ya gabata, kamar su Maqamatul Hariri da Alfu Laylah, saboda haka su wadannan na zamanin sai ya kasance sun koma ko dai suna samo kayan gininsu daga wadannan ko kuma suna juyar aikin marubuta adabin Yammacin Dauri ne kai tsaye, suna mai da su na Larabci. Marubuta da dama a kasashen Siriya da Lebanon da Egypt sun samar da ayyukansu na adabi daga Maqama, fitattun daga cikinsu akwai Al-Muwayhili da littafinsa na The Hadith of Issa ibn Hisham a zamanin mulkin Ismail a Egypt, wanda wannan littafin shi ne za a iya cewa ya haifar da wani sabon zango a adabin Larabci. Wannan yanayi shi ya ba marubucin nan dan kasar Lebanon,Goergy Zeidan, wanda kirista ne da ya yi hijira zuwa kasar Misira, bayan zanga-zangar da aka yi a Damaskus a 1860 damar fitar da basirarsa a fili sosai. An dai fara buga labarin Ziedan a farkon karni na 18 a cikin jaridar kasar Misira, wato Al-Hilal. Ba wani abu ya sa aka kira ayyukan wadannan mutane da na yayi ko na kasuwa ba sai ganin cewa su ne ayyukan da mutane suka fi sha`awa, saboda irin yadda aka samar da su da harshen da kalmomin da aka yi amfani da su da kuma yadda aka tsara su, sai kuma ficen da marubutan suka yi. Sauran wadanda suka kasance a cikin wannan tsarin sun hada da Khalil Gibran da Mikha`il Na`ima. Amma dai masana da dama na adabin Larabci sun bayyana cewa an fi ganin Littafin Zaynab na Muhammad Husayn Haykal da Adraa Denshawi na Muhammad Tahir Haqqi da kasancewa ayyukan adabi na farko a wannan karni masu kama da ayyukan adabin jama’a ko kasuwa, fiye da wadancan da muka ambata a baya. (dubi karin bayani a Arabic Literature daga Wikipidia: The free encyclopedia). Daga nazarin da aka gudanar an fahimci cewa litattafan adabin yayi ko na jama’a na Larabci sun fi bayyana rayuwar iyali, misali ayyukan Naguib Mahfuz na Cairo Trilogy, inda ya siffanta rayuwar iyali. Adabin Kasuwa Na Onitsha A Nijeriya Kamar yadda wannan fasali na adabin kasuwa ya samu karbuwa da watsuwa a sassan Turai da Amurka da kasashen Larabawa, haka ma inda Turawan suka yi mulkin mallaka fasalin ya samu zaunuwa, ko dai a cikin harshen ‘yan gida ko kuma cikin harshen bakin da suka zo cikin Afirkawa. Misalin da za a iya kawowa a nan shi ne na Adabin Kasuwar Onisha da ya wanzu cikin harshen Ingilishi, masana da dama sun bayyana yadda wannan fasali ya samu ya kuma wanzu . Haka kuma kamar yadda Okoro (2002) ya bayyana, adabin Kasuwar Onisha an yi shi ne a wani zamani a farkon karni na 20 a kasar Inyamurai a Nijeriya da ya kasance, wanda a lokacin an sami al’ummar Igbo da ba su da isasshen ilmin boko, wasu sun kammala Elementare, suka sami aikin malanta ko suka zama masinjoji ko sakatarori a ofisoshin gwamnati a Onisha, sai dai da yawa daga cikinsu sun fahimci ba za su iya rayuwa da irin wannan aiki ba, domin ba albashin kwarai, wasu kuma da ba su sami aikin ba, bayan sun kammala karatu, sai abubuwa suka cunkushe musu, domin wadanda suka yi karatun ma ya suka kare, su kuma masu aikin suna aiki, ga shi karo karatun na da matsala a wannan lokaci. Wannan ya sa wasu da dama suka fantsama cikin kasuwar Onisha ko dai a matsayin ‘yan tireda ko masu koyon sana’ar hannu ta kafinta ko teloli ko magina ko makera. Da yake yawancinsu, sun yi boko to ba su son su zauna haka nan ba abin karatu, ga shi kuma ayyukan adabin Ingilishi da ke makarantu ya fi karfin aljihunsu, sai suka shiga rubuta abin da ya zo ga ransu domin su karanta tsakaninsu; ire-iren wadannan rubuce-rubuce ne aka kira da Adabin Kasuwar Onisha. Ke nan kamar yadda Obiechina (1973) da Okoro (2002) da Malumfashi (2005) suka yi bayani daga nasu binciken ba wani abu ba ne Adabin Kasuwar Onisha sai kananan littatafan nan da aka samu da yawan gaske a kasuwar ta Onisha da wasu sassa na Kudancin Nijeriya a tsakiyar shekarun karni na 20, suka ce, an tsara da shirya da kuma sayar da su domin talakawan Onisha da ba su yi zurfin karatu ba. Wannan adabin na Kasuwar Onitsha, wanda shi ne za a iya kira da wanda ya fara samar da wurin buga litattafai, garin Onitsha dai yana kudancin Nijeriya, mutanen wurin wadanda Igbo ne sun shahara wurin kasuwanci, a wani lokaci ma ana iya cewa kasuwar ta Onitsha ita ce mafi shahara a Afirka. An fara samar da littafin adabi a wannan wuri cikin shekarar 1947, babu wani tsari ko fasali da aka bi domin samar da wadannan litattafan, hasali ma dai an fara samar da su ne domin cike wani gibi da aka samu na karatu da ko rubutu, saboda a lokacin samuwar addinin kirista da `yan mulkin mallaka sun taimaka wurin samar da makaranta a garin Onitsha domin su yi aiki, ko kasuwanci ko kuma su samu wata damar ta ci gaba. Wannan shi ya haifar da masu buga litattafai na bakin hanya ko na kasuwa da suka fara samar da wannan adabi. Wanda za a fara cewa ya fara samar da wadannan litattafan na kasuwar Onitsha ba wai kawai ya yi fice ba ne, a lokacin, mutum ne kuma wanda daga baya ya shahara ta fuskar ilimin boko, wanda kuma yana ma daga cikin wadanda suka wakilci jama`arsu, kuma kwararre wurin hada magunguna (Pharmacist), wato Cyprian Ekwensi, wanda ya tashi daga wallafa littattafan adabin kasuwa ko yayi zuwa wallafa gangariyar adabi. Littafin da aka fara samarwa a lokacin shi ne; Ikolo Wrestler na Cyprian Ekwensi, an samar da shi ne daga tatsuniyoyin Igbo, wanda aka buga a wurin sai da litattafai na Tabansi Bookshop da kuma dayan, When Love Whispers na soyayya. An sake samar da wasu bayan shekara biyu wato; Tragic Niger Tales, mawallafin litattafan wani malamin makaranta ne, yana ba da labarin aure ne ko ma`aurata. Su dai irin wadannan litattafai da aka samar sun yi tashe da suna a duk fadin garin Onitsha da kewaye, musamman a wurin matasa `yan makaranta, maza da mata. Wannan ya sanya wasu marubutan suka biyo baya, don ganin irin amsuwar da wadannan litattafai suka yi. Wannan kuma shi ya sanya aka shiga samar da sababbin masu buga litattafan na bakin hanya, da kuma na cikin kasuwa, shi ya sanya har zuwa shekarar 1960 abin ya habaka, wanda ya sanya masu buga litattafan suka watsu har zuwa garuruwan Aba da Fatakwal da Inugu da sauran manyan garuruwan gabashin Nijeriya. Akwai dalilai da dama da suka sanya aka samu wannan bunkasuwar a garin Onitsha kamar yadda Obiechina (1973) ya bayyana. Wasu daga cikin dalilan kuwa har da kasancewar kasuwar garin Onitsha ta yi fice ba a gabashin Nijeriya ko Najeriyar, kai har fadin Yammacin Afirka. Saboda haka idan aka lura za a ga cewa Adabin Kasuwar Onitsha ya kasance da siffofi da alamu da dama, wadanda suka yi kama da wadanda aka gani a kasar Ingila, ko a Jamus ko na kasar Larabawa, domin dai an yi shi saboda masu karamin karfi su samu abin karantawa, ke nan ba ya da tsada, sannan yana da saurin fahimta, ma`ana harshen da aka yi amfani da shi mai saukin fahimta ne, kuma an yi shi ne musamman saboda talakawa ko wadanda ba su tare da gangariyar adabi. Haka kuma ba su maganar komai sai labaran soyayya da tatsunniyoyi da rayuwar aure da kuma bunkasuwar kasuwanci. Sai dai wannan bai zama abin mamaki ba, domin suna yin la`akari ne da bukatun masu karatun su. Matakan Gane Adabin Kasuwa Abin lura a nan shi ne, irin wannan fasali da Adabin Kasuwar Onisha ya dauka shi ne Adabin Elizabeth a Ingila ko kuma na Kitsch a Jamus, da na Larabawa ya dauka. Ke nan babban matsugunin kowane aikin adabi da aka yi wa lakabi da na kasuwa ko na yayi bai wuce irin fasalin da ya tashi da shi ba, ko dai mai arha ne ko kayan da aka yi amfani da su wajen samar da shi ba su da inganci ko kuma masu yin sa da karanta shi wasu gungun jama’a ne, ba na kowa da kowa ba ne. Gungun mutanen na iya kasancewa masu kudi ko talakawa ko iyayen gari, sannan uwa uba kuma wannan adabi na da lokacin da yake rayuwa, ya kuma mutu, kamar yadda Malumfashi (2005) ya bayyana. Domin gane wannan fasali na adabin kasuwa bari mu dubi adabin Elizabeth na Ingila da kyau, ya dai yi tashensa ne cikin shekara 45, wato daga 1558 zuwa 1603, shi kuma na Kitsch da ke a Jamus, ya rayu ne daga 1860 zuwa 1870, wato shekara 10 ya yi a duniya ko kuma na Onisha daga 1947 zuwa 1975, ya shekara 28 ke nan a raye. Saboda haka, fasalin adabin kasuwa yana zuwa da siffofi da kamannu masu yawa. Sai dai domin takaitawa muna iya cewa shi ne adabin da ake samu a cikin kasuwa, ba wai ana nufin kasuwar dole ta kasance irin wadda muke tunani ba, duk inda jama’a suke hada-hadar saye da sayarwa, shi ake nufi da kasuwa a nan. Idan ana son a gane shi da kyau sai a dube shi da wadannan fasalce-fasalcen : Adabin kasuwa zai iya kasancewa mai saukin karantawa, wato mai jimloli marasa sarkakiya. Haka kuma nahawunsa zai kasance sassauka, ba mai nauyi ba. Haka yawancin wannan adabin yakan kasance bai da yawan shafuka, ma`ana, bai daukar lokaci za a iya karance shi. Ga shi kuma yana da arha, kusan kowa zai iya sanya kudi ya saya ba tare da wani tarnaki ba, (Obiechina, 1973). Jigogin Adabin Kasuwa Sakonni ko kuma jigogin da wadannan ayyuka na adabi suke isar wa sun bambanta ne daga wannan gari zuwa wancan ko kuma daga wannan kasa zuwa waccan, amma dai abu muhimmi shi ne kowane da abin da yake son ya isar ga al’ummar. Alal misali daga nazarin da aka yi wa Adabin Elizabeth da ya wanzu a zamanin sarauniya Elizabeth ta Ingila a tsakanin karni na 16 da na 17, ya shahara ne ta fuskar wasan kwaikwayo da kuma wakoki, sannan kuma kusan yawancin marubutan suna yin rubutunsu ne domin kare martabar masu mulki da kuma tajirai. Wannan ne ma ya sanya tun daga farkon mulkinta, Sarauniya Elizabeth ta kasance tamkar uwar kungiyar, kuma mai ba da taimako ga marubutan, ta yadda kamar yadda muka nuna a wasu lokutta har aiwatar da wasan kwaikwayon ake yi a gabanta. A adabin Larabawa ma musamman kuwa wakokin lokacin jahiliyya, jigonsu bai wuce fadakarwa ta zamantakewa ba, ko kuma rayuwa irin ta yau da kullum ba, sai kuma jigon wakokin yawace-yawace da kuma wakoki na kabilanci da kusan kowace kabila ke da shi. Amma bayan bayyanar Musulunci da wayewar kai sai abin ya canza, domin kuwa litattafan adabin Larabci a lokacin sun fi bayyana rayuwar iyali, misali ayyukan Naguib Mahfuz na Cairo Trilogy, Shi kuwa adabin Onitsha na Nijeriya jigoginsu sai suka sha bamban da na sauran sassan duniya, domin kuwa a lokacin da aka fara samar da shi a 1947, sai ya kasance ya ta’allaka ne wajen ba da labaran soyayya da suka shafi aure da kuma kasuwanci, a sassan wannan yanki na Nijeriya. Ke nan a iya cewa yawancin labaran na Adabin Onisha ba su maganar komai sai labaran soyayya da tatsuniyoyi. Daga baya kuma sun tattauna abubuwa da suka shafi yadda rubuta wasika da yadda ake koyon Ingilishi da kuma tallata haja da makamantansu. Daga binciken da aka gudanar an dai fahimci cewa yawancin jigogi na yawancin Adubban Kasuwa a kowace kasa, suna kasancewa abin da al’ummar wannan wuri ne suka fi so da ko sha’awar gani ko karantawa a daidai lokacin da ake aiwatar shi, ko dai na soyayyar ne ko kuma na kasuwanci, ko rayuwar iyalin ko kuma na masu mulkin, kusan a ce wannan shi ya fi rinjayar masu karanta ko sauraron wannan adabi na wannan yanki. Marubutan Adabin Kasuwa Marubuta wadannan litattafan dai kamar yadda muka nazarci wasu daga cikinsu, shahararru ne a fagen da suke, wasu kuma fitattun malamai ne a makarantun zamanin. Misali, marubuta adabin Elizabeth, wasunsu sun yi fice matuka, marubuta kamar Roger Ascham, wanda yake fitacce kuma shahararren malami ne, domin har sarauniyar Ingilar ma sai da ya koyar da ita a makaranta, an haife shi a shekarar 1515. Sannan ga masana irin su Edmund Spenser da William Shakespeare da Christopher Marlowe da Ben Johnson da Edmund Spencer da John Fletcher da Thomas Kyd da Thomas Middleton da Thomas Nashe da John Webster da John Donne da Philip Sidney, dukkansu fitattun marubuta ne wadanda suka yi tashe a wannan zamani na Elizabeth da kuma bayan wannan zamani. Idan muka dubi marubutan Adabin Kitsch na Jamus, shi ma ya samu fitattun masu zane da rubutu a lokacin, fitattun daga cikinsu kuwa su ne; Gabriel Thuller da Matk A. Cheetham da kuma George Wilhelm Friedrich Hegel. A Adabin kasuwa na Larabawa da muka gani, shi ma ya zo da nasa fitattun marubutan da suka shahara kuma suka samar da litattafai a lokacin, fitattu daga cikinsu akwai Muhammad Husayn Haykal da Muhammad Tahir Haqqi da Naguib Mahfuz da kuma Al-Hamadhani da fitaccen aikinsa na Maqamatil-Hariri da dai sauransu. Haka ma a kasuwar Onisha wanda za a fara cewa ya fara samar da wadannan litattafan na kasuwar Onitsha ba wai kawai ya yi fice ba ne, mutum ne wanda ya shahara ta fuskar ilimin boko daga baya, wato Cyprian Ekwensi, wanda daga baya ya tashi daga wallafa kananan litattafai zuwa manya. MakarantaAdabin Kasuwa Makaranta Ayyukan adabin kasuwa su ma sun bambanta, wasu talakawa ne kadai ke sauraro ko kallo, yayin da wasu kuwa kamar na Elizabeth ya kasance masu sarautar Ingila din suna daga cikin masu yi da sauraron wannan adabi. Sai da ta kai ma wasu ayyukan idan aka yi su, sai a ware wanda za a kai wa sarauniyar, da kuma wanda za a gabatar a bainar jama’a. Saboda haka sai ya kasance daga cikin masu sha’awar wannan aikin; wato ko dai wasan kwaikwkon ko kuma wakoki sun fito daga masarautar Ingilar. Wannan ne ma ya sa marubuta da dama na wannan lokacin sun ji dadin yadda `yan majalisar Sarauniya ke tararryar su. Shi kuwa adabin Kitsch ba wai na talakawa ba ne kadai, na sababbin matsakaitan tajirai ne da suke da kudin sayen irin wadannan ayyuka, amma karfinsu bai kai na sayen adabin masu gari ba, sun yi haka ne domin a tunaninsu sayen wannan aikin adabin zai sa su tafi kafada-kafada da sarakuna da tajiran Jamus, masu sayen ayyukan adabi na kwarai. Shi dai adabin kitsch an samar da shi ne domin matsakaitan masu kudi ko masu mulkin da ba su kai su yi gogayya da wadanda suka yi fice ba, duk da haka su ma wadanda suka yi ficen, ganin karko ko kuma yanayin wannan na Kitsch din ya sanya suka fara sayen shi. Shi kuwa Adabin Kasuwa na Onitsha ya fi shahara ne a wurin matasa `yan makaranta maza da mata, da kuma masu karamin karfi don su samu abin karantawa wanda baya da tsada, ta yadda kowa za iya sa kudi ya saya ba tare da wani tarnaki ba. Kasuwancin Adabin Kasuwa Duk aikin Adabin da ya kasance ana samun shi a wasu wurare da ba na saida litattafan ko aikin adabi ba ne to wannan adabi zai kasance na kasuwa ne ko yayi ko kuma mai tashe ne. Duk adabin da ake bi kasuwa-kasuwa, da shaguna, da wajen `yan tireda, da masu tura kaya a baro, ko wurin `yan kura, kai ko kawai a hanya, ana nemansa don a saya , adabin kasuwa ne, (Malumfashi, 2002). Wannan ya zama gaskiya idan aka yi la’akari da irin wuraren da ake sayar da littattafan zamanin Sarauniyar Ingila Elizabeth Ta Daya, yawancin littattafan ana sayar da samunsu a bakin shagunan da marubutan suka bude don tallata hajarsu, ko dai a cikin birnin London ko kuma kauyukan da ke makwabtaka da shi. An fi ganin su a bakin titi, ‘yan kalilan ne suka samu shiga shagunan sayar da littatafai na zamani. Wasu kuma kamar yadda muka bankado, ana saye da rarraba su ne ta hannu, tsakanin wannan marubuci ko marubuciya zuwa wancan marubuci ko marubuciya. Sai dai za a iya cewa wasu kuma ba ma sayar da su ake yi ba ana aiwatar ko gabatar da su ne a gaban jama’a a lokuttan bukukuwa ko tarurrukan marubuta. Kusan irin wannan fasali ne aka gani a adabin Kistch na Jamus, yaswancin zane-zanen da ayyukan adabin da suka yi tashe a wannan karon an samar da su ne a kasuwar birnin Munich, inda yawancin masu adabin suka rayu. Saboda haka za a iya cewa adabin da zane-zanen duk ‘yan kasuwa ne, don haka a bisa titi ake samu da sayar da su a tsakanin al’ummar wancan zamani. Idan kuma aka lura da tsarin saye da sayarwar littatafan Adabin Kasuwar Onitsha za a fahimci shi ma ya bi irin wannan fasali na baya. Tun da farko dai an yanke wa adabin cibi ne a kasuwar Onitsha, nan yawancin marubutan suka wanzu, sai kuwa wasu sassa na garuruwan Aba da makwabta. Saboda haka yawancin littattafan ana saye da sayar da su ne a wadannan kasuwanni. Ba kuma wani wuri na musamman aka tanadar musu ba, inda ‘yan kasuwar ke saye da sayarwar nan ne littattafan suka samu matsuguni. Samuwar Adabin Kasuwar Kano Daga abubuwan da aka gani a babin da ya gabata ke nan ba abin mamaki ba ne idan aka ci karo da Adabin Kasuwa a Amurka ko Turai ko Rasha ko cikin kasashen Asiya ko Larabawa, kai ko ma ina ne a cikin duniya. Hakan na faruwa ne ganin cewa ai ba kasashen Turawa ko wadanda suka ci gaba ne ke da damar su samar da adabin kasuwa su kadai ba, haka kuma ba dole sai harshen Ingilishi ko wani harshen da ya sami ci gaba kadai ne zai iya samar da shi ba; kowace kasa, kuma kowane irin harshe zai iya samun adabin kasuwa a cikin wani zangon rayuwar adabin. Domin inganta bincike, ya dace mu bi salsala, mu ga yadda aka samar da abin da yawanci ake kira Adabin Kasuwar Kano tsakanin Hausawa. 4.1.1 Rayuwar Farko : 1984-1989 Abin da aka dade ana kira Adabin Kasuwar Kano ya samo asali ne a farkon shekarun 1980, kuma wannan shekaru a kasar Hausa ko Arewacin Nijeriya baki daya, shekaru ne masu tarihi a bangaren samuwar ilmin boko da rubutu. A daidai wannan zangon rayuwa ne daliban UPE, shirin gwamnatin tarayya da aka soma daga 1976 domin ba kowane yaro damar samun ilimin furamare kyauta, suka fara shiga kasuwar rubutu da karatu da rububin abubuwan karantawa, domin daliban farko na wannan shiri sun baro firamare a shekarar 1982, daga wannan lokaci har zuwa 1984, an yaye dalibai har kashi hudu. Saboda haka an samar da sababbin makaranta da suke bukatar abin karantawa. Haka wannan zango ya zo daidai da lokacin da babban kamfanin wallafa da dab’i a kasar Hausa wato NNPC ya soma shiga tasku, ya soma sukurkucewa da neman durkushewa. A daidai wannan lokaci kamfanin NNPC ya daina buga littattafan hira da nishadi, bayan kuma ga dubban matasa da aka yaye daga shirin na UPE sun antayo cike da shaukin irin wadannan littattafai da babu su. Wannan shiri na UPE, duk da cewa bai zaunu da gindinsa ba, amma ya samar da sababbin makaranta a farkon shekarun 1980. Kuma a daidai wannan lokaci sai ga shi tattalin arzikin Nijeriya ya kara inganta, saboda gano man fetur da aka yi, ya kara wa kasar hanyar samun kudaden shiga masu yawa. Bincike kuma ya nuna cewa duk lokacin da irin wannan harka ta kasance haka, wato ga masu ilmi gwargwado, sa’annan ga ‘yan kudi a hannun jama’a, kamar yadda muka gani a fasalin Adabin Kasuwar Kitsch na Jamus, sai ka ga hanyoyin samar da adabi, mai kyau ko maras kyau, suna wadatuwa. Da yake tun can azal akwai kayayyakin rubutu da dab’i gwargwado a kasar Hausa, sai ya ba matasa damar da suka tsunduma cikin wannan harka ta wallafa littattafai ba ji ba gani, kamar yadda Furniss, (2001) ya yi nuni. Sai dai ko kafin shekarar 1984 da littafin Rabin Raina na Talatu Wada Ahmed ya fito kasuwa akwai birbishin rubuce-rubuce na soyayya a kasar Hausa. Idan ba a manta ba a shekarar 1978 kamfanin NNPC ya shirya gasa da ta samar da littattafai a shekarar 1980, kamar su Mallakin Zuciyata na Sulaiman Ibrahim Katsina da So Aljannar Duniya na Hafsat Abdulwaheed da kuma Amadi na Malam Amah na Magaji Dambatta, (Haruna, 2009). Sai dai abin lura shi ne wadannan littatafai daga gasa suka fito, wato sai da aka yi shiri da tsari, haka kuma na hukuma ko kamfani ne, don haka sun biyo tsari da ingancin da ya bambanta su da adabin kasuwa. Ke nan za a iya cewa wadannan littatafai na gasar 1978 sun dai nuna hanya ne na irin adabin da zai biyo bayansu, ba su ne farkon adabin na kasuwa a kasar Hausa ba. A daya bangaren kuma an danganta littafin Rabin Raina na Talatu Wada Ahmed da tushe ko tubalin samuwar adabin kasuwa a kasar Hausa saboda yanayin da ya samu da kuma yadda ya shiga kasuwa. Shi ma ba wai zama aka yi domin assasa wannan fage na adabin kasuwa ba tattare da shi ba. Kamar yadda a karo na farko wadda aka danganta aikinta da Adabin Kasuwar Kano, Talatu ta bayyana wa Mujallar Garkuwa (2000) yadda ta samar da littafin, ta ce ita ba ta san da wani abu wai shi adabin kasuwa ba lokacin da take rubuta littafinta. Ta kara da cewa ta dai rubuta shi ne a lokacin tana makarantar WTC Katsina, tana aji uku, wato wajajen shekarar 1980, ta kuma rubuta shi ne daga gyauron labaran da take ba ‘yan uwanta dalibai lokacin suna makaranta can da dare kafin su yi barci. Bayan ta gama sakandire ne ta fitar da shi ta hanyar aika shi gidan rediyon tarayya Kaduna domin a karanta a shirin Shafa Labari Shuni, amma aka dade ba a karanta shi ba, daga baya ta mika wa wani kamfanin bakin hanya da ake kira Ogwu a Kaduna domin ya buga mata shi. Kamfanin Ogwu ya buga, ya kuma shiga sayar da littafin da ya ga mutane sun dami suna son su karanta. A lokacin da Kamfanin Ogwu ya shiga sayar da littafin, ita Talatu tana Kwalejin Ilmi ta Kafanchan wajen karo ilmi, a can ne wata kawarta ta zo da littafin, tana yi mata bayanin yadda littafin ya yi kasuwa, ita ba ta ma sani ba. Wannan dadin abin da ya faru ya sa ta koma gida ta ji abin da ya auku. Mahaifiyar Talatu ta ba ta kudin da aka samu, ta yi murna kwarai da ganin arzikin da wannan littafi ya jawo mata. Daga wannan lokaci ne ta shiga sake buga littafin, ana watsawa a cikin kasar Hausa, ta yadda abin ya dinga ba ta mamaki na ganin cewa mutane, musamman masu sayar da littatafai daga ko’ina a fadin kasar Hausa ke kira ko yo sakon don Allah ta aika masu da kwafe 500 ko dubu ko dubu biyu ko ma fiye. Fitar wannan littafi da yanayin da ya samu kan sa lokacin bugu da sayarwa da kuma hanyoyin da aka bi aka samar da shi ya nuna wa sauran marubuta cewa ashe akwai wata hanyar rubuta da wallafa littattafai ba dole sai ta bin kamfanonin bugu da wallafa na gwamnati ba. Saboda haka daga samuwar wannan littafi na Rabin Raina a shekarar 1984 za mu iya cewa akalar adabin hira ko kagaggen labari ta soma sauyawa, kuma a iya cewa daga wannan lokacin ne Adabin Kasuwar Kano ya fara ginuwa. Sai dai abin da ke da muhimmanci a nan shi ne ba wai zama aka yi ba domin a tsara da gina wannan fasali na Adabin Kasuwar ta Kano ba, abu ne da ya kasance caccakude, kuma tattare da abubuwa mabambanta da suka hada da : Tun da farko dai akwai matsalar abubuwan karantawa a makarantu da kuma tsakanin sababbin makaranta kamar yadda muka yi bayani. Ga halin da kamfanin NNPC ya shiga daga farkon shekarun 1980 da rashin buga littatafan hira. Ga kuma daruruwan ‘yan makaranta da wadanda suka kammala makarantun, sun kuma rubuta littattafai masu yawa, ba wurin buga su, balle a san da su. Shirin gidan Rediyon Tarayya Kaduna na Shafa Labari Shuni da wasu da dama a gidajen rediyon jihar Kano da Katsina da Sokoto da wasu wurare da dama ya taimaka wajen fito da wadansu daga cikin marubutan da ke boye. Bugun littafin Talatu na bakin kasuwa da yadda ya sami karbuwa ya sanya wasu,kila suka ce su ma bari su gwada bugawa da sayarwa. Saboda haka littattafan da ake ta yayatawa a halin yanzu a matsayin wadanda suka biyo bayan littafin Talatu daga 1984, ba wai shawara suka yi da juna ba, kuma ba su san wani na yin irin wannan aiki ba, kamar yadda bincike ya nuna a halin yanzu. Ke nan jawabin da Malumfashi, (1994) ko wanda Adamu, (1996) da Adamu (2000) suka yi na lissafa littatafan da suka biyo na Talatu kamar haka ba daidai ba ne, sai dai daga littafin Talatu na Rabin Raina sai: Ibrahim Hamza Abdullahi da Soyayya Gamon Jini a 1986. Idris S. Imam da In Da Rai a 1987. Balaraba Ramat da Budurwar Zuciya a 1987. A.M Zaharadden da Kogin Soyayya a 1988. Idan so cuta ne, na Yusuf M. Adamu a 1989. An yi wannan hasashe bisa hujjar da ta nuna cewa babu wani bincike da ya tabbatar da jeruwa da daidaituwar wannan tsari ko kuma wani bayani da ya ce an tattauna tsakanin wadannan mutane na biyo sahun Talatu Wada. Bari mu yi nazarin batun da kyau, tun da farko dai garuruwan marubutan daban-daban suke, Talatu na Kaduna, Ibrahim Hamza na Kano, Idris S. Imam kuwa tun 1984 aka buga littafin nasa ba wai a 1987, Balaraba kuwa ko kafin ta shigar da littafinta na Budurwar Zuciya a layin adabin kasuwa ta fuskar shiga kungiyar Raina Kama, an riga an buga littafin a Zaria,(Gaskiya Corporation a 1984). Haka shi ma Zaharradeen a Kano yake, shi kuwa Yusuf Adamu yana dalibta a Sakkwato ne ya shigo da nasa littafin. Haka kuma daga binciken da aka gudanar an fahimci cewa ko kafin Ibrahim Hamza Abdullahi da littafinsa na Soyayya Gamon Jini a 1986, an samar da Hannunka Mai sanda 1 na Kamarradeeen Imam a 1985, me ya sa ba a shigar da shi cikin layin na farko ba ? Haka kuma a tsakanin 1984 da aka samar da littafin Talatu, ba wai littattafai hudu ne suka yi tashe ba kurum guda 13 ne. Ke nan ba wata kungiya ba ce ko kuma wani taro aka yi ba aka ce a samar da wannan abu da aka kira Adabin Kasuwar Kano daga baya. Shi kuma Malumfashi (1994) da ya kira shi da wannan suna, ya yi haka ne daga abin da ya gani masu kama da juna tsakanin littattafan da irin wadanda aka samar a Onisha kamar yadda ya bayyana daga baya, (Malumfashi, 2004). Kamar yadda muka gani can baya, rayuwar adabi takan shiga cikin wani sauyi ne na wani lokaci, daga baya kuma ta kasance cikin wani tsari na daban, irin wannan shi ne ya faru da abin da aka kira Adabin Kasuwar Kano yanzu. Sai dai wani abu da za a yi la’akari da shi, shi ne, yawancin matasan da suka yi tashe a wancan lokaci a wannan fage ba su yi amfani da kamfanonin dab`i da ake da su don bayyanar da ayyukansu na adabi ga jama’a ba, ba don komi ba kuwa sai don ba wani kamfani da ya damu ya buga ire-iren wadannan litattafai. Ba kuma wai don ba su da kasuwa ko kuma ba su sami karbuwa ba a tsakanin al`umma ba, a`a, a tsakanin shekarun 1978-1982 ba abin da ya fi tashe da karbuwa irin labaran da wasu suke rubutawa, suna aika wa gidajen rediyoyi daban-daban ana karantawa. Ba wani abu ya jawo hakan ba sai ganin litattafan da aka samar daga gasar da aka shirya a 1978 da suka samar da litattafan soyayya na farko da za a iya kira `yan zamani, sun yi tasiri ga rayuwar irin wadannan matasa. Sai dai da alama amfani da aka yi da kafar rediyo, wadda ta sanya kagaggun labarai irin wadannan suka sami martaba, ba wai kawai tsakanin wadanda suka yi boko ba kurum, har ga wadanda aikinsu shi ne sauraron rediyo, ba su iya karatun ba. Bisa wannan tafarkin aka shiga samar da sababbin marubuta, wasu ta hanyar kwaikwayon abin da aka rubuta, suka aika gidajen rediyoyin, wasu kuma ta sake wa tatsunniyoyi da labaran Hausa fasali, wasu ko ta kwaikwayo ko daukar fasalin wasu labaran Ingilishi ko fassara kai-tsaye ko kuma nade fina-finan Indiya da na Turawa zuwa takarda. Cikin dan lokaci kankani sai ga kabod-kabod na gidajen rediyoyin nan sun cika makil, wasu ma suka shiga konawa, wanda ya sa masu rubutun suka shiga guna-guni idan ba a karanta nasu labaran ba. Sai dai kuma wadanda Allah ya tarfa wa garinsu nono daga cikin wadanda aka karanta nasu a gidajen rediyoyin, sai ga shi sun fara samun suna da daukaka. Wannan ya jawo wasiku suka shiga gilmawa zuwa gare su, ana yaba masu, ta haka kuma aka ga cewa ga wata kafa ta samu ta kashe waccan kishirwa ta rashin labaran Hausa da ta addabi matasa, ta yadda a tsakanin shekarar 1984 zuwa 1998 marubuta da sababbin littatafai suka baje kasuwarsu a kasar Hausa. Idan aka yi nazari sosai za a ga ko da Talatu ta bayyana a 1984 a Kaduna, ba a Kadunar ta tsaya ba, domin littattafan sun baje duk fadin kasar Hausa, musamman a Kano da suka dasa rayuwarsu. A Kanon akwai irin littafin Talatu Wada da ya riga ya shiga kasuwa shi ma kafin ma bayyanar na Talatu, wato Wasiyar Babakere na Ibrahim Sale Gumel, a kuma wannan shekara ta 1984, an sami dan uwan na Talatu, wato In Da Rai Da Rabo na Idris S. Imam. Saboda haka ko da Kamarradeen ya shigo da nasa littafin a 1985, ba dole ba ne ya san da abin da Talatu ta yi ko kuma sauran da suka riga nata shiga kasuwa; musamman ganin cewa da ne ga marigayi Abubakar Imam, kuma yana aiki da kamfanin Huda-Huda da ke Zaria, wadanda su ne mawallafansa. Yadda Kano ta shigo cikin harkar da litatattafan da ‘yan Kanon suka samar bai rasa nasaba da suna da tashe da littafin Talatu da na Idris da Ibrahim suka yi a kasuwar Kanon. Littattafai tara ne suka wanzu a wannan lokaci a tsakanin 1986 zuwa 1989. Ga alama kuma su ne suka sanya Kano ta sami karbuwa da Tagomashi a wannan harka ta yadda daga baya Gusau ta shigo sahu, Kanon ta sake bayyana, daga can kuma sai Sakkwato, tare da Yusuf Adamu. Ga dai jerin irin wadannan littattafai da suka kasance na farko ko suka kasance jijiyar da ta gina wannan sabon yanayin rubutu da muke nazari. Daga nazarin wadannan littattafai an fahimci cewa marubuta mata guda biyu suka wanzu, sauran kuma duk maza ne. LAMBA LITTAFI MAWALLAFI SHEKARA 1 Wasiyyar Baba Kere Ibrahim Saleh Gumel 1983 2 In Da Rai da Rabo Idris S. Imam 1984 3 Rabin Raina Talatu Wada Ahmed 1984 4 Hannunka Mai Sanda 1 Kamaruddeen Imam 1985 5 Soyayya Gamon jini Ibrahim Hamza Bici 1986 6 Daji Bakwai Abba Ado Dandago 1987 7 In Da Rai… Idris S. Imam 1987 8 Kogin Soyayya Ahmed Mahmoud Zaharaddeen 1988 9 Turmi Sha Daka Kabiru Ibrahim Yakasai 1988 10 Budurwar Zuciya Balaraba Ramat Yakubu 1989 11 Soyayya Dankon Zumunci Bashir Sanda Gusau 1989 12 Tsalle Daya… Idris S. Imam 1989 13 Idan So Cuta Ne Yusuf M. Adamu 1989 Balaga: 1990 zuwa 1995 Nazarin rayuwar Adabin Kasuwar Kano a zamanin da muka kira na balaga ya fito mana da siffofi mabambanta. Da farko dai lokaci ne da littattafan da suka samu wanzuwa daga shekarar 1984 suka samu karbuwa tsakanin makaranta da masu buga littatafan da kuma masu sayar da su. A daidai wannan zamani ne na shekarar 1990 zuwa 1995 za a ce Adabion Kasuwar Kano ya shiga tashen balaga, mnarubuta da suka yi suna da karbuwa a tsawon shekaru, suka bayyana. Cikin su irin wadannan marubuta akwai Dan Azumi Baba Chediyar ‘Yan Gurasa, wanda ya wallafa littatafai guda 9 a cikin wannan tsakani da kuma Aminu Abdu Na’inna da ya fitar da littatafai guda 6. Akwai kuma irin su Ado Ahmad Gidan Dabino da Bala Anas Babinlata da Badamasi S. Burji da suka wallafa littattafai 4 kowanensu, haka kuma akwai marubuta irin su Balaraba Ramat da Yusuf Lawan Gwazaye da Alkhamees Bature da suka fitar da littattafai bibiyu kowane. Saura kuwa, irin su Ibrahim Mandawari da Ibrahim Sheme da Bashir Sanda, kowane ya fitar da littafi guda. A bangaren mata kuwa, a wannan lokaci ne aka sami fitowar manyan marubuta mata da suka yi tashe a cikin wannan harka da dadewa, marubuta irin su Bilkisu A. Funtua da Hadiza S. Aliyu da Hawwa Aminu da Atika S. Sidi da suka antayo daga shekarar 1994. Abin la’akari dangane da wannan zamani na balaga shi ne, yawancin littattafan da aka samar daga cikin sama da 110 da aka wallafa a wannan tsakani sun fito ne daga taskar kungiyar Raina Kama da muka yi bayani a baya, wadda ke karkashin jagorancin Ado Gidan Dabino. A daidai wannan lokaci za a fahimci cewa wanda ya fi tashe a cikin wannan kungiya shi ne Dan Azumi Baba, wanda ya fito da wani salo na labaran aljannu da dodanni da muridai, sai ko Ado Gidan Dabino da ya dauki fagen soyayya, wanda kuma ya fi kowane daga cikin marubutan shahara, saboda alakarsa da ‘yan jarida da suka yayata shi da shi kuma irin rawar da ya taka wajen tallata kansa da kuma kwazonsa wajen gina labari. Daga jadawalin marubutan da muka samu kai hannu kan su, mun fahimci cewa nan ma maza suka fi shahara a fagen rubutun, domin kuwa mata 12 ne suka tusgo, alhali maza 60 suka wallafa littattafai a wannan zangon Adabin Kasuwar Kanon. Dubi yadda jadawalin littattafan wannan zamani suka kasance daga binciken da aka gudanar a Rataye 7.1. Tsufa Da Hayayyafa: 1996 zuwa 2001 Daga lokacin da kasuwar littatafan Adabin Kasuwar Kano ta yi tashin gwauron zabo daga shekarar 1995 zuwa 1996 amon wannan sabon tsarin rubutu ba inda bai kai ba, wannan ne ya sa harkar ta koma irin ta wani babban kamfani. Kungiyoyin marubuta da suka bullo daga shekarar 1990 kamar su Kungiyar Matasa Marubuta da Kukan Kurciya da Raina Kama da Jigon Hausa duk a cikin birnin Kano da Ruwan Dare a Kaduna da kuma Kungiyar Matasa Marubuta ta Jihar Sakkwato a Sokoto (Adamu, 2006) su ma suka kara wa wannan harka martaba da daukaka a idon mutane. Haka kuma kungiyoyin makaranta irin su Dakata Readers Association da Kabuga Readers Association da Tudun Wada Readers Association da Hotoro-South Readers Association duk a cikin Kano sun agaza wajen tabbatuwar wannan harka. Daga cikin kuma masu sayar da littattafan da suka agaza sosai a daidai wannan lokaci akwai irin su Alhaji Baba na Jakara City Bookshop da Alhaji Musa Danbala na Sauki Bookshop kuma Alhaji Garba Mohammed na Garba Mohammed Bookshop da ke Sabon Gari Kano. Wannan aure na marubuta da makaranta da masu sayar da littattafai da kuma kungiyoyi daban-daban, su ne za a iya cewa kashin bayan wannan fasali na Adabin Kasuwar Kano, wanda ya sanya harkar ta hayayyafa, ta kuma bunkasa fiye da yadda ake tsammani. Wannan ne ya sa aka sami yawancin tarin littattafan adabin Kasuwar Kanon masu yawan gaske da suka kai sama da 400, a daidai wannan zango da muka tattauna. Daga wannan zango ne mata suka fara kunno kai sosai da sosai, domin kuwa an sami marubuta mata sama da 50 . ’Ya’ya Da Jikoki: 2002 zuwa 2008 Littattafan da aka yi wa lakabi da ‘ya’ya da jikoki su ne kagaggun labaran da aka samu daga shekarar 2002 zuwa shekarar 2008. Nazarin da aka yi wa wadannan littatafai an fahimci cewa duk da sauye-sauyen da aka samu na litattafan Adabin Kasuwar Kano a wannan zango, ba a bar fasalin da aka saba ba, wato na yin rubutun bisa tsarin ni na rubuta, ni na gyara, ni na kai inda za a buga mini, ni kuma ke sayarwa da kaina. An dai samu wasu sababbin marubuta ne da irin nasu fasali, sun bullo domin taka rawa irin tasu. Sai dai kamar yadda muka fahimta, wannan ba ya rasa nasaba da ganin cewa tsofaffin marubutan da suka yi tashe a baya, wasu sun watsar da rubutun, ko dai saboda sun yi aure ko kuma yayinsu ya wuce, wasu kuma sun koma wata sana’ar, musamman shirya fina-finai, ga shi kuma bukatar litattafan ba ta kau baki daya ba, wannan ya jaza fitowar sababbin marubuta domin nuna irin tasu fasahar. A wannan zangon kamar yadda muka nazarta, marubuta mata sun sami filin baje kolinsu. Daga cikin littattafan da muka samu kai hannu kan su marubuta mata sama da 76 ne suka yi tashe. Wannan shi ne karon da mata suka yi ambaliya sosai. Haka kuma daga hirar da na yi da makaranta littattafai a wannan zango sun nuna sha’awarsu kan rubuce-rubucen matan, kila wannan shi ya kara sa yawan marubuta matan. A cikin wadannan jerin litattafan na wannan zango, wadda ta fi yawan littattafai ita ce marubuciya Sa’adatu Saminu Kankiya tana da 14 da suka fita a wannan zango, wannan kuma alama ce da ke cewa litattafanta sun fi samun karbuwa ga makaranta. Mai yiwuwa saboda suna dauke da labaran da suka shafi soyayya da aure, wadanda bisa ga nazarin da aka gudanar su ne suka fi tashe a wannan zango. Akwai kuma wasu marubutan mata da suka fi shahara a wannan zango da suka hada da kamar su Saliha Abubakar Zariya da Hadiza Salisu Sharif da Amina Abdullahi Sharada da Zainab Birged da su Sa’adiya Kankiya da Rahmatu Hassan Sanda. Duk da cewa yawancin wadannan sababbin marubuta ne, duk da haka akwai fitattu da suka yi tashe, wasu tun daga haihuwa da kuruciya, ba su kuma daina ba har zuwan ‘ya’yan da jikoki. Cikin irin wannan fasali akwai irin su Rahma A. Majid da kuma su Hafsat A. Sodangi da Zuwaira Isa da Bilkisu Ahmed Funtua, da dai sauransu da dama. Daga cikin maza kuwa, litattafan Nazir Adam Salihi su ne suka fi karbuwa da tashe, ya rubuta guda 13 a cikin wannan zango da muka yi nazari. Shi kuma jigon litattafansa sun sha bamban da na sauran marubutan wannan zamani, domin wani lokaci za ka ga labaran nasa na soyayya ne, amma cikin ban takaici, wata sa’a ma da ban tsoro. Sai dai irin yadda yake wasa da harshe a cikin littattafan nasa ya sa yawancin masu karatu ke biye da shi a kullum. Maje El-Hejeej Hotoro shi ma wani marubucin ne da litattafansa da kuma tauraruwarsa, musamman a wannan zango suka yi tashe. Shi ma din yakan yi amfani da jigon soyayya ko kuma jigon ban tsoron da jan hankali. A daidai kuma cikin wannan zango ne aka soma ganin bullar sabon tsarin rubutun Adabin Kasuwar Kanon. Da farko dai an sami marubutan da suka canza akalar rubutun nasu domin ya dace da zamani musamman ganin cewa an sha suka da takaddama kan yawaitar rubuce-rubuce kan soyayya da aure. Ire-iren wadannan marubuta sun hada da Bala Anas Babinlata da Ibrahim Sheme da Sakina A. Aminu da Rahma A. Majid da Saliha Abubakar Abdullahi da sauransu da dama. Daga nazarin da aka yi, an fahimci cewa yawancin wadannan marubuta ko dai ilminsu na zamani ne da suka nisa a ciki ya sa littattafan nasu suka yi armashi; wato kamar Ibrahim Sheme da Rahma Majid da suka nazarcin adabin duniya daban-daban, da yake sun yi digiri, Ibrahim Sheme har digiri na biyu ya yi, ko kuma sun dai tsara littattafan ne domin su dan sha bamban da wadanda aka saba ji da gani a wannan zango bisa sani, domin sun ga yadda aka dade ana ta kai-kawo game da neman sauyi, wato kamar su Babinlata da Rahma da Saliha da Abdullahi da Mukhtar Yaron Malam. Duka dai alamu ne da ke nuni da cewa sabon yanka rake na Adabin Kasuwar Kano ya shigo kasuwa. Baya ga wannan kuma ga gasar kaga littatafai da ta kunno kai, musamman ta Bashir Karaye da aka fara a shekarar 2007, wadda ta ba da dama aka sake daga martabar rubutun da kuma marubutan wannan zango. A nan ana maganar irin su Ibrahim Sheme da Lawan Barista da Maje El-Hajeej da suka cinye gasar rubutun a cikin wannan zango. Siffofin Adabin Kasuwar Kano Da yake ana tariyar abin da ya wuce ne game da wannan fage na Adabin Kasuwar Kano, ta yaya za a iya gane aikin adabin da za a ce na Kasuwar Kano ne idan an gan shi, ko kuma wadanne siffofi ne za a ce su ne na Adabin Kasuwar Kano? Amsar na da sauki ganin cewa an riga an yi shimfida game da Adabin Kasuwa na bai daya a cikin babi na uku. Saboda haka abin da aka yi a nan shi ne a fitar da kamannun da su ne za a iya gani a ce wannan na daga cikin siffofin Adabin Kasuwar Kano. Haka kuma yin hakan ya zo da sauki domin daga cikin siffofi na bai daya da aka gani can baya game da adabin kasuwa da manazarta suka ayyana, an fahimci cewa yana dauke da manyan siffofi guda hudu: Adabi ne da ke yin tashe a wani zamani daga baya ya kau. Adabi ne da yake gudana tsakanin wasu gungun mutane kurum ba kowa da kowa ba. Adabi ne na kasuwa ko na yayi. Adabi ne da ake alakanta shi da wani wuri ko gari ko zamani ko yanayin da ya sami kansa. Idan muka dubi littatafan adabin da ake yi wa lakabi da Adabin Kasuwar Kano kamar yadda muka zayyana a baya, za a ga cewa sun shiga cikin sahun adabin kasuwa kamar yadda suke zayyane a sama. Tun da farko wannan harka ta samo asali ne a wani ayyanannen lokaci, wato daga farkon shekarun 1980, musamman a tsakanin shekarar 1983 zuwa 1984 ya zuwa farkon karni na 21, inda daga lokacin ya fara salamcewa, domin harkar fim ta sha gabansa. Saboda haka shi ma kamar sauran ayyukan adabin kasuwa irinsa, ya samu wani lokacin da ya fara da kuma lokacin da ya girma, kuma zai kasance ya koma cikin taskar tarihi a cikin wani lokaci mai zuwa. A halin yanzu dai an samu sama da shekara 25 ana aiwatar da wannan tsari na adabin kasuwa a kasar Hausa Haka kuma adabi ne na gungun matasa, ba na kowa da kowa ba, yawancin masu yin sa da karanta shi ba su wuce ‘yan shekara 18 zuwa 35 ba. Idan aka dubi samuwar wannan fasalin rubutu daga 1983, marubuta biyu ne daga cikin 13 da ake da su, suka haye shekara 25, wato Balaraba Ramat da Kamarradeen Imam, saura duk ‘yan kasa da 25 ne. Sa’annan kuma adabi ne na ‘talakawa’, wato wadanda suke da karamin karfi, ba dole sai masu kudi ko tajirai za su iya sayen sa ba, kamar yadda yake a gangariyar adabi. Da yake kuma adabin talakawa ne, shi kuma adabin talakawa yana zuwa da nasa siffofin na daban; daga ciki zai kasance mai saukin karantawa, wato mai jimloli marasa sarkakiya. Haka kuma nahawunsu zai kasance sassauka, ba nannauya ba. Ke nan wannan adabin yakan kasance bai da yawan shafi, ma`ana, bai daukar lokaci za a iya karance shi. Idan aka dubi nazarin da aka yi a sama za a ga cewa wannan fasali ya fito fili. Yawancin littattafan sun kasance masu saukin karantawa ga dan firamare ko sakandare, haka ma wanda ya yaki jahilci. Idan aka koma kan batun cewa adabin kasuwa ana alakanta shi da wani wuri ko zamani ko gari ko yanayi, za mu iya cewa lallai haka abin ya faru da Adabin Kasuwar Kano. Mun dai ga cewa zamanin Sarauniya Elizabeth ya haifar da Adabin Kasuwar Elizabeth a Ingila, na Kitsch ya haifar da Adabin Kasuwar Kitsch a Jamus, kasuwar Onitsha ta haifar da Adabin Kasuwar Onitsha a Nijeriya. Saboda haka sanya wa Adabin Kasuwar Kano sunan na kasuwar Kano ya danganta ne da ganin cewa Kano tana da fitacciyar kasuwa wadda daga ko`ina ana zuwa cin wannan kasuwa. Kamar yadda kasuwar Onitsha ta yi fice a duk fadin Afrika, ta yadda duk wani littafi da aka wallafa a wannan bangare za a iya samun shi a wannan kasuwa ya ba da damar a sa masa wannan suna. Ko da kuma aka gama cin kasuwar a kasar Inyamurai, a tsakanin shekarun 1947 zuwa 1969, kasuwar ta watse a 1975, sai aka yi wa wannan rayuwa da abin da ta haifar lakabi da Adabin Kasuwar Onitsha, (Okoro, 2002). Saboda haka ba sai an fada ba, tun da Kano birni ne na kasuwanci, sa wa adabin kasuwa lakabin Kano, an yi shi ne da sani da kuma amincewar haka abin yake a tarihin adabin duniya. Kasuwanci dai a birnin Kano ya sami gindin zama sama da shekaru dubu da suka wuce. Birnin Kano ya kasance matattarar kasuwanci da dadewa tsakanin kasashen Hausa, tun zamanin cinikin bayi. Saboda haka ko da wadannan litattafai suka soma bubbugowa daga Kano da Kaduna, Kano suka yada zango. Kuma daga shekarar 1984 da Talatu Wada ta fiddo littafinta, wanda shi ne ya yi wa wannan fasali mazaunin farko, Kano aka kawo shi domin sayarwa ga sassan duniya a can kuma ya samu karbuwa sosai. Daga wannan lokaci ne Kanawa da ke bin wannan sana’a suka shiga sayar da litattafan, suna sarar duk wani littafi da ya fito, su dinga biyan marubuta a hankali. Wasu masu sayar da litattafan suka shiga buga litattafan da kansu, wato su bayyana wa marubuci irin labarin da suke so a rubuta, su kuma sa kudi su buga, su rarrabar, su sami riba, (Adamu, 1998 da 2002). Shafuka Rashin yawan shafuka kamar yadda bincike ya nuna bai rasa nasaba da dalilai da dama. Na farko, tunanin yawancin marubutan irin wadannan littatafai bai cika cokali ba, don haka ko sun tashi yin tunani mai zurfi don su tsawaita labarin, sai ka ga zaren ya tsinke, sun kuge ga shafuka 40 zuwa 80. Daga baya ne dabarar tsinka labaran ta shigo ga marubutan, domin su ninka ribar da suke samu. Wannan shi ya haifar da littafi na daya da na biyu, ko uku, ko ma fiye, kamar yadda aka sami irin wannan siffa a ayyukan adabin Onitsha. Kila abin da wani zai tambaya shi ne me ya sa littattafan za su kasance marasa yawan shafi? Kamar yadda bincike ya nuna, yawancin marubutan da suka yi tashe daga 1984 zuwa 1991, an fahimci cewa ba su yi zurfi a ilmin zamani ba. Alal misali Ado Gidan Dabino, bai yi karatun zamanin ba, makarantar dare ya yi, daga baya ne ya wuce zuwa karo ilmi, shi ma bayan ya zama wani abu a cikin fagen rubuta irin wadannan littattafai. Su kuwa sauran matan da suka shahara a wannan fage ba su wuce karatun firamare da sakandare ba, irin su Zuwaira Isa da Bilkisu Ahmed Funtua, sun isa misali. Wasu kuma sun yi tishin karatun ne bayan sun yi shekaru da gama firamare, har an yi musu aure, suka koma fagen rubutun. Irin su Zuwaira Machika, sun zama misali. Saboda haka duk yadda irin wadannan marubuta ke son su tsawaita littatafan, sai a ga abin ya faskara. Sa’annan kuma uwa-uba, siffar irin wadannan littatafai ke nan, ba a yi su domin yawan shafuka ba. Yanayin Bugu Duk adabin da bai da wani kamfani takamaimai ko wurin dab`i da hukuma ta san da shi, ko kuma bai bin tsari da doka na dab`i kamar yadda aka tanada, to wannan adabi, na kasuwa ne. Duk wani adabi da ba a san shi a manhajar karatu ta firamare ko sakandire ko wani mataki na karatu daban da wadannan ba, ko kuma ya bi tsarin shigar da shi cikin manhajar ba, wato ta bin doka, to wannan adabi na kasuwa ne. Idan haka ne to da wuya irin wadannan littattafai su kasance ba na kasuwa ba. Wannan ya zama haka ne ganin cewa ana buga su ne a bakin titi ko wurin buga littattafai da ke makare a cikin kasuwa. Haka kuma ba sa shiga cikin manhajar karatu kamar yadda hukuma ta tsara domin da ma ba gangariyar ba ne. Idan har aka ga ana karanta su a sakandare ko jami’a to wani shiri ne tsakanin marubutan da malamai, ba wai hukumomin makarantun sun san da shirin ba. Ba wannan ba ma, hatta wadanda ke wallafa littattafan ba suna wallafa su ne domin su yi karko ne ba, a dai buga da takarda mafi sauki, da bango mafi arha, a kuma injuna marasa caji da tsada. Domin fahimtar wannan siffa sosai, ya dace a gane cewa takarda kala biyu ce ake amfani da ita wajen wallafa ire-iren wadannan littattafai; akwai news print da kuma bond. Ita newsprint tun asali ita ce ake amfani da ita, domin ta fi arha. A daidai lokacin da aka soma wannan harka, da naira dari biyar zuwa dubu daya za a iya sayen takardar da za a buga kwafe dubu zuwa dubu biyu, Saboda haka duk tsadar littafin bai wuce naira 5 zuwa 10 daga haihuwa zuwa kuruciya, a kuma samu sami riba in an sayar. Hatta bangon littafin ba da takardar kwarai ake buga shi ba, saboda a rage tsadarsa. Baya ga wannan masu bugawar ba su da kayan aiki na kwarai da suka hada da injuna da tawada da makamantan su. Ke nan duk wani littafin da ya sami kan sa a cikin irin wannan hali, to za a ga bugun zai kasance ba na kwarai ne ba, kamar dai yadda muka ga haka game da littattafan Grub Street a kasar Ingila da Kitsch a Jamus. Sako Ko Jigo Sakon da litattafan Adabin Ksauwar Kano ke isar wa a fili suke, domin kamar yadda (Adamu, 2006) ke cewa, kusan marubuta na farkon-farkon, wato irin su Talatu Wada Ahmed mai (Rabin Raina) da sauran su, soyayya ce suka tanada a cikin littattafan nasu, ba don komi ba sai don su ne ke shere masu karatu. Shi ya sa Adamu (2006) yake nuni da cewa kusan tun daga bangon litattafan za a fahimci jigonsu, saboda daga bangayen, jigon zai bayyana cewa wadannn litattafai na soyayya ne, domin ba abin da za ka gani daga ‘In Da So Da Kauna’, sai ‘Dace Da Masoyi’, sai ‘Kwabon Masoyi’, sai ‘So Tsunstu’, sai ‘Ruwan Soyayyar Zuciya’, sai ‘Kibiyar Soyayya’ da dai sauransu da dama masu dauke da irin wadannan sunayen. Da tafiya ta yi tafiya sai aka fara samun wasu masu magana kan auren da yanayin auren Hausawa da matsalolin da ke tattare da su. Ya zuwa shekarar 2002 zuwa 2008 sai ya kasance sakonnin ko jigogin litattafan sun canza fasali gaba daya, domin kuwa sama da kashi casa`in da takwas na litattafan sai suka koma ba su maganar komai sai labaran soyayya, kamar dai yadda suka faro daga farko. Sannan kuma daga abin da masu karatu suka fada game da sakonni ko jigogin litattafan sai aka fahimci cewa soyayya da rayuwar zaman aure su suka fi tashe, sai kuma zamantakewar yau da kullum, (Bashir, 2009). Sai dai domin a fidda wannan fasali fili, ya dace mu nazarci sakonni ko jigogin wadannan littattafai sosai. Tuni dai (Adamu, 2006) ya taba gudanar da makamancin wannan aiki, sai dai littattafan da ya nazarta ba su wuce 463 ba. Wannan nazari ya dora bisa wancan, an samu ganin cewa sakonnin da ke cikin litattafai sama da 712 da aka yi nazari sun kasance mabambanta, duk da haka dai jigon soyayya shi ne kan gaba. Ga yadda jadawalin ya kasance. JIGO ADADIN LITATTAFAI Soyayya 250 Rayuwar Aure 62 Zamantakewa 164 Rikici 30 Kishi 27 Yaudara 25 Biyayyar Iyaye 12 Ban Dariya 8 Siyasa 12 Hakuri 20 Wadanda Ba A Tantance Ba 102 Kamar yadda Adamu (2006) ya nuna daga nasa binciken kimanin kashi 35 ne kadai suke da jigon Soyayya, sauran kashi 65 kuwa suna magana ne kan wasu jigogin na daban, amma duk da haka wai manazarta na ta sukar marubutan, da cewa sun ta’allaka ne kan jigon soyayya. Amma daga nawa binciken, ana iya ganin cewa kaso mafi tsoka daga cikin littatafan da aka nazarta kusan 712 na soyayya sama da 250 ne, sai sauran jigogin da marubutan sukan tabo. Daga binciken da aka gudanar sauran jigogin da wadannan marubutan sukan tabo sun hada da Rayuwar aure (misali, Matsalar Mu Ce na Fauziyya D. Sulaiman,) da Kishi, (misali, Bakin Kishi na Muhammad Lawan Barista) da Yaudara, (misali, Mayaudariya na Abubakar Umar Mani) da Rayuwar Duniya, ( misali, Zaman Farko na Ibrahim Birniwa) da Hakuri, (misali, Mahakurci, na Sa’adatu Saminu Kankiya) da Ban Dariya, (misali, Namijin Kunama na Balarabe Abdullahi Yola) da Biyayyar Iyaye, (misali ,Tsakanin Da da Mahaifi na Sanusi Hashim,) da Rikici, (misali, Sadauki Diknar na Abdulkadir Mu’azu Isa,) da Tsaro, (misali, An Yanka Ta Tashi na Bala Anas Babinlata da dai sauran su. Su ma idan aka yi musu nazarin kwakkwafi za a ga cewa wasu daga cikin su na soyayyar ne kodayake ba kai tsaye ba, amma dai suna da alaka da soyayyar, musamman wadanda suka shafi rayuwar aure da kishi da makamantan su. Bincike ya nuna cewa an samu wadannan canje-canje ne dangane da fasalce-fasalcen wadannan littattafai da muke magana kai daga mabambantan dalilai. A cikin shekara bakwai da fara wannan harkar adabi, wato lokacin da shekarar 1991 ke karatowa, abubuwan sun bunkasa sosai a wannan fage. Wannan sabon salon rubutu ya cika da batsewa, ya kuma fantsama a ko’ina a kasar Hausa, musamman wurin mata da matasa. Haka kuma ya kasance rubutun ya tashi daga kagawa da aka fara gani a rubucen-rubucen farko, sai ya koma kwashewa ko gamade. Marubuta litattafan sai suka koma kwaso kayan cikin adabin daga fina-finan Indiya da majigin Turawa da Larabawa da kuma litattafan soyayyar Turawa suna mayar da su nasu. Daga shekarar 1991, lokacin da su Ado Gidan Dabino suka yi ruwa, suka yi tsaki, harkar buga litattafan ta koma tamkar kamfani, kungiyoyi daban-daban suka shiga bullowa, tare da shugabanni da mambobi da kuma masu tallata litattafan da suke wallafawa. Wannan kamar yadda muka yi bayani a baya ya taimaka sosai wajen tabbatuwar wannan harka, wanda ya sa aka samar da litattafai sama da 1,860 zuwa shekarar 2007. (Furniss, 2007). Bayan samun gindin zama da Adabin Kasuwar Kano ya yi, har ta kai ga sun kakkafa kungiyoyi domin tafiyar da harkokin rubuce-rubucensu, sai kuma sauran jama`ar gari suka bi sahu. Manazarta da `yan jarida da kuma sauran mutane suka fara tofa albarkacin bakinsu kan yanaye-yanayen wannan adabi. Wasu suke yabawa, yayin da wasu kuma sun nuna irin yadda rubuce-rubucen suka dagule, musamman idan aka hada su da gangariyar aikin adabi da suka gabata. Da dama mutane sun nuna rashin jin dadinsu na yadda batsa da mugayen kalamai suka fara gurbata al`adun Hausawa daga cikin rubuce-rubucen Adabin Kasuwar Kano. Su kuma marubutan a koyaushe kokarin kare kansu suke yi daga zarge-zargen da ake masu. Sukan nuna cewa jigon soyayya da suka dauka don gina ayyukansu, suna yi ne saboda ya dace da zamani ne. Wannaan ya sanya a lokacin idan mutum ya duba kasuwannin litattafai na Hausa ba abin da zai tsinkaya sai dalar litattafai daban-daban na soyayya, irinsu; In Da Rai… ko Rabin Raina ko Budurwar Zuciya ko Furen Soyayya ko Idan So Cuta Ne. Akwai kuma irin su Garin Masoyi da Marurun Soyayya da So Marurun Zuciya da Duniya Bautar Mata da sauransu dai da dama. Masu Sayarwa Kamar kowane irin tsarin adabin kasuwa, Adabin Kasuwar Kano ya zo da nasa fasalin sayar da littattafan. Sai dai shi ma kamar sauran ana sayar da littatafan ne a manyan kasuwannin kasar Hausa da suka hada da Kano da Kaduna da Jos da Sakkwato da Zaria da Gusau da Gombe da Bauchi da Minna da Katsina da sauransu da dama. Wadanda suka taimaka a wannan fage kamar yadda Adamu (2002) ya bayyana su ne dillalai ko masu bugawa da sayarwa a kasuwannin Kano da sauran sassan kasar Hausa, musamman da yake a wancan lokaci ba wani shago da ake da shi da ke tallata littatafan Hausa kurum. A birnin Kano, inda nan ne harkar ta zaunu sosai akwai irin su Alhaji Baba, mai Jakara City Bookshop da Alhaji Musa Danbala, mai Sauki Bookshop da Alhaji Garba Mohammed, mai Garba Mohammed Bookshop. Da farko dai wadannan shaguna suna dillancin littatafan ne da masu rubutawa ke kawo musu su sayar, amma daga baya sai suka koma masu wallafawa da bugawa su da kansu. Za su sayi littafi hannun mai shi ko kuma su sayi wanda ba a buga ba, su su buga suna sayarwa. Daga nan Kano harkar ta koma sauran biranen, su ma da manyan dillalansu da suka hada da irin su Alhaji Abdullah a kasuwar Sakkwato da kuma shagunan littattafai irin su Anti Bilki Bookshop a Funtua da makamantansu da dama. Haka wannan harkar ta ci gaba da wanzuwa har ta kai an samar da shaguna da suke ba sayarwa kurum suke yi ba suna bayar da hayar wadannan littatafai ga wadanda ba su da karfin sayen littattafan ko kuma ba su son su tara su jibgi a gida. Masu Karatu Masu karatun wadannan litattafan kamar yadda muka gani a can baya mafi yawa matasa ne. Sai dai domin mu fahimci inda aka fito dangane da wannan bangare na bincike, na ga ya dace a bi diddigin game tunanin masu karanta wadannan littatafai. Hanyar da aka bi domin yin haka, ita ce ta rarraba takardun neman bayanai domin a ji daga bakin masu karatu game da abubuwa da dama da suka shafi wannan harka. Daga cikin takardun neman bayanai sama da 400 da aka rarraba a sassan garuruwan kasar Hausa, kamar Katsina da Kano da Kaduna da Sakkwato da Zariya da Gombe da Dutse da kuma Bauchi, an samu guda 350 da suka dawo hannu. An yi amfani da wadannan takardun bayanai domin gane matsayin makaranta wadannan littattafai. Ga dai fasalin rabe-raben takardun neman bayanin da aka samu. JADAWALI NA FARKO: BAYANAI DANGANE DA SHEKARU SHEKARA WADANDA SUKA MAIDO ADADI 1-20 40 Kashi 2 21-40 287 Kashi 97 41-60 23 Kashi 1 JIMILLA 350 Kashi 100 Kamar yadda muka gani a sama, mafi yawan masu karanta wadannan litattafan da suka amsa tambayoyin neman bayani shekarunsu sun kama daga shekara 21 zuwa shekara 40. Sai kashi daya wadanda shekarunsu suka kama daga shekara 41 zuwa shekara 60. sai sauran da shekarunsu ya kama daga 1 zuwa ashirin. JADAWALI NA BIYU: BAYANAI DANGANE DA ADDINI ADDINI WADANDA SUKA MAIDO ADADI MUSULUNCI 350 Kashi 100 KIRISTANCI 0 0 JIMILLA 350 Kashi 100 Haka kuma an dubi addinan wadanda suka maido bayanan daga wadanda suke karanta wadannan litattafan. Su kuma kashi 100 cikin dari dukkan su musulmi ne. Wannan shi ma bai zama abin mamaki ba, musamman ganin cewa yawancin garuruwan da aka rarraba takardun na muslmi ne. JADAWALI NA UKU: BAYANAI DANGANE DA KABILA KABILA WADANDA SUKA MAIDO ADADI HAUSA/ FULANI 350 Kashi 100 SAURAN KABILU - Kashi 0 JIMILLA 350 Kashi 100 Daga takardun da muka samu karba na neman bayanai mun fahimci cewa mafi yawan wadanda suka yi mana bayanan Hausawa da Fulani ne, domin kamar yadda ya zo a teburi na uku, kashi dari na daga masu karanta litattafan Hausawa da Fulanin ne. Wannan ko bai rasa nasaba da cewa Hausawa da Fulani ke zaune inda aka rarraba wadannan takardun neman bayanai. Sannnan kamar yadda ya zo a teburi na hudu a kasa, mai nuna matakin ilimin wadanda suka amsa tambayoyin namu, mun ga cewa matakin ilminsu bai yi zurfi ba, domin sun kama daga matakin sakandare, mai kashi 27 cikin 100 ne, zuwa matakin karatun difloma ko NCE, ko kuma wata babbar shedar karatu, masu kashi 70 cikin 100. Sai dai akwai wadanda suka yi digiri masu rabin kashi da kuma wadanda suka yaki jahilci masu kashi daya. Sai kuma masu ilmin addini kurum, masu kashi daya su ma. JADAWALI NA HUDU: BAYANAI DANGANE DA MATAKIN ILIMI MATAKIN ILIMI WADANDA SUKA MAIDO ADADI ILIMIN ADDINI 14 Rabin Kashi ILIMIN SAKANDIRE 120 Kashi 27.1 N.C.E/DIFLOMA 148 Kashi 70 DIGIRI 10 Rabin Kashi YAKI DA JAHILCI 58 Kashi 1 JIMILLA 350 Kashi 100 Dangane da garuruwan da wadanda suka amsa tambayoyin suka fito, wannan binciken ya nuna cewa Katsina (da kashi 40) da Kano (da kashi 34), nan ne aka samu yawancin amsar tambayoyin bayanan da aka nema. Katsina dai ba abin mamaki ba ne, domin mai binciken a nan yake da zama, ke nan ana iya samun takardun neman bayanin da suka dawo masu yawa a nan. Kano dama can ake sayar da litattafan, saboda haka ba abin mamaki ba ne don an samu amsar tambayoyi da dama daga can. Haka akwai sauran sassan garuruwan da aka dawo da amsoshi kamar yadda yake a teburi na kasa. JADAWALI NA BIYAR: BAYANAI DANGANE DA GARI GARI WADANDA SUKA MAIDO ADADI KATSINA 142 Kashi 40 KANO 92 Kashi 34 GUMEL 2 Rabin Kashi SOKOTO 40 Kashi 10 BAUCI 2 Rabin Kashi GOMBE 2 Rabin Kashi ZARIYA 25 Kashi 5 KADUNA 45 Kashi 10 JIMILLA 350 100 JADAWALI NA SHIDA: BAYANAI DANGANE DA JINSI JINSI WADANDA SUKA MAIDO ADADI Namiji 112 Kashi 30 Mace 178 Kashi 65 Ba Jinsi 60 Kashi 5 JIMILLA 350 Kashi 100 Dangane da jinsin wadanda suka mayar da takardu kuwa, daga binciken da aka gudanar a teburi na 6, ya nuna cewa kashi 65 daga cikin wadanda suka mayar da bayanai mata ne, sai mai bi musu, maza, masu kashi 30. Akwai kuma wadanda ba su bayyana jinsinsu ba. JADAWALI NA BAKWAI: BAYANAI DANGANE DA SUNAN ADABIN KASUWAR KANO SHEKARA WADANDA SUKA MAIDO ADADI 1-20 20 Kashi 1 21-40 320 Kashi 98 41-60 10 Kashi 1 JIMILLA 350 Kashi 100% Daga binciken da aka yi sama da kashi 98 sun san da cewar ana kiran wadananan litattafan da litattafan soyayya ko kuma Adabin Kasuwar Kano, kalilan ne daga ciki ba su sani ba, su ma kuma din daga abin da aka kalato, rashin sanin nasu ba ya rasa nasaba da cewar ko dai ba su mai da hankali ba ne ko kuma suna yin karatun ne ba tare da sanin ana kiran su da wani suna ba, face Hadisan Kano da suka ce suna jin ana kiran su da shi. Yawancin wadanda suka san da sunan littattafan Littattafan Soyayya ko Adabin Kasuwar Kano, matasa ne masu shekara 21 zuwa 40 kamar yadda yake a teburin na bakwai. Mafi rinjaye daga masu karatun da suka san da wadannan sunaye da ake kiran wadannan littattafai da su suna karanta littatafan domin. kusan kashi 70 na wadanda aka nemi bayanansu, suna karanta litattafan musamman matasa, kamar yadda muka gani a teburi na uku. Sai dai wasu daga cikin wadannan kashi din suna ganin cewa sunan da ake kiran wadannan littattafai da shi bai dace da shi ba. Kusan kamar kashi uku na daga wannan kason suna ganin bai dace a rinka kiransu da Adabin Kasuwar Kano ba, sai dai a kira su da litattafan soyayya ko kuma a canza masu wani sunan. JADAWALIU NA TAKWAS: BAYANAI KAN INDA AKE SAYEN LITATTAFAN INDA AKE SAYEN LITATTAFAN WADANDA SUKA MAIDO ADADI KASUWA 345 Kashi 99.9 KANTUNAN SAIDA LITATTAFAI 5 ½ JIMILLA 350 Kashi 100 Sannan dangane da kudaden da ake sayen litattafan ma bayanai sun zo daidai, domin akasarin amsoshin da aka maido sun nuna cewa kudin litattafan sun kama daga Naira 40 zuwa Naira 200. Dangane da maganar ba da hayar wadannan litattafan, su ma din kusan kaso 80 cikin 100 na wadanda suka amsa tambayoyin sun tabbatar da cewa sun san ana ba da hayar wadannan litattafai. Kashi kamar ishirin ne ba su sani ba, su ma din watakila don sayen litattafan kawai suke yi, ba su mai da hankali ga lura da cewar ana ba da hayar ba. JADAWALI NA TARA: BAYANAI DANGANE DA KO ANA KARUWA DA KARATUN LITATTAFAN Sama da kashi 85 cikin 100 da suka amsa tambayoyin sun nuna cewar ba su karuwa da komai daga karanta wadannan litattafan, suka ci gaba da cewar suna karanta litattfan ne kawai ko dai don rashin abin yi ne ko kuma don nishadi. Kaso kamar 15 cikin 100 su ne suka ce suna karuwa da sakonnin littattafan, kuma daga cikinsu mafi yawanci mata ne suka ce suna karuwar da ko dai zaman aure ko kuma soyayya ko mallake miji da dai sauransu. Sannan kuma ko a maganar darussan da ke cikin litattafan maganar ba ta canza zane ba, saboda abin da aka zakulo, masu karatun sun nuna cewa sun fi sha’awar daga na soyayya, sai zamantakewar aure ko rayuwar jama’a da dai sauransu. Ga dai yadda fasalin yake a teburi na kasa. ANA KARUWA DA KARATUN LITATTAFAN WADANDA SUKA MAIDO ADADI EH 15 15 A’A 335 85 JIMILLA 350 Kashi 100 Dangane da masu sana’ar ta ko dai rubuta litattafan ko kuma buga su, su ma babu abin da suke cewa da ya wuce sun shiga harkar ne don bunkasa adabi, sai kuma don neman kudi. Wasu sun nuna cewar lallai harkar akwai riba, amma wasu sun nuna cewa babu wata riba sai dai a yi don bunkasar adabin kawai. Haka kuma kan maganar matsalolin da suke fuskanta wajen rubutun, maganar kudi ita ce gaba, sai kuma kayan aiki na dab’i da sauransu.